ARC-P Programs, Gombe State

ARC-P Programs, Gombe State Shiri Ne Dake Farfado Da Rayuwar Wadanda Ke Cikin Garari, Musamman Yara Da Basa Zuwa Makaranta

KUNGIYAR MASU SAYAR DA SHAYI DA INDOMIE NA JIHAR GOMBE SUN NUNA GAMSUWA DA AYYUKAN OFISHIN GINA AL'UMMA DA BUNKASA SUA r...
05/12/2022

KUNGIYAR MASU SAYAR DA SHAYI DA INDOMIE NA JIHAR GOMBE SUN NUNA GAMSUWA DA AYYUKAN OFISHIN GINA AL'UMMA DA BUNKASA SU

A ranar Litinin din nan 5 ga watan Disamba, 2022 kungiyar masu saida shayi da Indomie na jihar Gombe s**a ziyarci ofishin gina al'umma da bunkasa su, domin jaddada goyon baya ga ayyukan Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya.

Shugaban Kungiyar masu sayar da Shayi na jiha Shu'aibu Musa Ibrahim yace la'akari da yadda ofishin ke tafiyar da ayyukan sa da gamsuwa dasu tare da maraba baya a nan gaba don dorewar ayyukan, shine makasudin ziyarar.

Malam Shu'aibu Musa yace sun shaida wasu alkawura da Gwamna Inuwa Yahaya yayi wa kungiyar masu sayar da Shayi da Indomie na jihar Gombe, don haka suna bayan sa dari bisa dari.

Da yake mayar da martani, Babban mai taimakawa Gwamna ta fannin gina Al'umma da bunkasa su Barista Sani Ahmadu Haruna, ya ce sun daura dukkanin kungiyar bisa gaskiya ta yadda zasu ci moriyar shirye-shiryen ofishin.

Barista Sani Haruna yace yanzu haka sun karbi sunayen mambobin kungiyar guda dari 5 domin sanya su cikin shirin fadada ayyukan gina al'umma a fadin jihar Gombe nan bada jimawa ba, ganin yadda sana'ar sayar da Shayi da Indomie ke samar da ayyukan yi ga dimbin jama'a.

Kungiyar ta kuma karrama Barista Sani Haruna da lambar yabo bisa jajircewar aiki, inda tayi masa fatan tarin nasarori cikin ayyukan sa.

Mohammed Babawuro
Media Assistant to the SA on Human Capital Development.

SHIRIN KOYARWA NA ARC-P YA CIMMA GAGARUMAR NASARAA ranar Asabar din nan 5 ga watan Nuwanba, 2022 Shirin ARC-P ya ziyarci...
06/11/2022

SHIRIN KOYARWA NA ARC-P YA CIMMA GAGARUMAR NASARA

A ranar Asabar din nan 5 ga watan Nuwanba, 2022 Shirin ARC-P ya ziyarci wasu cibiyoyin tsangayu na karatun Alqur'ani a cikin garin Gombe, don duba matakin nasara da ake samu daga matasan Youth Facilitators dake koyar da almajirai ilmin boko baya ga karatun Allo da suke.

Shirin ARC-P karkashin matasan, na koyar da sana'o'i daban-daban ga almajiran baya ga ilmin boko, kamar su hada mawuka da kayan abinci yin jaka da takalma, kiwon kaji, kifi da dabbobin gida da dai sauransu.

Malam Yusha'u Dan Aljanna, mai tsangayar Tarbiyyatul Fai'da dake Unguwar Pizet, zawiyar Sheik Abubakar Daniya, ya nuna matukar farin ciki da godiya ga Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya da jagoran shirin ARC-P Barista Ahmadu Sani Haruna bisa taimakawa almajirai da karantarwar zamani.

Malam Yusha'u yace sakamakon shirin koyarwa na ARC-P almajiran sa sun koyi abubuwa da dama wadda ya kai ga koda bata s**ayi suna rubuta ko bayyana inda suke, sai ya bukaci karin wajan karatu koda ma gina musu rumfa ne.

Tawagar ta zarce tsangayar Farhil Islam ta Malam Sirajo Kagarawal, inda nan ma aka shaida dinbin nasara da ci gaba da harkar koyarwar zamani da shirin ARC-P ya kawo, da sauran tsangayu a unguwannin kumbiya-kumbiya, Nasarawo da sauran su.

Wasu daga cikin daliban da muka ziyarta Ibrahim Abdullahi da Khadija Dahiru Aliyu sun bayyaya jin dadinsu bisa wannna shirin ARC-P na koyar da ilmin boko da sana'o'i, wadda s**a bayyana a matsayin "ribar kafa'' wadda suke mora bayan karatun Muhammadiyya.

Mohammed Babawuro
Media Assistant to the SA, Human Capital Development.

