Ishaq Digital Hub

Ishaq Digital Hub Web3 Advocate ll Web3 Content Writer ll Airdrop Hunter ll Graphic Design ll Digital Marketer ll DEX Trader

Solving People Problems Through Digital Skills

Trump na shan caccaka bayan wallafa hoton kansa a matsayin Fafaroma ta hanyar AI" Channels TVKarin bayani:https://shortu...
04/05/2025

Trump na shan caccaka bayan wallafa hoton kansa a matsayin Fafaroma ta hanyar AI" Channels TV

Karin bayani:
https://shorturl.at/Mvgal
Ishaq Digital Hub

Allahu Akbar.. ina kyautata zaton wannan hoton an dauke shi ne a wajen rufe Daura kimanin shekaru 24/25 a garin Bauchi, ...
29/04/2025

Allahu Akbar.. ina kyautata zaton wannan hoton an dauke shi ne a wajen rufe Daura kimanin shekaru 24/25 a garin Bauchi, a ranar malam shine tafinta tsakanin mutane da su Sheikh Zarban, a karshen taro aka bukaci malam ya karanta Alqur’ani... Allah ya masa rahama.

Copy




Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

INNALILLAHI WAINNA ILLAIHIRRAJIUUN!!!😳A Jiya na dawo gida a gajiye. Sai na gayama matata cewa zan canza tufafina sannan ...
24/04/2025

INNALILLAHI WAINNA ILLAIHIRRAJIUUN!!!😳

A Jiya na dawo gida a gajiye. Sai na gayama matata cewa zan canza tufafina sannan in d'an kwanta in huta ka'fin ta gama abinci.

Haka naje na canza kayana sannan na kwanta a kan gado na rufe ida'nuna.

Ban bud'e ida'nuwana ba har saida aka kira sallar la'asar.

Sai na tashi na fito daga d'aki na doshi inda matata take dafa abinci

na qarisawa gurin sai naga matata sai jera abinci takeyi akan teburi.

Sai na zauna akan tebur
sannan na tambayeta me kika dafamana ne. Rabin zuciyata. Naga tayi shuru.

sannan na qara tambayarta me kika dafamana ne. Rabin zuciyata.

Amma sai tayi shiru ba tace mini komai ba.

Sai na qara tambayarta a karo na 3 da karo na 4

amma sai naga tayi shiru batace komai ba.

Rayuwa A Musulinci.

Sai raina ya 6a'ci. Amma sai na tina cewa yau shekararmu ashirin muna rayuwa a tare. Amma ban ta6a kiranta taqi amsawa ba.

Sai na waiwaya inda d'ana yake zaune sai nace masa yaje firij ya kawo mini ruwa a kofi.

Amma sai naga shima yayi shiru ya qya'leni. Sai abin ya bani ma'maki. Sai na tashi da niyyar fita daga d'akin girkin.‎

Kawai sai naji matata ta gayama d'ana cewa yaje d'aki ya taso babansa daga bacci. Sai naji hankalina ya tashi.

Haka d'ana yaje d'akina don ya tasheni daga bacci. Sai na d'aga muryata nace masa ga'ni anan. Amma ko waiwayowa baiyiba. Haka ya doshi d'akina a guje don ya tasoHaka d'ana yaje d'akina don ya tasoni.

Bayan k**ar minti 1 sai ya dawo a firgice. Sai babarsa ta tambayeshi
shin ka tasoshi ne?

Sai yace: na'yi_na'yi amma yaqi tashi..

Sai matata ta tafi d'akina da sauri d'ana yabita a baya. Sai na bisu don inga yadda zasu tasoni daga bacci.

Sai naga sunata qoqarin tashin wani mutum mai k**a dani da yake kwance akan gadona. Kuma mutumin ya sanya tufafina. Da taga ta kasa tashinsa daga bacci. Kawai sai hawa'ye ya riqa fitowa daga idonta.

Sai naga ita da y'ay'ana sunata kuka. Sai naga abin k**ar a mafarki.

