HRB Hausa News

HRB Hausa News Advertising

07/11/2021
30/10/2021

Shahararriyar jarumar wasan kwaikwayo wanda fitowa a matsayin uwa a cikin fina-finan masana’antar kannywood wato, Saratu Daso, ta wallafa wata bidiyo wanda ta janyo mata …

25/10/2021

Kada Allah Yasa 'ya'yana su zamo Jaruman Fim - Ummi zee zeezee, wannnanwannnan furucifurucinafurucifurucina, Ummi zeezee zeezee

19/10/2021
19/10/2021

Mukaddashin Kwanturola janar na hukumar shige da fice ya kame jami'ansa da kokarin aikata barna akansa. Sun nemi ya basu kudi cikin rashin sani basu san shi ban

19/10/2021

Marigayi Mai Shari'a Muhammadu Bello Dan Arewacin Nijeriya Na Farko Da Ya Zama Lauyan Sarauniyar Ingila (Queen's Counsel) Wanda Ya Yi Dai-dai Da Babban Lauyan Najeriya (SAN) A Halin Yanzu A Shekarar 1961

Allah Ya Jikansa Da Rahama!

11/10/2021

Daliban makarantar koyon larabci da alkur'ani a jihar Kwara, sun maida martani kan mummunan azabtarwar da malamai s**a musu sabida sun halarci shagalin party.

09/10/2021

Duk Wanda Ba Ya Maulidin Manzon Allah (S.A.W) Ba Musulmi Ba Ne - Cewar Prof. Maqari

Daya daga cikin ma su jan ragamar babbar masallacin Abuja, kuma babban malami mai bin mazhabar qadriyya, Prof. Maqari ya yi tsokaci akan tatamurzan bukin maulidin da a ka dade ana kumfar baki akai na nuna murna da samuwar fiyayyen halitta Manzon Allah (S.A.W) yanda ya bayyana cewa ai duk wanda ba ya maulidin, to shi ba musulmi ba ne.

A wani gajerin bidiyo da ya ke ta yawo a kafofin sada zumunta, jaridar Manuniya ta hango babbar malamin, mai bin mazhabar qadiriyya ya na furta cewa ai duk wanda ba ya maulidi, to shi ba musulmi ba ne.

A zancensa ya na cewa;"Duk wanda ba ya yin Maulidin Manzon Allah (S.A.W) ba Musulmi ba ne. Ina yawan fadin wannan, domin maulidi shi ne mujarradin murnar samuwar Manzon Allah (S.A.W). Da ka yi murna da samuwar Manzon Allah (S.A.W), ko cikin zuciyarka, ka yi maulidi - shi kuma ya ya ka aiwatar da murnar, shi ne a ke samun banbanci. Hanyar, ranar sha biyu ga wata a ciyar da abinci a yi kaza, wannan fahimtar wasu ne. Idan ka ce baka yarda da wannan hanyar ba, ijitihad..."

Maulidi dai buki ne da Al'ummar Musulmai su ke gudanarwa shekara-shekara domin nuna murnansu na samuwar fiyayyen halitta, Manzon Allah (S.A.W). Amma, wasu kaso daga cikiñ Musulmai su na alakanta bikin da "Bidi'a" saboda Manzon Allah bai ce a yi ba kuma sahabbansa ba su yi ba.

A gefe daya kuma, akwai wanda su ka nuna yin maulidin ya na da kyau sai dai yanda a ke gudanar da shi ne yanzu Sam bai kamata ba; cakuduwar maza da mata ana rawa da rairaya da kuma samar da dandazon mutane ta hanyar yin ma su lakabi munana irinsu; Nigogin Manzon Allah, yan barandan Manzon Allah da dai sauransu.

Address

Dawaki
Gombe
HRB

Telephone

+2349066084151

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when HRB Hausa News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to HRB Hausa News:

Share