Arewa Media Watch

Arewa  Media Watch News Media Company

Shekaru Biyu A Gwamnatin Da Ta Dawo Da Martabar Jihar  KanoA lokacin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya hau karagar mulki a r...
04/06/2025

Shekaru Biyu A Gwamnatin Da Ta Dawo Da Martabar Jihar Kano

A lokacin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya hau karagar mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023 al’ummar Kano sun fara ganin sauyi na gaske. Sauyin da ya tabbatar da aiki, tsare-tsare, da kula da lafiyar al’umma da tattalin arziki wannan ba mulki ba ne na alkawari kawai, wannan mulki ne mai cike da aiki da cika alkawari.

A cikin shekaru biyu kacal, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da cewa mulki nagari ba a magana ba ne, aiki ne da kishin al'umma

A bangaren noma da ban ruwa, sama da hectare dubu an samar da su domin noman rani, tare da gine-ginen dam-dam a kananan hukumomi fiye da goma sha biyu.

A fannin lafiya, an cire dubban masu rijista na bogi, an dauki matakan inganta kulawa da marasa lafiya, tare da shigar da dubban talakawa cikin tsarin lafiya kyauta.

Gwamnatin Abba ta kawo karshen matsalar rashin magunguna a asibitoci, ta kafa cibiyoyi na musamman da samar da injinan iskar oxygene masu amfani da hasken rana.

An ba da kulawa ta musamman ga yara da mata masu fama da cututtuka ta hanyar shirin ABBACARE, tare da tallafawa masu sikila da marasa galihu.

Tsarin rajista da kididdiga na zamani (EMR) ya kara inganta tsarin lafiya da sarrafa bayanai a asibitoci fiye da goma.

Gaskiya ce, Gwamna Abba Kabir Yusuf yana aiki tukuru, yana gina jihar Kano bisa gaskiya, adalci da amana. Wannan gwamnatin ba ta yi alkawarin da ba ta cika ba cikin shekara biyu da fara mulkin jihar Kano!

ABAISWORKING
📅 29th May, 2025
Wanda ya shuka nagarta, shi zai girbi tagomashi

AJAM Ta Yaba Wa Gwamnatin Tarayya Kan Nasarorin Da Ta Cimma Wajen Dawo da Zaman Lafiya a ArewaGamayyar Kungiyar Ayyukan ...
01/06/2025

AJAM Ta Yaba Wa Gwamnatin Tarayya Kan Nasarorin Da Ta Cimma Wajen Dawo da Zaman Lafiya a Arewa

Gamayyar Kungiyar Ayyukan Arewa (AJAM) ta jinjina wa Gwamnatin Tarayya bisa manyan nasarori da ta samu wajen dawo da zaman lafiya da tsaro a yankin Arewa, wanda da can ya kasance cike da matsalolin ta’addanci da miyagun laifuka.

Kungiyar ta bayyana musamman rawar da Ma'aikatar Tsaro ke takawa wajen aiwatar da manyan ayyukan tsaro masu amfani da fasahar zamani a yankunan Arewa maso Yamma da Arewa maso Tsakiya.

A cikin wata sanarwa da mai jagorantar kungiyar, Lauretta Bako ta fitar a ranar Alhamis, AJAM ta bayyana cewa an samu gagarumin ci gaba a fannin tsaro a yankin, wanda hakan ya biyo bayan dabarun rundunonin tsaro da gwamnatin ke aiwatarwa.

"A yau muna rayuwa a wani sabon yanayi na tsaro fiye da da, inda aka kore Boko Haram zuwa matsugunan duhu, yayin da shugabannin masu garkuwa da mutane da ‘yan bindiga s**a hallaka ko s**a tsere."

"Nasarorin da aka samu wajen kawar da ‘yan bindiga, ‘yan ta’adda da kuma sarkakiyar hanyoyin aikata laifi, tare da farfado da tattalin arzikin yankuna, ya nuna ingancin wannan tsari."

A cewar AJAM, daya daga cikin ginshikan wannan nasara shine Operation FANSAR YAMMA, wanda ya samu nasarori da dama, ciki har da hallaka sanannen shugaban ‘yan bindiga, Kachalla Dogo Isah, tare da wasu ‘yan ta’adda 44 a jihar Zamfara.

