29/05/2025
JAWABIN DA MAI GIRMA GWAMNAN JIHAR GOMBE, MUHAMMADU INUWA YAHAYA YA YI TA KAFAFEN YADA LABARAI KAI-TSAYE GA AL`UMAR JIHAR YAYIN BIKIN CIKAR SA SHAKARA SHIDA YANA JAGORANCI, A RANAR ALHAMIS 29 GA WATAN MAYUN 2025
Ya Yan Uwana al`ummar jihar Gombe,
2. Godiya ta tabbata ga Allah da ya nuna mana wannan lokaci da muke bikin cikar wannan gwamnatin shekara shida da kafuwa. Shekaru shida da s**a wuce kuka b ani amanar jagorantar wannan jihar tamu. Haka kuka sake jaddada wannan amanar a shekara ta 2023. Ina godiya matuka dangane da wannan amincin da kuka nuna mini.
3. Yayin da muke wannan biki, yana da kyau mu lura cewa a sannu ni ma nafara bankwana da wannan kujerar a matsayin Gwamna, kasancewar mun cinye kusan kashi saba`in da biyar cikin dari na wannan wa`adin Mulki. Saboda haka, dan lokacin da ya rage, za mu sadaukar da shi ne wajen ninkawa a kan gagarumin cigaban da aka samu ta yadda jihar Gombe za ta ci gaba da habaka da bunkasa fiye da kowane lokaci.
4. Lokacin da muka karbi ragamar Mulki shekaru shida da s**a wuce, mun yi alkawarin cewa za mu mayar da Gombe abar misali a fannin cigaba, kuma cikin yardarm Allah mun yi nasarar cika wannnan alkawarin. Lungu da sako babu inda aikin alherin da muke yi bai kai ba.
5. Gwamnatinmu ta cimma nasarori a bangaren kiwon lafiyar al`umma. A shekara ta 2020, mun kaddamar da wani gagarumin shiri na inganta harkar kiwon lafiya, inda muka gina asibiti guda tare da wadata shi da kayan aiki a kowace gundumar jihar nan su 114, sannan muka dauki jami`an lafiya su 440, da jami`an ungozoma 145, wadanda aka kai su wuraren da ake matukar bukatarsu domin kyautata harkar karbar haihuwa. Haka muka matsa-kaimi, mun yunkura za mu ninka abin da muka yi. Mun dukufa wajen sake gina karin sabitoci 114 , wanda zai ba mu adadin asibitoci 228 a sassa daban-daban na jihar Gombe. Kazalika mun daga darajar manyan asibitocinmu. Misali, mun sauya fasalin babban asibitin Gombe. An yi garambawul ga babban asibitin Bajoga da na Kaltungo. Ga asibitin Kumo da muka sake gina shi dungurungum muka makare shi da kayan aiki na zamani, har shugaban kasa Bola Tinubu ya daga martabarsa zuwa babban asibitin tarayya, wato Federal Medical Center.
6. A kokarin maganace matsalar karancin jami`an kiwon lafiya, mun gina sabuwar makarantar koyon aikin jinya mai daukar dalibai 1000. Mutum 369,817 ne suke cin gajiyar shirin mu na inshorar lafiya ta Go-Health, ciki har mutum 100,000 marasa galihu da ake kula da su kyauta. Harwayau, mun kara bunkasa harkar kiwon lafiya ta hanyar kafa wasu hukumomi masu muhimmancin gaske, da s**a hada da Hukumar da ke kula da asibitocin jihar Gombe, da Hukumar da ke samar da magunguna da kayan aikin asibiti ta jihar Gombe (GODMA). Wannan mataki da aka dauka ya samar da kyakkyawan sak**ako, ya taimaka gaya wajen inganta harkar riga-kafi, wanda ya karu da fiye da kashi 100 cikin 100. Misali, adadin riga-kafin da ake yi a shekarar 2018 bai wuce kashi 18 cikin dari ba, sai ga shi adadin zangonriga-kafin ya karu zuwa kashi 49 cikin dari a shekarar 2023, k**ar yadda alakaluman Hukumar da ke kula da kididdgar harkokin kiwon lafiya ta kasa s**a nuna, lamarin da yam ai da jihar Gombe ta zama abin koyi a fannin inganta kiwon lafiya.