ANA CI GABA DA TANTANCE YOUTH FACILITATORS NA SHIRIN ARC-P A JIHAR GOMBE. A ci gaba da tantance matasan dake koyarwa kar...
03/11/2022

ANA CI GABA DA TANTANCE YOUTH FACILITATORS NA SHIRIN ARC-P A JIHAR GOMBE.

A ci gaba da tantance matasan dake koyarwa karkashin shirin ARC-P na jihar Gombe, a yau Alhamis 3 ga watan Nuwanba, 2022 tawagar Jami'an ma'aikatan ARC-P sun ziyarci kananan hukumomin Funakaye, Nafada, Kwami da Dukku.

Da yake bayyaya manufar tantancewar, Ko-odinatan shirin ARC-P dake farfado da rayuwar wadanda ke cikin garari, Barista Sani Ahmadu Haruna yace "tsawon shekara kenan da kaddamar da matasa 500 bayan basu horo, sannan s**a shiga cikin al'ummomin su domin zakulo yara dake cikin garari.

" Mun kuma tabbatar kowa daga cikin matasan na kawo mana Bayani ayyukan da muka sanya su duk wata, don haka muka fara tantance su a yanzu domin tabbatar da ainihin wadanda ke aikin yadda ya Kamata"

Barista Sani Haruna ya kuma bada tabbacin ci gaba da gudanar da shirin ta bangarori da dama karkashin tallafawar Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, don inganta walwalar al'ummar jihar Gombe baki daya.

Kadan daga cikin matasan 'Youth Facilitators' Nu'uman Muhammad Bello daga Akko da Isiyaku Sa'adu Lafiya daga Dukku sun bayyaya farin cikinsu bisa yadda shirin ke tafiya, tare da godewa Gwamna Inuwa Yahaya da ya kawo wannna shiri dake agazawa matasan da s**a kammala karatu babu aikin yi.

Sun kuma jinjinawa jagoran shirin na ARC-P a jihar Gombe Barista Sani Haruna kan yadda yake jajircewa da yin tsayin daka wajen ganin an samu nasarar shirye-shiryen ARC-P karkdhin ofishin sa dake taimakawa Gwamna ta fannin gina Al'ummar jihar Gombe ba tare da nuna banbancin addini, yare, yanki ko kabila ba.

Tawagar ta kuma ziyarci cibiyar koyarwa ta Almajirai dake Cikin garin Bajoga inda ta duba yadda dalibai ke samun karatun zamani bayan na Islamiya.

Mohammed Babawuro
Media Assistant, SA Human Capital Development

03/11/2022
SHIRIN ARC-P YA FARA TANTANCE MATASAN DA KE KOYARWA KARKARSHIN SHIRIN...Tun bayan kaddamar da matasa 500 a fadin jihar G...
03/11/2022

SHIRIN ARC-P YA FARA TANTANCE MATASAN DA KE KOYARWA KARKARSHIN SHIRIN...

Tun bayan kaddamar da matasa 500 a fadin jihar Gombe da Gwamna Inuwa Yahaya yayi karkashin shirin farfado da rayuwar wadanda ke cikin garari musamman kananan yara, wato ARC-P, shirin karkashin jagorancin mai taimakawa Gwamna ta fannin gina Al'umma Barista Sani Haruna, ya ke bibiyar matasan da yadda suke gudanar da aikin da aka daura musu.

A ranar Larabar nan ne, shirin ARC-P ya fara aikin sabonta matasan wadanda yawancin su ke aikin koyarwa bayan zakulo yaran dake cikin matsin rayuwa, da nufin tantance ainihin wadanda ke aikin da kuma sabonta su.

Aikin tantancewar ya fara ne da kananan hukumomin Akko, Yamaltu Deba, Billiri, Kaltungo, Shongom da Balanga, inda matasan ke bayyana farin cikin su bisa yadda aikin koyarwar ta tallafin rayuwar su da yaran dake kewaye dasu.

Mohammed Babawuro
Media Assistant, SA Human Capital Development

02/04/2017

Tafiyar Ajali.
Ukubar Mata.
Tafanjama fanjam 2.
Alkalin masoya.
dadai sauransu, sunanan akasuwa ku nema kusheke kwarkwatar idanunku

28/11/2016

Da fim din Tsananin So da Hamagawa wanne yafi burgeka kuma ina ne yafi burgeka ?

18/10/2016

Fina-finan da s**a antawo muku.
Garuje.
Jami'in tsaro.
Zakin mata.
Gaskia daya.
Fuska biu.
Rikon amana.

17/07/2016

Wadannan sune fina-finan da s**a fita a yan watannin da s**a shude:
Komai tafanjama famjam.
Sangami.
Jamurin kasa.
Gosulo.
Mai lasisi.
Farcen gumurzu.

24/03/2016

Fim din Zaki ko Damisa da kuma Malin fita ta 3 wadda bai kalla ba ya hanzarta ya nema.

Address

Off Goodluck Jonathan Road, Buba Shongo Gombe Metropolitan
Gombe

Telephone

+2349020440889

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when ARC-P Programs, Gombe State posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share