Sanarwar ta kara da cewa, “Kashe fitattun masu aikata laifi ciki har da masu sayar da mak**ai da shugabannin ‘yan bindiga ya tarwatsa manyan hanyoyin aikata laifi, tare da isar da sako ga sauran masu laifi cewa gwamnati ba za ta yarda da rashin tsaro ba.”

Tasirin wadannan matakan tsaro ya wuce kidayar alkaluma kawai; yana da tasiri kai tsaye ga rayuwar yau da kullum ta ‘yan kasa. Hanyoyi k**ar hanyar Kaduna-Abuja, wanda da can aka fi jin tsoro, yanzu sun fi aminci ga matafiya, hakan kuma yana taimakawa wajen kasuwanci da zirga-zirga.

Kasuwanni a wurare irin su Giwa, Birnin Gwari da Jibia suna samun sabuwar rayuwa, inda shugabannin al’umma da jama’a ke tabbatar da ingancin tsaro. Farfadowar harkokin kasuwanci na da nasaba kai tsaye da nasarorin da sojoji s**a samu tare da samar da yanayi mai kyau ga kasuwanci.

Gina Brigade na National Mission Force a Samaru Kataf shima ya taka rawa wajen warware matsalolin tsaro a Kudu ta Kudancin Kaduna, wanda ya haifar da ingantattun yanayin zamantakewa da tattalin arziki. A cikin watanni ukun farko na shekarar 2025 kadai, an hallaka ‘yan ta’adda 122 kuma an k**a fiye da 1,000 daga cikin masu laifi.

A matsayinmu na Arewa Joint Action Movement, muna tare da kokarin da Ma’aikatar Tsaro ke yi wajen kare al’ummominmu da dawo da fata a zukatan jama’a. Muna fahimtar cewa har yanzu akwai kalubale, amma nasarorin da aka samu sun haskaka mana hanya. Zamu ci gaba da goyon bayan manufofi da matakan da za su kawo zaman lafiya, tsaro da cigaba mai dorewa a Arewarmu.

Peter Obi Ya Karyata Jita-Jitar Zama Mataimakin Atiku A Zaben 2027 – Inji Obidient MovementDaga Comr Haidar H Hasheem Ob...
19/05/2025

Peter Obi Ya Karyata Jita-Jitar Zama Mataimakin Atiku A Zaben 2027 – Inji Obidient Movement

Daga Comr Haidar H Hasheem

Obidient Movement ta bayyana cewa rahoton da ke yawo a kafafen yada labarai na cewa tsohon ɗan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP a zaben 2023 Mr. Peter Obi ya amince ya zama mataimakin Alhaji Atiku Abubakar a wani sabon hadin gwiwar siyasa da ake kokarin kafa wa gabanin zaben 2027, karya ne kuma babu gaskiya a cikin rahotan.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Nana Kazaure, Daraktar Sadarwa da Tsare-Tsare ta kungiyar, ta fitar a ranar 19 ga Mayu, 2025, inda ta bayyana cewa rahoton ya kasance kirkirar wasu marubuta ne kawai, kuma hakan yana iya janyo rudani da kuskuren fahimta a tsakanin jama'a.

Ta ce ko da yake ana ci gaba da gudanar da tattaunawa cikin lumana da wasu manyan ‘yan siyasa da masu ruwa da tsaki don samar da hadakar da za ta ceto Najeriya, babu wata tantama cewa Mr. Obi bai amince da mukamin mataimaki ba, kuma babu wata yarjejeniya da ta shafi hakan.

Sanarwar ta bayyana cewa manufar Mr. Obi da Obidient Movement ita ce samar da cikakken hadin kai don yaki da mulkin rashin nagarta, cin hanci da rashawa, yunwa, talauci, matsalar kiwon lafiya, da karancin ilimi ga yara ba siyasar karbar mukami kawai ba.

Kungiyar ta sake jaddada cewa Mr. Obi har yanzu na cikin jam’iyyar Labour Party, kuma idan zai sauya sheka ko jam’iyya a nan gaba, zai bayyana hakan da kansa.

Daga karshe, Obidient Movement ta bukaci 'yan Najeriya da kafafen yada labarai da su kauce wa yada jita-jita da rahotannin da ka iya tada tarzoma saboda rashin tushe, su maida hankali wajen taimakawa tare da gina Najeriya mai inganci da adalci.

Ranar: 19/05/2025
Sa hannu: Nana Kazaure, Daraktar Sadarwa da Tsare-Tsare, Obidient Movement

05/05/2025

Ikon Allah!

