11/06/2026
Daliban Sashen Mass Communication na Jami'ar Tarayya da ke Kashere, karkashin ƙungiyar su ta MACOSA, sun gudanar da wani gagarumin gangami a harabar jami'ar a wani ɓangare na bukukuwan makon MACOSA na shekarar 2026.
Gangamin, wanda ya gudana ranar 10 ga watan Yunin 2026, ya samu halartar ɗalibai da dama waɗanda s**a fito cikin annashuwa domin nuna goyon baya ga bukukuwan ƙungiyar tare da wayar da kan al'ummar jami'ar game da ayyukan da ake gudanarwa a yayin makon.
Masu halartar gangamin sun zagaya sassa daban-daban na harabar jami'ar, inda s**a nuna haɗin kai da zumunci tsakanin ɗaliban Mass Communication tare da ƙarfafa sauran ɗalibai su shiga cikin shirye-shiryen da aka tanada.
An bayyana gangamin a matsayin mai cike da nishaɗi da armashi, lamarin da ya nuna jajircewar ɗaliban wajen tabbatar da nasarar bukukuwan MACOSA Week 2026.
Rahotanni sun ce taron ya gudana cikin lumana tare da nuna irin rawar da ƙungiyar ke takawa wajen ƙarfafa haɗin kai da bunƙasa harkokin ɗalibai a jami'ar.
✍️ Bashir Habeeb Adam
Media Director, MACOSA