02/07/2025
DA DUMI-DUMI: Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Gombe Ta K**a Wani Matashi Da Zargin Mallakar Jabun Daloli A Yamaltu-Deba
Rundunar ‘yan sandan jihar Gombe karkashin jagorancin Kwamishinan ‘Yan Sanda CP Bello Yahaya, psc(+), ta samu nasarar k**a wani mutum bisa zargin hada baki da kuma mallakar kuɗin jabun Dalar Amurka.
Rahoton ya bayyana cewa a ranar Asabar, 28 ga Yuni, 2025, da misalin karfe 10:04 na safe, jami’an ‘yan sanda da ke aiki a sashin tsaro na Filin Jirgin Sama na Lawanti yayin gudanar da ayyukansu na sa-ido, sun k**a wani mutum mai suna Usman Kawu, ɗan shekaru 35, a kauyen Kuji Kwadon, da ke cikin karamar hukumar Yamaltu-Deba, jihar Gombe.
Abubuwan Da Aka Gano
A cewar bayanan ‘yan sanda, an k**a wanda ake zargin da jabun takardun kuɗi na Dalar Amurka guda goma (10), kowanne mai darajar $100, wanda jimillar su ya kai $1,000. Ana zargin ya yi niyyar amfani da kuɗin wajen yaudarar jama’ar gari.
Binciken farko ya bayyana cewa idan an canza jabun kuɗin zuwa kuɗin Najeriya, zai kai kusan ₦1,500,000 (Naira miliyan daya da dubu dari biyar). Haka kuma, an gano wani adadin ₦10,000 a matsayin kuɗin Najeriya a boye cikin gajeren wandonsa na ciki.
Bayanin Wanda Ake Zargi
A lokacin tambayarsa, Usman Kawu ya amsa cewa ya san da kudin jabun, amma ya bayyana cewa wani ne ya bashi domin gudanar da kasuwanci. Sai dai har yanzu rundunar ‘yan sanda na ci gaba da bincike domin gano asalin wanda ya ba shi kudin, tare da bankado duk wata alaka da wasu rukuni ko gungu da ke safarar jabun kuɗi a cikin ƙasa.
Sanarwa Daga Rundunar
Rundunar ‘yan sandan jihar Gombe ta bayyana cewa bincike na ci gaba, kuma za a sanar da al’umma sak**akon binciken a nan gaba.