
23/06/2025
Wane Ne Ke Neman Bata Sunan NAHCON?
Daga Ibrahim Baba Suuleiman
Zarge-zargen da ke yawo cewa Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta kashe sama da Naira biliyan 1.64 wajen daukar nauyin matan ma'aikata yayin aikin Hajjin 2025 ba kawai ƙarya ba ce, har ma suna k**a da wani yunkuri na ganganci domin bata suna da kwarjinin hukumar da shugabancinta. Zargin da ya fi daukar hankali shi ne wanda ke cewa Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya kwana a ɗakin otal a Hilton Makkah Suites da ke biyan $1,000 kowane dare tare da kawo ‘yan uwansa 12, wannan batu babu ƙaƙƙarfan hujja ko shaidar gaskiya a cikinsa.
Don fayyace gaskiya, manufofin NAHCON ba su ba da damar amfani da kudaden gwamnati wajen daukar nauyin tafiya ko masaukin matan ma'aikata ba. Abin da ke akwai shi ne tsarin walwala da hukumar ta amince da shi ta hannun kwamitinta, wanda ke ba ma'aikatan da ke yi wa ƙasa aiki a Saudiyya har na tsawon fiye da wata guda damar daukar matansu da kudinsu, cikin tsarin rangwame da ya kebanta. Wannan tsari bai haɗa da muhimman abubuwa ba k**ar masauki a Makka, abinci, kuɗin tafiya (BTA), da sufuri tsakanin garuruwa. Wadannan duk ma'aikacin ne ke daukar nauyinsu daga alawus dinsa.
Wannan tsari ba sabon abu ba ne a NAHCON. Hukumomi k**ar NNPC, CBN, FIRS da ma’aikatar harkokin wajen Najeriya suna da irin wannan tsari na tallafa wa ma’aikata yayin dogon aiki a ƙasashen waje. Manufar NAHCON na bin matakin da ya dace ne da dokoki da ka’idojin kasa da kasa, kuma ba ta da alaka da almundahana ko amfani da dukiyar jama’a ta hanyar da ba ta dace ba.
Yin zargin cewa ma'aikatan NAHCON ba su da ikon daukar nauyin matansu babban kuskure ne kuma magana ce ta raina hankali. Wannan magana ta son rai ne, kuma a wasu lokuta matan ma'aikatan suna taka rawar gani wajen daukar wasu daga cikin kudin tafiyarsu. Babu wani laifi ko karya doka a wannan tsarin.
Adadin kudin da aka ambata a cikin rahotannin da ke yawo an cika su da ƙarya kuma sun ginu ne a kan ƙaryar da ba ta da tushe. Rahotannin sun yi kuskure wajen ɗaukar cewa duk kudin da aka kashe iri ɗaya ne ga kowa da kowa, ba tare da la’akari da ainihin abin da wannan tsrari ya ƙunsa ba. NAHCON ta bayyana cewa abubuwan da aka haɗa a cikin wannan tsarin na matan ma'aikata sun ƙunshi takardun visa, tikitin jirgi da masauki kawai a Masha'ir da Madinah. Ma'aikatan sun san waɗannan iyakokin kuma suna shiryawa bisa haka.
Maganar cewa Shugaban ya kwana a ɗakin $1,000 a dare kuma ya kawo iyalanshi 12 ƙarya ce tsagwaron ta. Babu wata shaida ko takardar biyan kudi da ke nuna hakan daga hukumar. A hakikanin gaskiya, Shugaban ne da kansa ya dauki nauyin tafiyar matarsa ta hanyar da ya dace, kuma babu wani daga cikin iyalansa da ya halarci aikin a matsayin jami’in NAHCON. Ko visa da aka yi wa matarsa ma, ba a karkashin hukumar aka yi ba.
Har ila yau, ƙarya ce a ce matan ma'aikata sun mamaye dakunan da aka tanada wa mahajjata ko jami’an hukumar. NAHCON tana da ƙa'idoji na masauki da ake kula da su ta hanyar kwamitoci da aka ware. Duk wani sauyi ko sabani ana gyara shi nan da nan. Babu wata shaida da ke nuna an yi amfani da dukiyar gwamnati ba bisa ka’ida ba.
Kiran da wasu ke yi na a binciki NAHCON ta hannun EFCC yana da kyau, NAHCON ba ta da abin ɓoyewa. Ana duba asusun ta akai akai ta Ofishin Auditor-General na Tarayya kuma hukumar na bin doka wajen dukkanin harkokinta na kudi. Amma irin wadannan binciken dole ne su dogara da gaskiya ba sharri ko siyasar karya da nufin bata suna ba.
Abin takaici shi ne, bayan gudanar da aikin Hajji mafi nasara a cikin kusan shekaru 15, aikin da aka yaba masa daga kowane bangare, wasu mutane sun dage wajen bata sunan NAHCON. Shin saboda an daina salon "ta fiya ta zo" da aka saba? Ko saboda Shugaban ba ya karbar cin hanci? Ko kuma saboda malami ne kuma Sheikh mai tsantseni, wasu ke jin tsoro da jajircewarsa da adalcinsa?
Ko menene dalili, lokaci zai fayyace gaskiya. NAHCON za ta ci gaba da jajircewa wajen nuna gaskiya, rikon amana da yi wa al’ummar Musulmi ta Najeriya hidima. Wadanda ke son bata sunanta don wata manufa ta siyasa ko ta son kai, a ƙarshe za su sha kunya.
Rubutawa: Alhaji Mubarak Oyewale
Mahajjacin Hajjin 2025 daga Ilorin
Jibwis Nigeria