30/09/2025
Arsenal za ta ƙulla sabuwar yarjejeniya da Saka, Barcelona na jan ƙafa kan tsawaita zaman Rashford, manyan Kungiyoyin premier league na son daukar Semenyo, Newcastle na son rike Kieran Trippier, zai wahala Liverpool ta dau Upamecano, kungiyoyin premier league na son daukar Rayan, Spurs na son daukar Arda Guler, kungiyoyin championship na rububin daukar Watson
Arsenal na tattaunawa da ɗan wasan gefe Bukayo Saka, mai shekara 24, game da sabon kwantaragi wanda zai sanya shi zama ɗaya daga cikin ƴan wasan da ke karɓar albashi mafi tsoka a ƙungiyar. (Express)
Barcelona ta na nazari kan yanke shawarar gabatarwa ɗan wasan gaban Manchester United Marcus Rashford, mai shekara 27, kwantiragin zaman dindindin.
Ɗan wasan gaban Bournemouth Antoine Semenyo na ci gaba da jan hankalin wasu ƙungiyoyin premier League duk da cewa ya sanya hannu kan sabon kwantaragi a bazara. Tottenham da Manchester United, da Manchester City da Aston Villa duk sun nuna sha'awarsu kan ɗan wasan mai shekara 25. (TBRFootball)
Newcastle na son bai wa tsohon ɗan wasan bayan Ingila Kieran Trippier sabon kwantiragi. Kwantiragin ɗan wasan mai shekara 35 na yanzu zai ƙare ne a ƙarshen kakar wasa ta bana. (Chronicle)
Liverpool na iya fuskantar cikas a yunƙurin da ta ke yi na ɗaukar ɗan wasan Bayern Munich Dayot Upamecano, mai shekara 26, a watan Janairu yayin da kulob ɗin na Bundesliga ke son ƙulla sabuwar yarjejeniya da ɗan wasan na Faransa. (Insider football)
Tottenham da Chelsea da Brighton na cikin jerin ƙungiyoyin da ke zawarcin ɗan wasan gaban Brazil Rayan, mai shekara 19, wanda ke taka leda a Vasco da Gama. (Sport Witness)
Haka kuma Spurs ɗin na son ɗauko Arda Guler daga Real Madrid. Ɗan wasan na ƙasar Turkiyya mai shekara 20 na fuskantar ƙalubale wurin samun gurbi a tawagar Madrid ta farko, kuma Newcastle da Arsenal na nuna sha'awarsu kan ɗan wasan. (Fichajes)
Ƙungiyoyin gasar championship ta Ingila, Preston da Derby da Hull suna sha'awar ɗaukar ɗan wasan Brighton ɗan ƙasar Ingila Tom Watson, mai shekara 19, a matsayin aro a watan Janairu. (Lancashire Post)
Wanna gyara ya kamata kungiyar ku ta yi?