21/08/2026
’Yan Sanda Sun Ceto Mutane 75 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Kaduna
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta ce ta ceto mutane 75 da wasu ’yan bindiga s**a yi garkuwa da su a ƙauyen Folwaya, da ke kusa da Birnin Gwari.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, DSP Mansir Hassan, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, 21 ga Agusta, 2026.
A cewar sanarwar, waɗanda aka yi garkuwa da su sun haɗa da maza, mata da yara da ke tafiya cikin motocin haya, lokacin da wasu mahara ɗauke da makamai s**a tare su tare da tilasta musu bin su zuwa cikin daji.
Rundunar ta ce bayan samun rahoton lamarin, ta tura jami’an ’yan sanda daga Birnin Gwari zuwa yankin domin ceto mutanen.
Sai dai kafin jami’an su isa inda ake tsare da mutanen, ’yan bindigar sun tsere bayan sun hango jami’an tsaro, inda s**a bar waɗanda s**a yi garkuwa da su a wurin.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kaduna ya yaba wa reshen ƙungiyar NURTW na Birnin Gwari bisa samar da bayanan da ya ce sun taimaka wajen gudanar da aikin ceto.
Kwamishinan ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro bayanan sirri game da duk wani mutum ko motsi da s**a yi zargin zai iya zama barazana ga tsaro.
Ya ce haɗin gwiwar jama’a da jami’an tsaro na da muhimmiyar rawa wajen dakile hare-hare da kuma kare rayuka da dukiyoyin al’umma.