Zakarim INFO.

Zakarim INFO. Aslm Alaikum Yan uwa ina mai marabtanku da ziyarar wannan page din mai Albarka, maraba sosai � ~Da

DA DUMI-DUMI: Gwamnatin jihar Gombe zata dauki sabbin matasa su dubu 2,000 aiki, a karkashin hukumar GOSTEC.Zakariyya Ab...
18/09/2025

DA DUMI-DUMI: Gwamnatin jihar Gombe zata dauki sabbin matasa su dubu 2,000 aiki, a karkashin hukumar GOSTEC.

Zakariyya Abdulkarim

DA DUMI DUMI: ‎A Cikin Wata Sanarwa Da Wani Dan Jam'iyyar NNPP A Majalisar Wakilai Hon Abdulmumin Jibrin Fitar Bayyana C...
04/09/2025

DA DUMI DUMI: ‎A Cikin Wata Sanarwa Da Wani Dan Jam'iyyar NNPP A Majalisar Wakilai Hon Abdulmumin Jibrin Fitar Bayyana Cewa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, Jagoran Jam’iyyar Adawa Ta Kasa A Shirye Yake Ya Koma Jam’iyyar APC Mai Mulki.

Me Zaku Ce?

Kana Son Duba Sahihan Labarai Shigo Jaridar 👉 Zakarim INFO 👈 Yanzu Yi Following Karku Bari Komai Ya Wuceku...

Tinubu ya kawar da matsalar rashin biyan albashi a jihohi 27 — Mohammed IdrisMinistan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya b...
04/09/2025

Tinubu ya kawar da matsalar rashin biyan albashi a jihohi 27 — Mohammed Idris

Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya bayyana cewa sauye-sauyen da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aiwatar sun kawo ƙarshen matsalar biyan albashi a jihohi 27.

Ya yi wannan bayani ne a Abuja yayin da kwamishinonin yaɗa labarai daga jihohi 36 s**a kai masa ziyara.

Idris ya ce manufofin shugaban suna tafiya ne don amfanin ƙasa baki ɗaya, ba siyasa ba, tare da tabbatar da cewa ayyuka suna gudana a dukkan jihohi ba tare da nuna bambanci ba.

Ministan ya ce cire tallafin man fetur ya buɗe sabbin hanyoyin samun kuɗaɗe ga jihohi, wanda ya taimaka musu wajen aiwatar da muhimman ayyuka.

Ya ƙara da cewa kafin Tinubu hauhawa mulki, kaso 97 cikin 100 na kuɗaɗen shiga na tarayya ana amfani da su wajen biyan bashi, abin da ya hana jihohi biyan albashi yadda ya k**ata.

Idris ya yi kira ga gwamnatocin jihohi da su yi aiki tare da shugaban kasa wajen tabbatar da cigaban ƙasa. Haka kuma ya sanar da cewa ma’aikatarsa za ta kai ziyara zuwa wasu jihohi domin duba ayyukan da ake yi da kuma jin ra’ayin jama’a.

Shugaban taron kwamishinonin yaɗa labarai, Usman Tar daga jihar Borno, ya ce sun yi alkawarin inganta haɗin kan ƙasa ba tare da la’akari da jam’iyya ko bambancin siyasa ba.

Follow
Zakarim INFO.
For update

04/09/2025

Mun shiga uku 🥹🥹
Wannan wace irin mummnar kaddara ce 🤔
Duk Wanda Yake son ganin full video yabiyone DM inada shi

3rd September,  2025Clean Energy Drive: Gombe to Host Major CNG Hub as Inuwa Yahaya Seals Deal with Greenville LNGGombe ...
03/09/2025

3rd September, 2025

Clean Energy Drive: Gombe to Host Major CNG Hub as Inuwa Yahaya Seals Deal with Greenville LNG

Gombe State Governor, Muhammadu Inuwa Yahaya, CON, has met with a delegation from Greenville CNG/LNG, led by its Chairman, Mr. Eddy van den Broeke, as part of efforts to fast-track the establishment of a Compressed Natural Gas (CNG) Hub in Gombe State.

The meeting, held at the Gombe State Governor’s Lodge in Abuja, was attended by the Company’s Managing Director, Ritu Sahajwalla and the Chief Executive Officer, Mutiu Sommonu.

They held talks to finalize plans for a major energy infrastructure project designed to deliver cleaner, safer and more cost-effective fuel options for both transportation and industrial purposes in Gombe and beyond.

The planned CNG hub will include Liquefied to Compressed Natural Gas (LCNG) Refill Stations.

Governor Inuwa Yahaya confirmed that the State Government has already allocated land for the project and approved engineering designs.

“We are committed to leveraging natural gas to make transportation more affordable, reduce environmental pollution and stimulate industrial growth in our region.”

