28/08/2018
Anatare::::::: Kaunarki ta mamayemini
Dukkannin sassan ilahirin jikina.
Tabi jini, tsoka, zuwa bargon
ashina. Domin zuciyata ita ce
ma’adanin surrikan tinaninki
a kodayaushe, Masoyiyata
Tabbas zuciya wata aba ce
waddda takan sa gangar jiki
rashin amfani idan ba ta samu
abin da take so ba ban san sonka
ya yi nisa haka a zuciyata ba sai da
Na zauna ina tunaninka kawai na ga hawaye
Na zuba daga cikin idona
hakika kaunarka ta kai mutukar kurewa a cikin raina
Na kasance ma’abocin soyayya
zuciyata ma ta gaskata hakan,
Lokaci na shudewa soyayyarki
na karuwa a cikin zuciyata,
a lokacin da ki ke cikin farin ciki
kyakkyawar fuskar ki na bayyanar
da murmushi mai taushi da tausasa
zuciyar ma’abocin kallonta, kece
wadda na ke so a cikin zuciyata
babu wata da za ta iya canja
matsayin ki a wajena.
Ni fa ina ganin da akwai wata mace
da zata ganka ta kalle ka tabbas zan iya
sawa ayi mata duka saboda tana kallon
muradin raina nifa saboda tsantsar
Kaunarka bana bacci sai naga fuskark
haka zalika da ita nake fara
farkawa daga bacci.
Ka da ki fadawa kowa kalaman sirrin
bude soyayya da kawancen dake
tsakanin mu, domin kuwa a dukkan
lokacin da kika furta wadannan
kalaman sirri ga wani wato *Ina SonKa*
hakan na nuni da cewa zai yi amfani
da shi wajen bude mana akwatin
soyayyar mu ta sirri wanda hakan
zai ba shi damar yi mana gagarumar
sata har ya yi sanadiyar raba ni
da ke har abada, Ina son ki.