11/09/2021
Sarkin Obajana Engr. Dr Idowu Isenibi, Oba Of Obajana Ya Bawa Musulman Garin Obajana Makeken Fili Hetka 10 Domin Ya Zama Maƙabarta Ga Al-ummar Garin, Bayan Ruwan Sama Ya Lalata Tsohuwar Maƙabatarsu
Daga Ƙungiyar "Arewa Media Writers"
Idan baku manta ba, a farkon wannan watan ne Ƙungiyar marubutan Arewa a kafofin sadarwar zamani "Arewa Media Writers" ta fitar da Rahoton neman taimako ga Al-umma kan wani Ruwa mai ƙarfi da aka yi a garin Obajana, wanda yayi sanadiyyar ambaliya a ƙoramu, har ruwa ya gangara cikin maƙabartar garin, Maƙabartar ta zama cikin ruwa tare da tone ƙaburbura sama da 100.
A jiya Lahadi Ƙungiyar "Arewa Media Writers" reshen jihar Kogi ta halarci taron ziyarar godiya zuwa fadar sarkin Obajana Engr. Dr Idowu Isenibi, Oba of Obajana akan gudumuwar da ya bawa musulman garin obajana.
Sarki Engr. Dr. Idowu Isenibi, ya tarbi al-ummar garin hannu biyu-biyu kuma yaji daɗin wannan ziyara kuma yayi Addu'a da fatan zaman lafiya a yankin mu na Arewa dama ƙasar mu Najeriya baki ɗaya.
Sarkin yayi alhini na ibtila'in da ya faru da musulmai na lalacewar maƙabartar su.
Wannan dalilin yasa Sarki Engr Dr. Idowu Isenibi Idowu Isenibi, ya bawa Musulman garin Obajana makeken fili Hetka 10 wato 150×150 guda tamanin 80 a matsayin maƙabarta ga muslim society na Obajana.
Mutane da dama sun taimaka sanadiyar kai koken su ga al-umma da manyan ƙasar da Ƙungiyar "Arewa Media Writers" tayi wanda zuwa yanzu an samu kuɗi da s**a kai kimanin Naira Miliyan Ɗaya da Rabi 1,500,000.
Oba na Objana Engr Dr. Idowu Isenibi, ya bada takardar fili ga sarkin Hausawan Obajana da limaman masallatan Obajana.
Shuwagabanni da Limaman Obajana sun yiwa Sarki Addu'a ta ɗaukaka da zaman Lafiya a ƙasar dama yankin mu na Arewa dama ƙasar mu baki ɗaya.
Rubutawa✍️✍️✍️
Abu Bilal Dan Majema,
Chairman "Arewa Media Writers" Kogi State Chapter.