14/05/2019
Sarki Sanusi Lamido Sanusi
Muhimmiyar Shawara Ga shugaba
Buhari Domin Ceto Kasarmu Nijeriya.
*Ya Kamata Canji Ya Soma Daga
Majalisa
* Sanata na karbar Naira Miliyan
36,000,000 kowane wata*.
Idan aka raba gida biyu yana karbar
Naira Miliyan 18,000,000, ragowar
*Naira Miliyan 18,000,000 za a iya
amfani da su wajen daukar 'yan
Nijeriya 200 aiki kowa ya rika daukar
albashin Naira Dubu 90,000 kowane
wata.*
Idan aka yi mutum 200 sau adadin
Sanatocin mu 109 hakan na nufin za
a dauki 'yan Nijeriya *dubu 21800
aiki *.
A takaice 'yan Nijeriya 200 za su iya
rayuwa a wadace da rabin albashin
Sanata na kowane wata.
*Dan Majalisar Wakilai na karbar
albashin Naira Miliyan 25,000,000
kowane wata.*
Idan aka raba albashin gida biyu ya
zama Naira Miliyan 12.5million a
wata. Ragowar *Naira Miliyan 12.5
za ta isa a dauki 'yan Nijeriya 135
aiki su rika daukar albashin Naira
dubu 92,500 a wata*.
'Yan Nijeriya 135 sau adadin yawan
'yan Majalisar Wakilai 360, hakan na
nufin za a dauki 'yan Nijeriya *dubu
48600 aiki*.
'Yan Nijeriya 135 za su rayu a
wadace da rabin albashin dan
Majalisar Wakilai.
*Don haka Baba Buhari gwamnatin ka za ta iya daukar 'yan Nijeriya dubu
70,400 aiki da za a rika ba su
albashin Naira dubu 90,000 wasu
kuma Naira dubu 92,500. Kuma cikin
ruwan sanyi ta hanyar RABA
ALBASHIN Sanatoci da 'yan
Majalisar Wakilai!!*
Ka gwada yin wannan lissafin ya mai
girma Shugaban Kasa....
Yanzu aikin kowane dan Nijeriya ne
ya yada wannan sako domin
Sanatoci da 'yan Majalisar Wakilai su
san a dalilin albashin da suke dauka
mutane nawa ne ba su da aiki a
Nijeriya..
*Ya kamata SAUYI ya fara daga
MAJALISA!*
A taimaka wajen yada sakon nan!!
*ALLAH YA TAIMAKI NIJERIYA*