20/08/2026
Innā lillāhi wa innā ilaihi rājiʿūn. 😭😭
Allah Ya karɓi rayuwar Khalifa Sheikh Muhammadul Eid At-Tijani At-Tamasini, wanda yake daga cikin manyan shugabannin Tijjaniyya, kuma Sheikh na Zawiyar Tamasini.
Rasuwar tasa babban rashi ce ga ‘yan uwa da almajiran Ɗariƙar Tijjaniyya, musamman waɗanda suke da alaƙa da Tamasini da kuma Ain Madhi.
Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta masa, Ya jiƙansa da rahamarSa, Ya sanya shi cikin bayinSa salihai, Ya ɗaukaka darajarsa, Ya kuma ba iyalansa da almajiransa haƙurin jure wannan babban rashi.
Allah Ya gafarta masa, Ya sa Aljanna ce makomarsa. Amīn, Yā Rabbal ʿĀlamīn.