Katafaren ginin gidan alfarma kenan da Kauran Bauchi ya ginawa kansa don jindadinsa da samun kwanciyar hankalinsa.

Ministan Tsaron Nigeria, Mohammed Badaru Abubakar, Ya Karɓi Baƙuncin Wakilin Majalisar Ɗinkin Duniya Kan Harkokin Jinƙai...
30/04/2025

Ministan Tsaron Nigeria, Mohammed Badaru Abubakar, Ya Karɓi Baƙuncin Wakilin Majalisar Ɗinkin Duniya Kan Harkokin Jinƙai

A ranar Talata, 29 ga Afrilu 2025, mai girma Ministan Tsaro na Ƙasa, H.E. Mohammed Badaru Abubakar, CON, mni, ya karɓi baƙuncin Mr. Mohamed Malick Fall, wanda shi ne Wakilin Majalisar Ɗinkin Duniya a Najeriya kuma mai kula da harkokin jinƙai.

Tattaunawar wanda aka gudanar a ofishin Ministan dake Ship House, Abuja, ta mayar da hankali ne kan yadda Najeriya za ta ƙara tallafawa ayyukan jinƙai da Majalisar Ɗinkin Duniya ke gudanarwa a ƙasar.

Me za ku ce kan ajiye mukamin da Dr Hakeem Baba Ahmed yayi?Dr Hakeem Baba Ahmed, shine tsohon mai magana da yawun kungiy...
04/04/2025

Me za ku ce kan ajiye mukamin da Dr Hakeem Baba Ahmed yayi?

Dr Hakeem Baba Ahmed, shine tsohon mai magana da yawun kungiyar Dattawan Arewa, shine za kuji kullum yana kalubalantar Gwamnati a duk inda tayi kuskure a gidajen Rediyo da Television da kafofin sada zumunta.

Tun ranar da Tinubu ya bashi mukamin mai bashi shawara ya turashi Ofis din Kashim aka daina jin duriyarshi, ya daina cewa komai akan sha'anin kasar.

Yasha caccaka da shagube iri-iri a wurin al-umma, yau da safe kwatsam sai ga sanarwar ya ajiye mukaminshi a jaridar Daily Trust.

ƊAN BELLO ƘATON MAƘARYACI NE KUMA AZZALUMI.Sanarwa daga Jibwis Nigeria ✍️Na kalli Video da Dan Bello yayi yana zargin Sh...
01/04/2025

ƊAN BELLO ƘATON MAƘARYACI NE KUMA AZZALUMI.

Sanarwa daga Jibwis Nigeria ✍️

Na kalli Video da Dan Bello yayi yana zargin Sheikh Abdullahi Bala Lau da kungiyar Izala da karban kudi a hanun Gwamnatin tarayya da sunan gina ajujuwa, kuma yake cewa wai an cinye kudin ba'ayi aikin ba.

Abunda ya bani mamaki shine yanda tsananin son ɓata sunan Malamai ya rufewa Dan Bello ido ya gagara gane description na aikin gine-ginen ajujuwan da yake magana akai, wanda duk wanda yake da ilimi kuma ya sanya nutsuwa zai gane meye abun yake nufi cikin sauki.

Aiyyukan ginin ajujuwa da Dan Bello ya nuna, CONSTITUENCY PROJECTS na HON. MUKHTAR ALIYU BETARA, Dan Majalisar tarayya mai wakiltar Bayo/Biu/Kwaya-Kusar... Federal Constituency a Majalisar Wakilai.

Yanda description na aikin yake shine, Hon. Mukhtar Betara ya saka zai gina ajujuwa wa kungiyar Izala da Sheikh Bala Lau yake jagoranci, wacce itace ake cewa "IZALA KADUNA", haka nan zai gina ajujuwa a makarantun kungiyar Izala da Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir yake jagoranci, wacce ita ake nufi a takaddar da cewa IZALA JOS, kuma zai ginawa yan Darika ma har bangarori biyu, dukka za'ayi wannan gini ne a Kwaya-Kusar LGA Borno State, k**ar yanda yake jikin screenshot da nayi attaching a kasa.

Sunan JOS da KADUNA da akayi amfani dashi ba anyi ne don bambancewa tsakanin Izala 1&2, ba wai aiyyukan a JOS da KADUNA suke ba, k**ar yanda shi Dan Bello ya fada.