7. Matakan da muka dauka na yin garambawul a bangaren ilimi ma sun samar da kyakkyawan sak**ako a dukkan bangarori. Azujuwan da muka gina sababbi da wandada muka yi musu kwaskwari sun kai fiye da 1,600 a makarantu 350. Sannan mun dauki malamai kwararru 1000 da nufin inganta harkar koyarwa. A Shirin BESDA mun yi nasarar rage yaran da ke gararamba ba sa zuwa makaranta mutum 350,000, wadanda s**a koma bakin karatu. Don tabbatar da dorewar wannan tsarin, muna gina tsangayoyi na zamani a kowace karamar hukuma, ga kuma Mai bai wa Gwamna shawara a kan karatun tsangaya da gwamnati ta nada, kuma nuna shirin kafa hukumar da zata kula da kaatun almajirai, alamar da ke nuna hikimar gwamnati ta surka karatun addinin musulunci da na boko.
8. A matakin karatun sakandare, mun gina manyan makaratun sakanadare sha-kundum (Mega College) guda biyar wadanda aka wadata su da kayan aiki. Mun kuma kafa hukumar da ke kula da makarantun sakandare don tabbatar da cewa suna samun kulawa sosai. Tsarin da muka yin a tilasta wa yara rubuta jarrabawar gwaji ta kammala karatun sakandare kafin a biya wa dalibai kudin rubuta jarrabawar kammala karatunsu yana taimakawa sosai wajen inganta karatunsu, kuma kwalliya tana biyan kudin sabulu, saboda sak**akon wannan tsarin kimanin kashi 76 cikin dari na daliban da ke rubuta jarrabawar suna samun adadin makin da ake bukata don shiga manyan makarantu, wato darusa biyar, ciki har da lissafi da Ingilishi (Turanci), sabanin shekara ta 2019, wanda a wancan lokacin adadin daliban da ke samun kyakkyawan sak**akon ba ya wuce kashi 22 cikin dari. A bangaren manyan makarantu, mun kara yawan kudin da muke bai wa Jami`ar Jihar Gombe, da sauran makarantun gaba da sakandare sannan mun kafa wasu muhimman tsagayoyi guda biya a karkashin jami`ar, wato da Kwalejin Nazarin kimiyyar Muhalli da ke Dukku da kuma Kwalejin kimiyyar aikin gona da ke Kwami. Mun yi haka ne domin mu tunkari kalubalen da ake fuskanta na samar da isasshen abinci da fafutukar raya biranenmu da muhalli.
9. Wadannan matakan sun daga martabar jihar Gombe ta sha gaban sauran jihohi a fannin kirkirar hanyoyin inganta ilimi, har ta kai ga ma`aikatar ilimi ta gwamnatin tarayya da sauran hukumomi da kungiyoyi abokan tafiya suna yaba wa jihar Gombe dangane da tsare-tsare da dabaru daban-daban da take amfani da su wajen inganta harkar ilimi.
10. A bangaren gina hanyoyin mota ma gwamntinmu sai sambarka! Mun samar da hanyoyi masu yawa ta Shirin nan na gina hanya akalla kilomita dari (100) a kowace karamar hukuma a jihar Gombe. Kuma a cikin wannan Shirin mun yi nasarar gina hanya kilomita 900 a yankunan karkara da biranen jihar Gombe. Wadannan hanyoyin mota sun saukaka zirga-zirga da sada zumunci, sun bunkasa tattalin arziki. Mun maida hankali ne wajen gina hanyoyi a muhimman yankunan da gwamnatocin baya s**a yi watsi da su. Alal misali, hanyar DegriβTalasse, da BambamβTula Yiri, da MalalaβZange, da MonaβKutare, da Tashan MagaryaβPapa, da Kuri-Lambam DasaβTalasse. A cikin kwaryar fadar jiha ma mun samar da hanyoyi ga al`ummomin da s**a dade suna nema k**ar su al`ummar Tunfure, da Nayinawa, da Mallam InnaβKagarawal, da Arawa don inganta rayuwarsu.
