30/12/2023
Ƙungiyar Izala ita ce ƙungiyar musulunci tilo a Najeriya da ba ta da na biyu da take gabatar da gasar karatun Alqur'ani maigirma tun daga matakin makarantu, anguwa, gunduma, ƙaramar hukuma, jiha, ƙasa (har da ƙasahen maƙwafta irin Nijar da Ghana).
Mahalarta daga duk wani sassan Najeriya da ƙasashen maƙwafta irin su Nijar, Cameroon, Chad, Benin Republic, Togo, Ghana, Guinea Conakry da sauran su.
An fara wannan gasa 1998, ba a taɓa fasawa ba don wani uzuri ko dalili daidai da shekara guda, bana shine karo na 27.
Kyaututtuka sun haɗa da motoci huɗu, na 9M, 5M, 4M da 2.5M, babura da dama, fridge, keken ɗinki da kuma ƙarin kuɗaɗe akan ko wani kyauta. Sannan kuma duk wani ɗan takaran da ya hau kujera bai ji sunan sa daga na 1 zuwa 5, akwai kyautan kuɗi da litattafai da aka tanada masa.
An gabatar da gasan a babban ɗakin taro na Multipurpose Hall da ke University of Jos Main Campus. An sauƙe dukkan baƙi daga 'yan takara, shuwagabanni da 'yan takara a manyan hotel na alfarma na birnin Jos, kamar Sharna, Shamshek da sauran su.
Abun farin ciki, cikin waɗanda s**a samu mota akwai ɗan jihar Ogun wanda ya lashe izu 20, da kuma ɗan jihar Benue da ya lashe izu 3. Izala leƙa gidan kowa.
Irin waɗannan manyan ayyuka na ƙungiyar Izala shi yasa mahassada suke ƙiran su da 'yan Mushede. Alhali babu wani aikin addini na kuɗi da zasu iya yi makamancin wannan.
In Allah ya kaimu farkon watan Izala Sheikh Muhammad Thani Alhaji Yahya Jingir zai jagoranci buɗe JIBWIS Islamic Center a babban birnin tarayya Abuja, wanda ya lashe sama da biliyoyin kuɗi.
Allah ya ƙara wa ƙungiyar Izala albarka, ya kunyatar da maƙiyan ta, Amin.