04/07/2025
🌑 Abubuwan Da S**a Faru Ranar 9 Muharram (Tasu'a):
A wannan rana, rundunar Umar ibn Sa’ad ta soma shirye-shiryen kai hari kan Imam Husain (AS) da mutanensa. Sun yi niyyar kammala yaƙin kafin daren 10 ga Muharram.
Imam Husain (AS) ya tura ɗan'uwansa Abbas ibn Ali da wasu daga cikin sahabbansa su je su roƙi Umar ibn Sa’ad ya ba su dama su kwana ɗaya, domin su yi ibada, addu'a da istighfari kafin su fuskanci yaƙi.
Imam Husain ya ce:
"Ina son mu kwana mu gabatar da salla, mu yi addu'a da istighfari. Allah ya san cewa bana son komai kamar salla da karatun Qur’ani da yin addu’a da istighfari.”
Umar ibn Sa’ad ya amince da hakan bayan ya nemi izini daga Ibn Ziyad (wakilin Yazid a Kufa).
Imam Husain (A.S) da sahabbansa sun yi taro domin karfafa juna da tuna alkawari da aminci. A cikin daren ne Imam Husain ya ba sahabbansa izinin su gudu, yana cewa:
"Dukkan ku an bar ku ku tafi, babu wani alkawari a wuyanku. Ku ceci rayukanku. Wadanda muke fuskantar mu suna da niyyar kashe ni ne kawai.”
Amma duk sahabbansa sun ki barinsa, suna cewa:
"Wallahi, da za a kashe mu sau ɗaya, a kona mu, a yayyafa turɓaya, a tashi mu sake kashe mu har sau dubu, ba za mu bar ka ba."
Wannan daren ya kasance cike da tsarki da ibada. An ce ba abinda ake jiyowa a tentin Imam Husain da na sahabbansa sai sautin karatun Qur’ani, salla, da tasbihi kamar karar saukar tsuntsaye.
Abubuwan Da Aka Fuskanta a wannan rana ta 9 ga Muharram.
Tsananin ƙunci da ƙishirwa, domin an hana su ruwa tun daga rana ta 7 ga Muharram.
Tsoron kai hari a cikin dare, don haka aka tsaurara tsaro a kusa da zirin tentin su.
Tabbatar da aminci da cika alkawari daga dukan sahabbai, musamman daga Ahlul Bayt, irin su Abbas, Ali Akbar, Qasim, da sauransu.
Ranar Tasu’a ta kasance rana ta shiri, juriya, da ibada, kafin fuskantar shahada da yaƙi a gobe (Ashura). Tana nuna yadda Imam Husain da mabiyansa s**a kasance masu ƙarfin zuciya, tawakkali, da tsantsar imani.😭
WA HUSSAIN.
Abban Imamu ✍️