Map Magazine TV

Map Magazine TV Map magazine TV is a Television and Magazine station on internet, we broadcast programs in Hausa language. GOMBE

Ya Zama Dole Ne Mu Dinga Yin Kukan Kurà Muna Tunkarar Masù Kwacèn Waya, Domin 'Yàn Sanda Kimanin Dubu Goma Sun Yi Kadan ...
24/07/2025

Ya Zama Dole Ne Mu Dinga Yin Kukan Kurà Muna Tunkarar Masù Kwacèn Waya, Domin 'Yàn Sanda Kimanin Dubu Goma Sun Yi Kadan Su Kare Rayukan Mutane Sama Da Milyan 12 Dake Fadin Jihar Kano, Ra'ayin Ado Hassan Almustapha

Me za ku ce?

DA DUMI-DUMI: Akwai yiwuwar a samu daukewar Network din MTN, AIRTEL da Glo a jihohin Kaduna, Abuja, Kogi, Delta, Ribas, ...
24/07/2025

DA DUMI-DUMI:

Akwai yiwuwar a samu daukewar Network din MTN, AIRTEL da Glo a jihohin Kaduna, Abuja, Kogi, Delta, Ribas, Kuros Riba, Akwa Ibom, Ogun, Ondo, Edo, Legas, Neja, Osun da Kwara, Saboda yawaitar sata da lalata kayayyakin kamfanonin a garuruwan.

Inda kamfanonin s**a gargadi mutane da su daina sace musu kayayyakin su, matukar basu son network ɗinsu ya dauke.

Banyafe ba motata da Buhari ya k**a, cewar Namalamai"A ranar 10th February 2021, A cikin dokokin da Marigayi Buhari yayi...
23/07/2025

Banyafe ba motata da Buhari ya k**a, cewar Namalamai

"A ranar 10th February 2021, A cikin dokokin da Marigayi Buhari yayi na kuntatama Talaka yasa aka k**amin Mota a Katsina nayi asarantan Har abada sai munje gaban Allah, Allah zaikarban min hakkina.

"Wanda baijaji dadin wannan maganarba Don Allah yaje yatambaya nawa kudin Kanmota da Tanki yake yasiyomin yabiyani sai inyafemishi.

Daga Abdallah Muhammad NaMalamai

Yadda Gwamnan Jihar Gombe Ya Shimfida Ayyuka A Gombe Ta KuduA kokarin gwamnati na cigaba da ayyukan raya karkara da bira...
23/07/2025

Yadda Gwamnan Jihar Gombe Ya Shimfida Ayyuka A Gombe Ta Kudu

A kokarin gwamnati na cigaba da ayyukan raya karkara da birane a ƙarƙashin jagorancin gwamna Muh'd Inuwa Yahaya, yanzu haka an kammala aikin T**i daga Ture zuwa Gelengu.

T**in mai tsawon Kilomita 10.8 zai haɗe garuruwan Bakasi, Balansani, Matinja, Dasa Buzu da Lajangara, wanda waɗannan garuruwa suna ƙananan hukumomin Kaltungo da Balanga.

Waɗannan garuruwa akasarin su garin manoma ne waɗanda wannan aiki zai sauƙaƙa musu fita da amfanin Gonakin su zuwa kasuwanni.

Wannan aiki yana cikin alwashin da gwamna Inuwa yayi na yin Kilomita 100 a kowacce karamar hukuma a jihar Gombe.

Daga Haji Shehu
SA Media

Shin Da gaske ne zogale yafi kaza
23/07/2025

Shin Da gaske ne zogale yafi kaza

DA DUMI-DUMI: Akpabio ya yi kuskure a wajen jawabi a majalisa, ya ce “jana’izar Tinubu” a maimakon Buhari.Copied
23/07/2025

DA DUMI-DUMI: Akpabio ya yi kuskure a wajen jawabi a majalisa, ya ce “jana’izar Tinubu” a maimakon Buhari.

Copied

CIKIN HOTUNA: gwamna Radda kenan bayan sallamo shi Daga Asibiti
23/07/2025

CIKIN HOTUNA: gwamna Radda kenan bayan sallamo shi Daga Asibiti

Gwamnan Kano ya sake lashe lambar yabo ta gwarzon shekara Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya lashe lambar yabo ta ...
23/07/2025

Gwamnan Kano ya sake lashe lambar yabo ta gwarzon shekara

Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya lashe lambar yabo ta “Gwamnan Shekara ta 2025” daga Jaridar Blueprint.

An ba da wannan lambar yabo ne sak**akon gagarumar gudunmawa da gwamnan ya bayar wajen bunkasa fannin ilimi, inda ya ware mafi yawan kudin kasafin kudi zuwa bangaren ilimi fiye da kowace jiha a Najeriya a 2025.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sanusi Dawakin-Tofa, mai magana da yawun gwamnan, ya fitar a Kano a jiya Talata.

A yayin taron, Sanusi Bature Dawakin-Tofa, wanda ya wakilci gwamnan, ya sake jaddada kudurin gwamnatin sa na sauya tsarin mulki da tafiyar da gwamnati tare da mayar da hankali sosai kan ilimi.

Shin zaku iya kara zabar jamiyar APC idan kwankwaso ya koma cikin ta?
23/07/2025

Shin zaku iya kara zabar jamiyar APC idan kwankwaso ya koma cikin ta?

Dan Allah ina Rokon Masu kasheni A social media Suyi Hakuri haka sun kasheni yafi Sau GomaSakon Rabiu Rikadawa zuwa GA Y...
23/07/2025

Dan Allah ina Rokon Masu kasheni A social media Suyi Hakuri haka sun kasheni yafi Sau Goma
Sakon Rabiu Rikadawa zuwa GA Yan Social media

23/07/2025

Daga bauchi

Tsarin mulkin Tinubu ya jefa ƴan Najeriya cikin wahala — ADCMai magana da yawun jam’iyyar African Democratic Congress (A...
23/07/2025

Tsarin mulkin Tinubu ya jefa ƴan Najeriya cikin wahala — ADC

Mai magana da yawun jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Bolaji Abdullahi, ya ce manufofin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke aiwatarwa sun gaza rage radadin da ’yan Najeriya ke fuskanta.

A yayin wata tattaunawa a tashar Channels a ranar Laraba, Abdullahi ya caccaki salon tafiyar da tattalin arzikin kasar, yana mai cewa fa’idodin da aka yi alkawari ga talakawa har yanzu ba su bayyana ba.

“Manufofin wannan gwamnati ba suyi aiki ba,” in ji Abdullahi, yana mai cewa: “Mutane na cikin wahala, amma jami’an gwamnati suna tafiya da gagarumin ayari, suna rayuwa cikin alatu, yayin da kuke cewa talakawa su ci gaba da hakuri.”

Ya bayyana cewa akwai babbar gibin da ke tsakanin kalaman gwamnati da hakikanin rayuwar talaka.

Abdullahi ya kalubalanci gwamnati kan rashin fayyace wa’adin wahalar da ake sa ran mutane za su sha da kuma irin lada ko sauki da za su samu daga bisani.

Address

Gombe

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Map Magazine TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Map Magazine TV:

Share