11. Bugu da kari, mun Sanya wutar sola a kan dukkan hanyoyin motar da muka gina, kuma hakika wannan wutar tana taimakawa wajen haska hanyoyin idan dare ya yi, kana tana inganta tsaro. Hanyar ratsen nan mai tsawon kilomita 20, wadda aka tsara za ta tashi daga hanyar zuwa Potiskum da zagaya gefen gari ta dangana da har zuwa Biu kadai ta isa babban misali .
12. Gwamnatin ta mayar da Gombe jiha ta farko da ta kasance cibiyar masana`antu a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya sak**akon gandun masana`antu mai hekta 1,000 da take bunkasawa. Bayan haka, muna kokari mu ci amfanin noman rani da arzikin Allah ya mana na madatsar ruwa da ke Dadinkowa da Balanga. Nan ba da dadewa ba za mu fara aikin gina gandun hada-hadar amfanin gona mai hekta 184 wadda za ta hada `yan kasuwa na gida da na wajen Najeriya, da kasuwar dabbobi ta kasa da kasa da kuma kwata ta zamani. Da yardar Allah, wadannan abubuwa za su daga martabar Gombe ba shiyyar arewa maso gabas kadai ba, har a arewacin Najeriya baki daya, saboda za ta kasance a gaba a fannin hada-hadar amfanin gona da kasuwanci. Daga nan kuma sai hanyar samun arziki ta bude wa al`ummar jihar Gombe.
13. Sana`ar noma ita ce ginshikin tattalin arzikinmu, kuma ita ce hanyar da mafi yawan al`ummarmu s**a dogara da ita wajen biyan bukatun rayuwa. Cikin shekarun shidan da s**a wuce, gwamnatinmu ta ba da fifiko wajen tallafa wa manoma da makiyaya ta hanyar samar da takin zamani da kayan aikin gona. Kazalika ana yi wa dabbobi huji, sannan gwamnati tana daukan matakai don magance rikici tsakanin manoma da makiyaya. Yanzu dai da irin muhimman ayyukan da gwamnati ta sa a gaba, irin su gina makwararin ruwa don noman rani a madatsar ruwa ta Balanga, da cibiyar masana`antu majibanta amfanin gona da ke tafe da Sanya Gombe da aka yi a a cikin cibiyoyin sarrafa amfanin gona , babu shakka Gombe za ta samu gagarumin cigaba a harkar noma. Bayan habaka harkar noma, yanayin zai taimaka wajen samar da aikin yi ga miliyoyin jama`a tare da bunkasa tattalin arzikinsu.
14. Matakin da gwamnatinmu ta dauka na kafa hukumar taswirar kasa ta GOGIS da hukumar tsarawa da raya birane ta GOSUPDA ya taimaka gaya wajen bunkasa harkar raya birane a jihar Gombe. Kuma suna taka rawa wajen zamanantar da harkar filaye tare da tabbatar da cewa ana bin ka`ida. Manyan ayyuka k**ar bunkasa gundumar Shehu Abubakar da sauran ayyukan da ake yin a tsara birane suna nuna dukufar da muka yi wajen girka tsari mai dorewa na inganta harkar raya birane. Yayin da Gombe ke cigaba da habaka da bunkasa, akwai bukatar a ta dinga habaka bisa kykkyawan tsari ta yadda za ta dinga tafiya da martaba irin ta manyan birane.
15. Wadannan ayyuka da tsare-tsaren da muke yi daban-daban sun taimaka wajen samar da daddadan yanayin kasuwanci da bunkasar tattalin arziki. Wannan ne ma ya sa Gombe ta kasance ta daya Najeriya ta fuskar saukaka hanyar yin kasuwanci a shekara ta 2021 da 2022. Rattaba hannun da nayi a kan dokar samar da wutar lantarki ishara ce da ke nuna cewa mun yi haramar samar da kasuwar mak**ashi a jihar Gombe, wadda za ta taimaka wajen kawo karshen karancin mak**ashi. Daga nan sai masana`antu su yi ta habaka. Ana sa ran hukumar habaka jari ta jihar Gombe za ta shige gaba wajen kawo sauye-sauye a harkar zuba jari, tare da bude hanyar cin gajiyar kafofi daban-daban na zuba jari da Allah ya huwace wa jihar nan.
