06/03/2025
AYI MANA UZURI.
Akwai dayawa dake ganin kamar muna tsanantawa, wasu ma har shagube suke mana kamar biyanmu ake yi, to wallahi abin duk ba haka bane, a yadda muke jinsa zuciyarmu, wallahi idan farashi aka sanya karatunsa sai an biya kudi za'a saurara, to kuwa zamu bude asusune na adashe da zamu tara abinda zamu biya domin mu saurara, domin wallahi kimar abinda ke fitowa bakinsa bai da farashi abin kimantawa a wajenmu.
MALLAM KANA SAURARON KARATU KANA JIN KAMSHI DA DANDANON ILHAMA NA SAUKA, ANA MAKA KARATU KANA GANIN IKHLASI NA NASO, ANA KARATU ZAKAJI RUWAN FAHIMTA NA ZUBA.
Muna son duka Malamai muna girmama kowa, fatanmu kowannenmu ya zamo wakili da zai jibanci aikin hidimar yada karatukan Malamin da ya kwanta masa a zuciya ba tare da kyarar waninsa ba.
ALLAH A BARMU DA KAUNAR MASU KAUNAR BAYIN ALLAH DA GASKE..
ALHAMDULILLAH.