27/06/2025
Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya kaddamar da aikin noman damina na shekarar 2025 tare da rabon takin zamani a farashi mai rahusa domin ƙarfafa samar da abinci da tallafawa dubban manoma a fadin jihar.
Da yake jawabi a yayin ƙaddamarwar a garin Gombe, fadar gwamnatin jihar Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa ta sayi tan 10,000 na taki—daidai da buhu 200,000—na taki nau’in NPK.
A cewar wata sanarwa daga Daraktan Yada Labarai na gidan Gwamnatin Jihar Gombe, Ismaila Uba Misili, kowanne buhu da aka saya akan naira 44,000 za a sayar da shi ga manoma akan farashin rangwame na naira 27,000.
Ya bayyana cewa wannan tallafin ya ninka yawan taki da aka raba a kakakin noman shekarar 2024 fiye da sau biyu, kuma yana nuna aniyar gwamnati na sauƙaƙa harkar noma da samar da ɗimauta.
Gwamna Yahaya ya ce fiye da kaso 80 cikin ɗari na al’ummar jihar suna dogaro da noma, kuma tsawon shekaru shida da s**a wuce gwamnatinsa tana ci gaba da bayar da tallafin kayan noma duk da ƙalubalen tattalin arziki.
Ya ce wannan shiri yana daga cikin tsarin Renewed Hope Agenda na Shugaba Bola Ahmed Tinubu wanda ke ganin noma a matsayin ginshiƙin ci gaban tattalin arzikin da ya haɗa kowa da kowa.
Gwamnan ya jaddada muhimmancin samun kayan aiki cikin lokaci domin ƙara yawan amfanin gona da tabbatar da isasshen abinci.
Ya umurci Ma’aikatar Noma ta jihar tare da hukumomin tsaro da ƙungiyoyin fararen hula da su sa ido sosai wajen sayarwa da rabon taki don hana karkatarwa da tabbatar da cewa ya isa hannun sahihan manoma a dukkan mazabu 114 na jihar.
Gwamna Yahaya ya kuma bayyana wasu manyan ayyuka da ake aiwatarwa domin canza fannin noma a jihar, ciki har da haÉ—in gwiwa da Gwamnatin Tarayya, Bankin Duniya, da Bankin Raya Afirka.
Gwamnan ya kuma ambaci ayyukan da ake yi k**ar shirinan na bunkasa kiwon dabbobi wato Agro-Livestock Development Zone da kuma Muhammadu Buhari Industrial Park, wanda ke dauke da sabon katafaren wurin sarrafa iri domin ƙara samarwa.
Gwamnan ya bukaci manoma su yi amfani da takin yadda ya dace tare da bin shawarwarin yanayi domin kare amfanin gonakinsu.
Haka kuma, ya yi kira da a zauna lafiya tsakanin manoma da makiyaya, inda ya ja kunnen sarakunan gargajiya kan mamaye filayen kiwo da hanyoyin shanun, yana mai cewa duk wanda aka k**a yana tayar da rikici zai fuskanci hukunci bisa shawarar kwamitin sasanta rigingimu.
A cikin sakonsa na fatan alheri, Ko’odinetan Ma’aikatar Noma da samarda abinci ta Tarayya a jihar, Mista Absalom Akwaras Lansibol, ya yabawa jajircewar Gwamna Yahaya wajen bunkasa harkar noma, yana bayyana wannan shirin a matsayin wani babban mataki na ƙarfafa rayuwar al’umma da tabbatar da wadatar abinci.
Tun da farko, a jawabinsa Kwamishinan Noma na jihar, Dakta Barnabas Malle, ya nuna godiya ga Gwamnan bisa ci gaba da tallafawa manoma, yana cewa wannan kokari ya sake tabbatar da cewa gwamnati na da cikakkiyar niyya wajen gyara harkar noma
RAMFAK REDIO & TELEVISION
NIGERIA