16. Batun shawo kan kalubalen da da ya shafi muhalli na cikin manyan bangarorin da gwamnatinmu ta maida hankalinta. Muna dawainiya sosai ta kashe kudi da lokaci wajen raya muhalli ta hanyar dashen miliyoyin itatuwa a cikin Shirin nan na 3G (Gombe ta yi shar-shar). Harwayau, ta Shirin NEWMAP da ACReSAL, mun karya-lagon zaizayar kasa, mun dauki matakan raya wuraren da zaizayar kasa ke cinyewa a jihar Gombe. Miuna yaki da manyan kwarurruka irin na FCE(T), da Jami`ar jihar Gombe da makarantar sakandaren mata, ko Mega College ta Doma da Hayin Kwarin Misau. Muna fadi-tashi ne da nufin kare muhalli da inganta rayuwar al`ummar mu.
17. A cikin shekaru shidan da s**a wuce, gwamnatinmu ta cimma nasara mai yawa a bangaren samar da ruwan sha ta hanyar gina rijiyoyin burtsatse fiye da dari takwas (800), sannan ta aiwatar da aikin nan na yalwata ruwan sha a fadar jiha da kewaye. A kokarin da muke yi samar da ruwan sha a kananan hukumomi, muna hada gwiwa da gwamnatocin kananan hukumomi don aiwatar da wani shiri mai dorewa na samar da ruwan sha. Bayan samar da ruwan sha mun dukufa wajen inganta tsabta ta hanyar gina wuraren ba-haya da zuba shara. Sannan muna karfafa hukumar da ke kula da tsabtar muhalli ta GOSEPA don kyautata aikinta na kwashe shara da tsabtace muhalli.
18. Gwamnatinmu ta tabbatar wa duniya irin dukufar da ta yi wajen kyautata walwalar ma`aikata, musamman ma irin hobbasar da ta yi wajen amincewa da biyan albashi mafi kankanta a kan kari. Ga kuma tsabar kudin da ta kashe wajen biyan kudin sallamar ma`aikata da ta gada da ya kai sama da naira biliyon 21, domin ma`aikatan da s**a yi ritaya su ji dadin rayuwarsu. Ta Hukumar Inganta Aikin Gwamnati, muna aiki wurjanjan na kyautata aikin gwamnati ta hanyar horar da ma`aikata tare da zamanantar da kayan aiki. Wasu daga cikin manyan abubuwan da gwamnatinmu take musu sun hada da gina sabuwar majalisar dokoki da rukunin manyan kotunan jiha da babbar Sakatariya da za ta kunshi ma`aikatu da hukumomin gwamnatin jiha. Yin wadannan gine-gine da samar da kayan aiki za su taimaka wajen samar da daddadan yanayi na aikin gwamnati, sannan aiki ne da ake yi mai nagarta wanda hatta al`umomi masu tasowa za su ci gajiyarsa.
19. Harwayau, gwamnatinmu ba ta manta da al`adunmu na gargajiya ba. Farar aniyarmu ta fito fili ko daga aikin da muke yi na ginawa da kwaskwarima ga gidajen sarakuna a sassa daban-daban na jihar nan. Manufar daukan wannan mataki ita ce a tabbatar da cewa manyan sarakuna da hakimanmu sun kasance a gidaje masu Daraja da s**a dace da martabarsu. Kazalika mun kafa wani kwamiti da aka dora masa alhakin adana wuraren tarihi da kayan al`adunan gargajiya na al`umomin jihar Gombe. Wadannan matakai muna daukansu ne domin kare martabar al`adunmu.