Mr. Eddy VdB, noted that
One of the biggest challenges in Northern Nigeria has been the absence of gas pipelines, which limits access to affordable clean energy.

The Greenville-led project, he said, will help bridge this gap through trucking of LNG from the South to Gombe, where it will be regasified and distributed as CNG for various uses.

He praised the leadership and vision of Governor Inuwa Yahaya, noting that the strategic location and enabling policies of Gombe make it ideal for such a regional gas hub.

The CNG hub is expected to significantly reduce the cost of transportation by providing cheaper fuel alternatives for vehicles, including public transport systems.

Plans are already underway to introduce CNG-powered tricycles and other vehicles as part of the State’s evolving transportation master plan.

In addition to public use, CNG conversion centres will be established to help vehicle owners transition from petrol and diesel to natural gas, further boosting energy security and lowering emissions.

According to officials at the meeting, the next phase involves mobilizing equipment and resources to the project site, finalizing technical documentation, and the ground breaking to ensure smooth implementation and adoption.

Recall that a Director from Greenville CNG/LNG, Alhaji Yusuf Zaiyana, was recently in Gombe alongside a technical team to inspect and collect drawings as well as approvals for the four hectares of land allocated to the company by Governor Inuwa Yahaya.

According to him, Greenville plans to invest more than $2 million CNG and LCNG projects with mobilization to site set to commence soon.

Once completed, the CNG hub in Gombe will serve the state, the North-East and parts of the North-West, contributing to job creation, cost reduction and a cleaner environment.

Zakarim INFFO.

DA DUMI-DUMI: Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal yayi rantsuwa cewa ya san inda yan bindiga suke ko da wayar sa zai iya n...
03/09/2025

DA DUMI-DUMI: Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal yayi rantsuwa cewa ya san inda yan bindiga suke ko da wayar sa zai iya nuna su amma kuma babu yadda ya iya da su.

Me za ku ce?

03/09/2025

Hi

DA DUMI DUMI: Duk Masu Gidaje Na Zama Da   S**a Sauya Amfanin Su Zuwa Wuraren Kasuwanci Ba Tare Da Izini Ba Zasu  Biya T...
03/09/2025

DA DUMI DUMI: Duk Masu Gidaje Na Zama Da S**a Sauya Amfanin Su Zuwa Wuraren Kasuwanci Ba Tare Da Izini Ba Zasu Biya Tarar Naira Miliyan Biyar A Abuja

Hukumar Gudanar da Babban Birnin Tarayya (FCTA) ta sanya tara ta Naira miliyan 5 kan duk masu gidaje na zama da s**a sauya zuwa wuraren kasuwanci ba tare da izini ba a wasu manyan tituna na Abuja, ciki har da Titin Gana, Titin Gimbiya, Titin Aminu Kano, da Titin Ademola Adetokunbo.

Wannan matakin ya fito ne daga rahoton kwamitin wucin-gadi da Ministan Abuja Nyesom Wike, ya kafa a ranar 8 ga watan Agusta, 2025 domin tantance matsalolin amfani da Gidaje da kuma canjin dalilin bayar da filaye da ake yi ba bisa ka’ida ba.

Kwamitin, ƙarƙashin jagorancin Daraktan Kula da Ci gaban Birni, Mukhtar Galadima, ya gano cewa mafi yawan gine-ginen da ke kan titunan Gimbiya a Garki, Gana a Maitama da kuma Ademola Adetokunbo a Wuse II an sauya su zuwa otal-otal, ofisoshi da shaguna ba tare da bin ka’idar Hukumar Babban Birnin Tarayya Abuja ba.

Kwamitin ya ba da shawarar cewa a sake ayyana waɗannan gine-ginen zuwa wuraren kasuwanci ta hanyar biyan kuɗaɗen da s**a haɗa da:

-Bakwai da digo biyar na kimar gidajen a matsayin kuɗin canjin sauya amfani.

-Biyan sabbin kuɗaɗen mallakar fili (Statutory Right of Occupancy) bisa sabon nau’in amfani.

-Idan aka gano filin anyi kari ko an haɗe wani wuri da wani wuri ko an raba ba bisa ka’ida ba, za'a biya karin biyu cikin dari na kimar wurin

Kwamitin ya kuma bayyana cewa duk wanda bai bi wannan doka ba za a iya:

-Rufe gine-ginen,

-Rusa gini,

-Ko kuma kwace takardar mallakar fili

Hakazalika, kwamitin ya ba da shawarar cewa a soke tsofaffin takardun mallakar ƙasa sannan a sake fitar da sababbi na shekaru 99 bisa sabon yanayin amfani da ƙasa.

An kuma umarci masu filaye da ba su riga sun gina ba a cikin kwarya birni wato Central Business District da wani yanki da ake kira Phase II Sector Centres su fara gini cikin watanni uku ko kuma su fuskanci kwacewa.

