Bizstar Hausa

Call Directions Contact the business

Bizstar Hausa Labaran gida Dana ketare

20/08/2026

Da Dumi-Duminsa: Jirgin Kasar Rasha Na-35S Ya Harbo Wani Jirgin Yáƙin MiG-29 Na Kasar Ukraainé

19/08/2026

Da Dumi-Duminsa:Saudiyya Ta Yi Allah-wadai da Hárîn Da Israa’ilaa Takai a kasar Siriya

19/08/2026

YANZU-YANZU: Kasar Isarela Ta Haramta Siyarwar Kasar Qatar Mákámáî Da Kayan Sojî

19/08/2026

WATA SABUWA:Matatun Mai na Amúrka Na Kwasar Fiye da Rabin Man Fetur ɗin Da Venezuela Take Samarwa

19/08/2026

Yakin da cin hanci a Mulkin Tunubu

19/08/2026

Irán Ce ta samu nasara a karfin sôjin da Siyasa kan Amûrká da Îsrá'ila - Ghalibâff

18/08/2026

Nigeria na Shirin dawo da Yan kasan zuwa gida daga Africa ta Kudu

18/08/2026

Cigaban Tattalin Arziki a zamanin Tunubu

Sakataren Yaɗa Labaran ADC a karamar Hukumar Kwami Ukasha Bolawa ya fice daga jam’iyyar zuwa APC Ukasha Ibrahim Bolawa, ...
18/08/2026

Sakataren Yaɗa Labaran ADC a karamar Hukumar Kwami Ukasha Bolawa ya fice daga jam’iyyar zuwa APC

Ukasha Ibrahim Bolawa, wanda ya kasance Sakataren Yaɗa Labarai na jam’iyyar African Democratic Congress, ADC, a ƙaramar hukumar Kwami ta jihar Gombe, ya yi murabus daga mukaminsa tare da ficewa daga jam’iyyar.

A cikin wata wasikar murabus da ya sanya wa hannu a ranar 18 ga Agusta 2026, Ukasha ya ce ya kuma ajiye shugabancin tawagar yaɗa labarai ta kafafen sada zumunta ta ADC a jihar Gombe.

Ya ce matakin ya biyo bayan dogon nazari da shawarwari da ya yi, inda ya yanke shawarar bin wata sabuwar hanyar siyasa da ta fi dacewa da akidunsa da burinsa na siyasa.

Ukasha Ibrahim Bolawa ya bayyana cewa zai bi sahun jagoransa na siyasa kuma shugabansa, Injiniya Aliyu Mohammed Kombat, wajen komawa jam’iyyar All Progressives Congress, APC.

Ya jaddada cewa matakin nasa zaɓin siyasa ne na kansa, ba tare da wata niyyar raina ko zubar da mutuncin ADC, shugabanninta ko mambobinta ba.

Ya kuma gode wa shugabannin ADC bisa damar da s**a ba shi ta yi wa jam’iyyar hidima, tare da bayyana cewa ya samu kyawawan alaƙa da abokantaka a lokacin da ya kasance ɗan jam’iyyar.

Ukasha ya nemi shugabannin ADC su amince da murabus ɗinsa da ficewarsa daga jam’iyyar, tare da yi wa jam’iyyar da mambobinta fatan zaman lafiya da ci gaba.

“Mun zaɓi inda za a tarbe mu,” in ji wani saƙon da aka wallafa tare da sanarwar, yayin da ake bayyana komawarsa APC.

17/08/2026

Akwai Yi wuwar sake tsanatar rikicin Yankin Gâbás Ta Tsákiyá - Irán

Address

Gombe

Telephone

+2348034059379

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Bizstar Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Bizstar Hausa:

Shortcuts

Share