Haka nan abunda Dan Bello ya saka na cewa an ware kudade domin ginin ajujuwa a JIBWIS Collage of Education Jega, Kebbi State, shima Constituency projects ne na Senator da yake wakiltar yankin a Majalisar dattijai, Senator Muhammad Adamu Aliero, kuma Senator Aliero shi ya gudanar da aikinsa da kansa, ba kungiyar Izala aka turawa kudi ba k**ar yanda Dan Bello ya fada.

Shima wannan aikin daƙiƙi Dan Bello yace wai ba'ayi ba, kuma karya ne Senator yayi aikin k**ar yanda yayi alkawari a wani taron kaddamar da Collage din (Akwai hoton allon kaddamar da ginin da Sunan Senator Aliero, da kuma hotunan makarantar a kasa).

Wallahi tallahi na jima da gane cewa abubuwa da yawa da Dan Bello yake fada shaci-faɗi ne kawai, yana samun karbuwa ne a wajen mutane kawai saboda yana attacking shugabanni ne, sak**akon rashin jituwa da take tsakanin talakawa da shugabanni.

Duk wanda yake son fahimtar gaskiya kan abunda na fada, ya nutsu ya sake kallon video Dan Bello with an open and objective mind.

Lalle Ɗan Bello ya tabka kuskure a wannan bincike da yace yayi, wanda ke ciki da sharri da cin mutunci ga shugaban mu, wannan kuma ya kara tabbatar mana da cewa akwai waɗanda suke ɗaukar nauyin sa da bashi bayanan ƙarya, domin biyan buƙatar kan su.

Da farko dai yace Sheikh Abdullahi Bala Lau Yana da akawun sunfi guda talatin, wannan ƙarya ne tsagworanta, zamu so ya kawo mana cikekken bayani akan waɗannan akawun guda talatin da ya faɗa ɗaya bayan ɗaya.

Duk waɗannan zarge-zarge da Ɗan Bello yayi basu da alaƙa da Sheikh Bala Lau ko ofishin sa a matakin ƙasa, kuma bai san da su ba.

A ƙusa da ƙarshe Ɗan Bello ya bada adireshin wani office a garin Lau dake jahar Taraba, wannan ƙarya ne, Sheikh Bala Lau bayi da wani office dake zama a Lau mallakar sa, in banda gidansa wanda in yaje garin yake sauƙa da iyalansa.

A ƙarshe Ɗan Bello ya ƙarƙare da cin mutuncin shugaban mu da ƙiransa da suna na ƙasƙanci.

Matsayar mu: Da farko dai mun kai ƙararsa wajen Allah, tare da addu'ar Allah ya nuna misali da shi, shi da dukkan masu aiki irin nasa, su girbi abun da s**a shuka tun anan duniya.

Abu na biyu, zamu je kotu da shi domin yazo ya bada dukkan bayanan abun da ya faɗa, musamman yadda ya samo BVN tunda munsan ko hukuma ce zatayi bincike irin haka, sai ta nemi izini daga mahukunta, Insha Allah da Ɗan Bello da waɗanda suke temaka masa da labaran ƙarya ƙarshenku yazo, domin sai gaskiya ta bayyana Insha Allah.

Sannan akwai buƙatar Ɗan Bello yasan waye shugaba Sheikh Abdullahi Bala Lau a ɓangaren kasuwanci tun kafin ya zama shugaban JIBWIS, yafi ƙarfin waɗannan kuɗin da yake ambatawa. ~Jibwis Nigeria

Ministan Tsaron Najeriya Ya Kai Ziyara Depot Na Sojojin Najeriya Dake Garin ZariyaMai Girma Ministan Tsaro, Mohammed Bad...
25/03/2025

Ministan Tsaron Najeriya Ya Kai Ziyara Depot Na Sojojin Najeriya Dake Garin Zariya

Mai Girma Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar CON, mni, ya kai ziyarar tantancewa ta yini guda a Depot na Rundunar Sojojin Najeriya da ke Zariya a yau, Talata, 25 ga Maris, 2025.

A yayin ziyarar, Minista da tawagarsa sun samu cikakken bayani daga Kwamandan Depot, Manjo Janar AB Mohammed, kan tsarin aiki, gudanar da ayyuka, da horon da ake bai wa sojoji a cibiyar.

