14/08/2025
Majalisar zartarwa ta ƙasa Ta Dakatar da Kafa Manyan Makarantu har tsawon shekaru 7 don Inganta Wanda Ake Dasu
Majalisar zartarwa ta ƙasa (FEC) ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta amince da sanya takunkumin shekaru bakwai kan kafa sabbin manyan makarantu na gaba da sakandare na tarayya a faɗin ƙasar. Wannan ya haɗa da jami’o’i, kwalejojin fasaha da kwalejojin ilimi. Ministan Ilimi, Tunji Alausa, ya bayyana cewa matsalar da ake fuskanta a fannin ilimi yanzu ba ta samun damar shiga makarantu ba ce, sai dai yawan maimaita kafa sababbin makarantu ba tare da isasshen kayan aiki da ma’aikata ba, wanda ke rage ingancin ilimi da lalata darajar da ɗaliban Najeriya ke da ita a idon duniya.
Alausa ya ce akwai jami’o’i na tarayya 72, na jihohi 108, da masu zaman kansu 159, haka kuma akwai irin wannan yawaitar a kwalejojin fasaha da na ilimi, gami da wasu cibiyoyi kamar monotechnics, kwalejojin noma, na kiwon lafiya da makamantansu. Ya bayyana cewa a wasu makarantu adadin ɗaliban da ke nema ya ragu ƙwarai. Haka ma a kwalejojin fasaha 295 da kwalejojin ilimi 219, inda wasu daga ciki basu samu ɗalibi ko ɗaya ba, lamarin da ke nuna asarar kuɗaɗe da rashin inganci.
Ya ce akwai misali daga arewacin ƙasar inda wata jami’ar tarayya ke da ƙasa da ɗalibai 800 amma tana da ma’aikata fiye da 1,200, wanda ya kira da abinda ba zai ɗore ba. Bisa haka, gwamnati ta dauki matakin takaita kafa sababbin makarantu domin maida hankali wajen inganta waɗanda ake da su, ta hanyar ƙara ƙarfin su, gyara kayan aiki da samar da ƙwararrun malamai. Ya ce manufar ita ce a ƙara ingancin ilimi, don tabbatar da cewa ƙasashen duniya na ci gaba da girmama digirorin Najeriya.
Sai dai duk da takunkumin, FEC ta amince da kafa sabbin jami’o’i masu zaman kansu guda tara wanda s**a daɗe a hukumar Jami’o’i ta kasa (NUC) kimanin shekaru shida. An kammala gina makarantun tuni da saka jarin biliyoyin naira. Alausa ya kuma ce an yi garambawul ga ka’idoji guda 350 ba sa aiki aiki a baya, kuma daga yanzu duk makarantar da za a kafa, ko ta gwamnati ko mai zaman kanta, ba zata samu amincewa ba sai ta cika sabbin sharuddan. Ya gargadi cewa idan ba a dauki mataki ba, yawan rashin aikin yi ga matasa zai ƙaru, kuma hakan zai rage tasirin digirin Najeriya a duniya.