20. Muna ba da fifiko sosai ga harkar tsaro, ganin cewa ba a samun cigaba mai dorewa idan ba tsaro. Ina alfahari da jihar Gombe kasancewar ana zaman lafiya daidai gwargwado duk kuwa da irin kalubalen tsaron da ake fama da shi a shiyyar arewa maso gabashin kasar nan. Wannan yana nuna irin jajircewar al`ummarmu da kuma irin hadin kan da muke da shi. Muna samun wannan nasarar ne sak**akon kokarin da muke yi wajen k**anta adalci da daidaito ga kowa da kowa. Muna samun nasara ta hanyoyin da muke bi na inganta zaman lafiya da fahintar juna a wannan jihar , ciki har da hukumar da ke kula da zirga-zirgar masu abun hawa GOSTEC) da dabarun sasanta tsakanin al`umma daban-daban, da kuma tallafin motoci da kayan gudanarwa da muke bai wa hukumomin tsaro.
21. Ya al`ummar jihar Gombe, cikin shekaru shidan da s**a wuce, shekaru ne da aka nuna juriya da hadin kai da sauye-sauyen cigaba. Tare muka jure, tare muka yi fadi-tashi lokacin da aka shiga iftila`in annobar korona da komadar tattalin arzki. Haka cikin ikon Allah muka gudu tare, muka tsira tare. Wannan nasarar da aka cimma taku ce, al`ummar jihar Gombe masu kwazo da himma. Ina godiya ga kowa da kowa.
22. Yayin da muke wannan biki, yana da kyau mu dinga tunawa cewa cigaban jihar Gombe hakki ne da ke wuyan kowa da kowa, wanda kuma yake bukatar gudummuwar kowa da kowa ba tare da la`akari da bambancin addini ko kabila ko kuma siyasa ba. Irin gadon da muke fatan bari ba
don mutane kalilan ba ne, gado ne na kowa da kowa, da wadanda suke raye da kuma wadanda za a Haifa nan gaba.
23. cikin shekaru masu zuwa za mu zage-dantse wajen ganin mun kyautata tsarin da muka yi don cin gajiya a fannin kasuwanci da noma da samar da mak**ashi. Za mu karfafa hukumominmu ta yadda za su dinga k**anta gaskiya da shugabanci nagari. Sannan za mu cigaba da bunkasa matasanmu ta hanyar koya musu sana`o`I da share musu hanyar cigaba a rayuwa.
24. A daidai wannan lokacin ina mika godiyata ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu dangane da irin goyon bayan da yake ba mu da kuma jagoranci da hangen nesan sa da yake tasiri a kan cigaba da muke samu. A bangare guda kuma ina godiya ga majalisar dokokin jihar Gombe da bangaren Shara`a sak**akon hadin kai da fahintar junan da ke tsakaninmu. Ina godiya ga sarakunanmu, da shugabannin addini da shugabannin al`umma da jagororin siyasa, da kungiyoyin farar-hula. Muna godiya dangane da irin hadin kai da goyon bayan da kuke ba mu. Yayin da muke shiga zangon karshe na wannan gwamnatin muna godiya matuka sak**akon goyon bayan da kuke ba mu a daidai wannan lokacin da muka dukufa wajen ciyar da jihar Gombe gaba.
25. Ya al`ummar jihar Gombe. Tafiya ta riga ta yin isa, ba maganar komawa da baya! Tubalin da muka aza yana da karfin gaske. Amma duk da haka da sauran aiki. Ya k**ata mu cigaba da tafiya da irin hadin kai da himma da jajircewar da muka yi da ya nauso mu zuwa wannan matakin. Idan muka cigaba da hadin kai za mu cigaba da samun nasara fiye da yadda ake tsammani, sai mu daukaka jiharmu, wadda tauraruwarta ke haskakawa a Najeriya.
26. Na gode da adu`a da goyon bayan da kuke ba mu. Da yardarm Allah da irin goyon bayan da kuke ba mu, Allah ne kadai ya san irin nasarorin da ke jiran mu.
27. Na gode.
Allah ya daukaki jihar Gombe da Najeriya baki daya!