Cikin tawagar Ministan akwai Sakataren Dindindin na Ma’aikatar Tsaro, Ambasada Gabriel Tanimu Adudu; Mai Ba da Shawara Kan Fasaha, Janar AT Jibril (Rtd); da Babban Jami’in Ma’aikata, Birgediya Janar AA Garba.

Mati Ali
PA Media & Publicity to the Hon Minister of Defense.

Tinubu Ya Ƙuduri Aniyar Inganta Tsaro Tare Da Bayar Da Horo Na Musamman Ga Sojojin Najeriya ~ Badaru Ministan Tsaro, Moh...
24/03/2025

Tinubu Ya Ƙuduri Aniyar Inganta Tsaro Tare Da Bayar Da Horo Na Musamman Ga Sojojin Najeriya ~ Badaru

Ministan Tsaro, Mohammad Badaru Abubakar, ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu na kokarin samar da kayayyakin yaki na zamani, don inganta jin dadin jami’an tsaro, da basu horo na musamman domin inganta tsaro a Najeriya.

Ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da horon Special Operations Force a Jaji, Kaduna, wanda za'a horas da sojoji dabarun yaki na zamani, yakar ta’addanci, leken asiri, da ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.

Shirin zai fara da dakaru 800 daga cikin jimillar 2,400 da ake sa ran horaswa, kuma gwamnatin Tinubu ta kuduri aniyar samar da mak**ai, na’urorin leken asiri, da horas da sojoji kan sabbin dabaru.

Badaru ya jaddada cewa wannan horo zai karfafa tsaro, kare ‘yancin kasa, da kuma tabbatar da zaman lafiya a Najeriya da makwabtanta. Ya bukaci dakarun da ake horaswa su jajirce, domin su zama garkuwa ga kasa.

Mati Ali
PA Media & Publicity to the Hon. Minister

Sabuwar Jam'iyyar Maja Ta Su EL-RUFAI DA ATIKU Yaudara Ce Ba Talakawa Ne A Gabansu Ba... Gamayya ce ta masu neman muƙami...
21/03/2025

Sabuwar Jam'iyyar Maja Ta Su EL-RUFAI DA ATIKU Yaudara Ce Ba Talakawa Ne A Gabansu Ba
... Gamayya ce ta masu neman muƙami da mulki da neman takara, ba al'umma ko talakawa ne a gabansu ba.

Ya ku al’ummar Arewa, ku dubi halin da ake ciki ku tambayi kanku, shin har yanzu za mu ci gaba da bari wasu ‘yan siyasa su rika amfani da mu don biyan bukatunsu? Yanzu da aka saka dokar ta ɓaci a Jihar Rivers, sai gashi Nasiru El-Rufai da Atiku Abubakar sun hada kansu da wasu domin su caccaki gwamnatin Tinubu.

Ina s**a kasance lokacin da ake kashe al’ummar mu a Kaduna, Katsina, Zamfara, Kebbi da Sokoto? A lokacin da aka yi ta satar mutane, garkuwa da su, da hallaka iyayenmu da ‘ya’yanmu, ina ku ke? El-Rufai, kana gwamnan Kaduna, lokacin da garkuwa da mutane ya zama ruwan dare a jiharka, ba ka taba yin taron manema labarai domin nuna damuwarka ba. Atiku, lokacin da kake cikin gwamnati a baya, ba ka taba kokarin kawo mafita ga Arewa ba.

Amma yau da aka cire gwamnan Rivers, sai gashi kun fito kuna ihun adalci! Shin, lokacin da kuka ke mulki Atiku yana mataimakin shugaban kasa, ba kun cire gwamnonin jihohi k**ar Bayelsa da Plateau ba? El-Rufai da Atiku, lokacin da kuka ke mulki a zamanin Obasanjo, har gwamnonin jihohi uku kuka tsige! To me yasa a lokacin hakan ya zama daidai, amma yanzu da Tinubu ya yi, sai ku ce rashin adalci ne? To menene banbancinku da shi Tinubu ɗin, ko dan shi daga Kudancin Najeriya yake, ku kuma daga Arewa?

Shin me kuka yi lokacin da aka cire tallafin man fetur? Me yasa baku taba yin magana ba lokacin da aka jefa talaka a cikin wahala? Domin kun san cewa baku ne za ku sha wahalar ba, shiyasa kuka yi shiru. Amma yanzu da bukatarku ta taso, sai gashi kun fara taron manema labarai da shirye-shiryen kafa wata jam’iyyar maja.

