05/06/2026
Dan takarar dan majalisa a jihar Gombe Hon Mubarak Musa Dantori, tare da dubunnan magoya bayansa, sun fice daga jam'iyyar ADC zuwa jam'iyyar PDP domin marawa Professor Isa Ali Pantami baya a zaben 2027.
A yau Jumma'a daya daga cikin shahararrun matasa 'yan siyasa masu taimakon al'umma a jihar Gombe Hon Mubarak Musa Dantori kuma dan takarar dan majalisar jiha na Gombe ta kudu karkashin jam’iyyar ADC ya sanar da ficewarshi tare da dubunnan magoya bayansa daga jam'iyyar ADC zuwa jam'iyyar PDP.
Hon Mubarak Musa Dantori yace sun fice daga jam'iyyar ADC ne zuwa jam'iyyar PDP domin marawa tafiyar Pantamiyya baya karkashin jagorancin Professor Isa Ali Pantami domin samar da ingantaccen shugabanci a jihar Gombe.
Hon. Dantori ya bayyana cewa ayyukan Alkhairan da Professor Isa Ali Pantami ya shimfida a jihar Gombe da samawa daruruwan matasa ayyukan yi a jihar Gombe yana daga cikin abubuwan da s**a ja hankalinshi na shiga tafiyar Pantamiyya domin shima ya bada tashi gudummawa na ciyar da al'ummar jihar Gombe gaba.