08/08/2026
Gwamnatin jihar Gombe za ta kashe Naira miliyan 998.3 domin sayen katifu da matasan kai guda 22,000 ga makarantun sakandaren kwana na gwamnati da ke faɗin jihar.
Matakin na daga cikin shirin gwamnatin jihar na gyara harkokin ilimi da inganta walwalar ɗalibai, tare da ƙara ingancin karatu, kamar yadda Jaridar Aminiya ta ruwaito.
Kwamishiniyar Ilimi ta jihar, Aishatu Umar Maigari, ta bayyana cewa kwangilar ta haɗa da saye, jigilar kaya, lodawa da kuma rarraba katifu da matasan kai ga makarantun sakandaren kwana 20 da ke faɗin jihar.
Ta ƙara da cewa majalisar zartarwar jihar ta kuma amince da ƙaddamar da shirin Gombe Basic Education and Skills Transformation (GoBEST), wanda aka tsara domin sauya fasalin ilimin bai ɗaya ta hanyar haɗa koyar da sana’o’i da ƙwarewar fasaha cikin tsarin karatu.
Kwamishiniyar ta bayyana hakan ne bayan kammala zaman majalisar zartarwa karo na 55 da aka gudanar ranar Juma’a.
A cewarta, an yanke shawarar ne bayan gudanar da cikakken bincike kan buƙatun makarantun, inda aka gano ƙarancin kayan kwanciya a matsayin ɗaya daga cikin manyan matsalolin da ɗaliban makarantun kwana ke fuskanta.
Maigari ta ce shirin zai taimaka wajen inganta walwalar ɗalibai, tare da shirya makarantun kwana, ciki har da sabbin manyan makarantun da aka kafa, domin karɓar ƙarin ɗalibai.
Ta ce ana sa ran sabbin manyan makarantun, waɗanda aka fi sani da Mega Schools, za su ɗauki kusan ɗalibai 15,000.
Kwamishiniyar ta kuma bayyana cewa majalisar ta amince da rahoton Kwamitin Gyara da Farfaɗo da Ilimin Bai Ɗaya da na Fasaha na Jihar Gombe, wanda Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya ƙaddamar a ranar 17 ga Nuwamban 2025.
Ta ce an ɗora wa kwamitin alhakin tantance halin da ilimin bai ɗaya da na fasaha ke ciki, tare da bayar da shawarwari masu amfani domin inganta ingancin ilimi da sakamakon karatu.
A cewarta, ɗaya daga cikin muhimman shawarwarin kwamitin shi ne kafa shirin GoBEST, wanda zai zama babban tsarin gwamnatin jihar na sauya fasalin ilimin bai ɗaya.
Ta ce za a aiwatar da shirin tare da yin garambawul ga hukumomin da ke ƙarƙashin Ma’aikatar Ilimi, domin inganta gudanar da ayyuka da samar da ingantattun ayyukan ilimi.
Maigari ta ce shirin GoBEST zai ƙarfafa tsarin ilimin bai ɗaya na shekaru 12 a jihar, ta hanyar haɗa koyar da sana’o’i da ƙwarewar fasaha cikin manhajar karatu.
Ta ƙara da cewa shirin zai kuma ginu ne kan nasarorin da aka samu ta hanyar shirin AGILE, wanda ke da nufin inganta ilimin ‘yan mata da kuma ƙarfafa damar samun ilimi.
Kwamishiniyar ta ce gwamnatin jihar na sa ran fara ganin gagarumin tasirin shirin cikin kwanaki 100 na farko da fara aiwatar da shi.