Atiku da El-Rufai, kuna son sake hada wata jam’iyyar maja domin me? Ba ku ne kuka kafa APC ba? Ba ku ne kuka ce ita ce mafita ga Najeriya ba? Yanzu da ku ka gaza cimma burin ku, sai ku dawo kuna kokarin yaudarar mutane da wata sabuwar jam’iyyar?

Ya ku ‘yan Arewa, muna gane wasan waɗannan mutanen, ka da mu sake bari su yi amfani da mu don biyan bukatunsu karshe su watsar damu. Mun koyi darasi daga baya, kuma wannan karon, ba za mu bari su yi amfani da mu ba!

Haɗin Gwiwa Don Cigaban Kasa..... Mai Girma Ministan Tsaro ya gana da Ministan Kudi domin inganta hadin kai tsakanin ma’...
21/03/2025

Haɗin Gwiwa Don Cigaban Kasa
..... Mai Girma Ministan Tsaro ya gana da Ministan Kudi domin inganta hadin kai tsakanin ma’aikatun gwamnati don inganta tattalin arzikin kasa da tsaro

Mai Girma Ministan Tsaro, H.E. Mohammed Badaru Abubakar, CON, mni, ya kai ziyarar girmamawa ga Mai Girma Ministan Kudi, Mista Adebayo Olawale Edun, a ofishinsa da ke Ma’aikatar Kudi ta Tarayya, Abuja, a yau Juma’a, 21 ga Maris, 2025. Taron ya mayar da hankali ne kan karfafa hadin gwiwar ma’aikatu don ci gaban kasa.

Najeriya Za Ta Samar Da Sabbin Dabarun  Kwarewa Kan Tsaro, Noma da Hadin Gwiwar Soji da Bangladesh – BadaruMinistan Tsar...
21/03/2025

Najeriya Za Ta Samar Da Sabbin Dabarun Kwarewa Kan Tsaro, Noma da Hadin Gwiwar Soji da Bangladesh – Badaru

Ministan Tsaron Najeriya, Mai Girma Mohammed Badaru Abubakar CON, mni, ya bayyana cewa Najeriya za ta raba kwarewa da Bangladesh a bangaren tsaro, noma da hadin gwiwar soji.

Wannan hadin gwiwar zai ba da damar shigar da jami’an soja cikin wasu sassan da ba na yaki ba, k**ar noma, gine-gine, da ci gaban ababen more rayuwa.

Manufar wannan tattaunawa ita ce tabbatar da cewa jami’an soja suna da ayyukan da za su rika yi a lokutan da ba a fuskantar yaki, wanda hakan zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikinsu da kuma ci gaban kasa gaba daya.

Tattaunawar hadin gwiwar ta gudana ne yayin ziyarar girmamawa da Mansur Rahman, Jakadan Bangladesh a Najeriya, ya kai a Ship House, Abuja. Taron ya jaddada damar da ke akwai na amfanuwa daga irin wannan musayar kwarewa tsakanin kasashen biyu.

Minista Badaru ya jaddada cewa wannan hadin gwiwa a fannin tsaro da noma zai ba wa jami’an soja damar yin ayyukan da za su bunkasa basirarsu da kuma ci gaban al’ummarsu.

A nasa jawabin, Jakadan Bangladesh, Mansur Rahman, ya nuna goyon bayansa ga wannan tsari, yana mai cewa shigar da jami’an soja cikin ayyukan farar hula zai taimaka wajen dorewar ci gaba da daidaiton tattalin arziki. Ya kuma bayyana cewa hadin gwiwar bangaren tsaro na iya taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa tattalin arziki na Najeriya.

Wannan hadin gwiwa yana nuni da jajircewar Ma’aikatar Tsaro wajen kirkiro sabbin dabaru da za su inganta rayuwar jami’an soji da kuma ci gaban Najeriya gaba daya.

Mati Ali
PA Media & Publicity to the Hon. Minister

Address

Pantami Hurumin Da'u Quaters
Gombe

Opening Hours

Monday 06:00 - 12:00
Tuesday 06:00 - 12:00
Wednesday 06:00 - 12:00
Thursday 06:00 - 12:00
Friday 06:00 - 13:00
Saturday 06:00 - 12:00
Sunday 06:00 - 13:00

Telephone

+2348125747767

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Arewa Media Watch posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Arewa Media Watch:

Share