Da yake karɓar rahoton, Mini

Gwamnatin soji ta Burkina Faso ta haramta auren jinsiGwamnatin sojin Burkina Faso a ƙarƙashin jagorancin Faso Ibrahim Tr...
03/09/2025

Gwamnatin soji ta Burkina Faso ta haramta auren jinsi

Gwamnatin sojin Burkina Faso a ƙarƙashin jagorancin Faso Ibrahim Traore ta sanar da haramta auren jinsi a ƙasar baki ɗaya.

Wannan na zuwa ne kimanin shekara guda bayan an amince da wani daftarin dokoki da aka yi garambawul a kan dokokin iyalin ƙasar, inda a ciki aka ƙara auren jinsi.

BBC Hausa ta ruwaito cewa ƙasar da ke yankin Sahel ta kasance a cikin ƙasashen Afirka 22 a cikin 54 da s**a amince da auren jinsi, lamarin da ke ɗaukar hukuncin kisa ko zaman gidan kaso mai tsaro a wasu ƙasashen.

A jiya Litinin ne gwamnatin ƙasar ta amince da sabuwar dokar wadda ta haramta auren na jinsin.

A sabuwar dokar, wanda aka k**a da auren jinsi zai iya fuskantar zaman gidan yari na shekara biyar, k**ar yadda ministan shari'a na ƙasar Edasso Rodrigue Bayala ya sanar a kafar gwamnatin ƙasar ta RTB.

A bara ma dai maƙwabciyar ƙasar, Mali ta yi dokar haramta auren jinsi.

Ko zuwan Rasha Afirka ya inganta tsaro a yankin Sahel?

Gwamnatin Tarayya ta bayyana Juma’a, 5 ga Satumba, 2025 a matsayin ranar hutu don bikin Eid-ul-Maulid na  haihuwar Annab...
03/09/2025

Gwamnatin Tarayya ta bayyana Juma’a, 5 ga Satumba, 2025 a matsayin ranar hutu don bikin Eid-ul-Maulid na haihuwar Annabi Muhammad (SAW)
Wata sanarwa daga babban Sakatare D na Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, Dr Magdalene Ajani, ta fitar a madadin Minista, ta taya musulmi a Najeriya da ma duniya baki ɗaya murnar wannan lokaci, tana mai kira da a yi Koyi da ɗabi’un Annabi wajen zaman lafiya, ƙauna, tawali’u, haƙuri da jin ƙai.
Sanarwar ta kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su yi amfani da wannan dama wajen addu’a domin samun zaman lafiya, tsaro da kwanciyar hankali a ƙasar, tare da goyon bayan ƙoƙarin gwamnati na haɗin kai da cigaba.
Ministan Harkokin Cikin Gida yana yi wa musulmi fatan biki mai cike da farin ciki da zaman lafiya na Eid-ul-Maulid.

Matsalar tsaro: Dole ma mu kirkiri ƴansandan jihohi - Tinubu Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce kafa rundunar ’yan sa...
03/09/2025

Matsalar tsaro: Dole ma mu kirkiri ƴansandan jihohi - Tinubu

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce kafa rundunar ’yan sandan jihohi ya zama dole, domin magance matsalar tsaro da ke damun ƙasar.

Tinubu ya bayyana haka ne a Abuja lokacin da ya karɓi tawagar manyan ’yan asalin Katsina ƙarƙashin jagorancin gwamna Dikko Radda.

Ya umarci hukumomin tsaro da su sake duba dabarun aikin su a Katsina, tare da tabbatar da rahoton yau da kullum, sannan ya sanar da amincewar gwamnati kan ƙarin sayen jiragen leƙen asiri (drones).

Shugaban ƙasar ya kuma bayyana cewa za a tura kayan aikin soja na zamani da na’urorin sa ido a jihar, tare da duba yiwuwar ƙarfafa mafarauta da aka tura.

Tinubu ya jaddada cewa matsalar tsaro ba za ta gagari gwamnati ba, yana mai cewa: “Za mu kafa ’yan sandan jihohi, za mu magance rashin tsaro, dole mu kare ’ya’yanmu, mutanenmu, da wuraren ibadarmu.”

Ya kuma tabbatar da ci gaba da kiyaye amanar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, yana mai cewa Buhari ya bar wa Najeriya tarihin nasara.

A nasa jawabin, gwamna Radda ya gode wa shugaban ƙasa kan goyon bayansa ga jihar, yayin da tsohon gwamna Aminu Masari da Wazirin Katsina, Ibrahim Ida, s**a yaba da ayyukan ci gaba da Tinubu ke aiwatarwa a jihar, tare da neman ƙarin kulawa musamman a fannin tsaro da filin jirgin sama na Katsina.

28/12/2024

Address

Cheheniya Police Barrack Gombe
Gombe
760001

Telephone

+2347068578729

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Zakarim INFO. posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Zakarim INFO.:

Share