25/09/2025
25/09/2025
Gwamnan Gombe Ya Yi Farin Ciki da Ƙarin Girman da Aka Yiwa Kupan Amos Zuwa Matsayin Mataimakin Babban Kwanturolan Gidajen Kaso
Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya, CON, ya bayyana matuƙar jin daɗinsa kan ƙarin girman da Dakta Kupan D. Amos, mni ya samu zuwa muƙamin Mataimakin Babban Konturolan Hukumar Gyaran Hali ta Najeriya.
A yau Alhamis ne Ministan Harkokin Cikin Gida, Hon. Olubunmi Tunji-Ojo ya liƙawa jami'in tambarin ƙarin girman biyo bayan amincewar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, bisa shawarar da Hukumar kula da Rundunar Tsaro ta Civil Defence, data Gidajen Yari, da Kwana-kwana da Hukumar Shige da Fice Imagireshan (CDCFIB) ta bayar.
Kwararren jami'in ɗan Jihar Gombe abin alfahari, Dr. Kupan Amos, ya fito ne daga Ƙaramar Hukumar Kaltungo. Ya iso wannan sabon muƙamin ne bayan shafe fiye da shekaru 30 yana aiki da hukumar, wadda ke cike da nagarta, ƙwarewa da jagoranci na ƙwarai.
Gwamna Inuwa Yahaya, ya yabawa Dr. Amos bisa yadda ya yi fice a aikinsa, inda ya bayyana shi a matsayin abin koyi na ƙwarai saboda ƙwazon aiki, wanda salon riƙon muƙaman daya yi ke zama abin burgewa da koyi ga ƴan baya masu zuwa musamman matasa.
Gwamna Inuwa Yahaya yace, "Jihar Gombe na matuƙar alfahari da wannan gagarumin ci gaba na ɗaya daga cikin jiga-jigan 'ya'yanmu, wanda ya nuna ƙwarewa, kishin ƙasa da kuma biyayya wajen yi wa kasarmu hidima.
Ya buƙaci matasa musamman jami’an tsaro su yi koyi da jajircewar da DCG Amos Kupan a wuraren ayyukansu daban-daban.
Gwamnan ya baiwa sabon Mataimakin Koturolan tabbacin goyon bayan gwamnati dana al’ummar Jihar Gombe a kodayaushe.
"Muna taya Dr. Amos Kupan da iyalansa murnar wannar gagarumar nasara, muna yi masa addu'ar ci gaba da samun nasara da riƙe manyan muƙamai a fagen yiwa al'ummarmu hidima."
Ismaila Uba Misilli
Babban Daraktan Yaɗa Labarun Gwamnan Jihar Gombe