13/06/2026
Gwamna Inuwa Yahaya ya yi Jimamin Rasuwar Hon Yaya Bauchi Tongo
Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya nuna matuƙar baƙin ciki game da rasuwar dan majalisan tarayya mai wakiltar Mazaɓar Gombe/Kwami/Funakaye a majalisar wakilai, Hon. Yaya Bauchi Tongo, wanda ya rasu ranar Juma'ar nan a Abuja, bayan fama da jinya.
A saƙonsa na ta'aziyya ta cikin wata sanarwa da Babban Daraktan Yaɗa Labarunsa Ismaila Uba Misilli ya fitar, gwamnan ya bayyana marigayin a matsayin ɗan siyasa mai hazaƙa, gogaggen ma'aikacin gwamnati kuma wakili mai himma wanda ya sadaukar da rayuwarsa ga hidimar jama'arsa da kuma ci gaban jihar.
Gwamnan yace rasuwar Hon. Yaya Bauchi Tongo babban rashi ne mai raɗaɗi, ba kawai ga iyalansa ko ƴan mazabarsa ba, har ma ga Jihar Gombe da Najeriya baki ɗaya.
Yace marigayi ɗan majalisan ya shahara ta fannin gudanar da ayyukan raya mazaɓu masu tasiri, da taimakon jin ƙai da kuma jajircewa wajen inganta rayuwar al'ummar da yake wakilta.
Yace “Hon. Yaya Bauchi Tongo shugaba ne mai himma da kuma tushen ci gaba wanda gudunmawarsa ga ci gaban al’umma da ayyukan gwamnati ta sa mutane da yawa suke girmama shi. Hakika rasuwarsa babban rashi ne ga jiharmu da kuma ƙasa baki daya,” in ji Gwamnan.
Gwamna Inuwa Yahaya ya tuna da shekarun da marigayi ɗan majalisan ya shafe yana aiki a fannoni daban-daban, yana mai cewa za a ci gaba da tunawa da dabiunsa na tawali'u, sauƙin kai da kuma jajircewa ga ci gaban al'ummar mazaɓarsa.
Ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan mamacin, da al'ummar mazabar tarayya ta Gombe/Kwami/Funakaye, Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas, da 'yan Majalisar Dokoki ta Kasa, da abokan siyasarsa da dukkan al'ummar jihar Gombe bisa wannan babban rashi.
Gwamnan ya yi addu'ar Allah ya gafartawa marigayin kurakuran da ya yi, ya saka masa da Aljannar Firdaus, sannan ya bai wa iyalansa, da abokan aikinsa da kuma al'ummarsa juriyar wannan babban rashi.