Yaah Ila'hee, wai me yake faruwa ne? Waye wancan mutumin mai k**a dani.? Me yasa inayi magana basa'ji? Me yasa basa ganina. Sai d'ana ya fita da sauri. Can sai naga ya dawo. shi da babana da babata da wasu y'an uwana. Dukkanninsu sunata kuka.
Babata ta riqa rungume wannan mutumin mai k**annina. Sai naje wajenta na riqa qoqarin ta6ata da yimata magana. Amma abu ya faskara. Sai na juya wajen babana da y'an uwana amma sai naga basa jin muryata.
Sai naji y'an uwana suna maganar ayi mini jana'iza.
Sai mai yin wankan ga'wa. yazo ya riqa wanke wannan mutumin mai k**a dani da yake kwance a d'aki na. Y'ay'ana s**a taimaka masa aka wanke mutumin aka sanya masa likkafani aka d'aurashi akan makarah.
Abokaina da masoyana s**a cika gidanmu suna yima babana da yan uwana gaisuwar makoki.
Sannan s**a d'auki makarar s**a kaita Masalla'ci. Kowa ya fita daga gidan mata kawai aka bari. Sai nayi sauri na fita na nufi masallaci na iske maqwabtana da abokaina sunyi sahu a bayan liman.
Haka na riqa ra'tsa dandazon masu sallah ba tareda na ta6a kowa ba.
Lima'mi yayi Kabbara ta 1. Ni kuma ina tayi musu ihu. Inacewa wai wa kuke salla'ta?
Ga'ninan a atare daku. Ba kwa'gani ne!!!
Magana nake muku ko ba kwa'jina ne?
Alokacin da na fitar da rai cewa zasu kula'ni. Sai na qya'lesu s**a riqa sallarsu. Ni kuma na nufi inda makara take. Na cike likkafanin don inga fuskarsa. Kawai sai naga ya bud'e ida'nunsa
yace mini: ni na gama aikina. Kai kuma har abada kaine zaka riqa yin komai da kanka.
Rayuwa A Musulinci.
Domin adah atare mukeyin komai har tsawon shekaru 40. Amma yanzu ni qasah zan zama. Kai kuma hisabi za'a maka.
Ban ankara ba. Sai jina nayi akan makara. Kuma ga66aina sun kaasa motsi. Banda qarfin yin motsi.
Haka s**a binneni. Sukai tafiyarsu. Tun inajin motsin ta'kalmansu har na daina.
Rayuwa A Musulinci.
A wannan lokacin ne na fahimci cewa qarshena yazo.
Sai na fara tinanin yadda mutuwa tazo mini bagatatan. Alha'lin ayyuka sunyi mini yawa kuma akwai alqawarur_rukan da ban cika ba.
Kuma akwai way'anda suke bina bashi kuma ban rubuta ba. Ban gayama kowa ba. Banyi wasiya ba.
To yaya zanyi ? Ga'shi inaso inyi umarni da kyaky_kyawa kuma inyi hani da mummuna.
Ina cikin wannan tinanin ne naji ala'mar ana tafiya an doso inda nake.
Babu makawa Munkaran da Nakiyr ne s**a taho inda nake.
Sai na fara ihu ina cewa: Ya Allah a mayar dani duniya.
A mayar dani duniya.
A mayar dani duniya.
A mayar dani. Domin in aikata aikin alheri.
Rayuwa A Musulinci.
Haka nata fadi' har muryata ta disa'ashe. Amma aduk lokacin da nace a mayar dani. Sai inji wata murya tana cewa inah. Inah. Ai lokaci yazo qarshe.
Sai naji wata murya a kusa da kunnena ana cemini baba baba baba.
Ina bud'e ido sai naga ashe wata y'atace take ta'shina daga bacci.
Nanfa nayi ajiyar zuciya nayi murmushi. Na godema Allah s.w.t.
Sai na zauna akan katifa gumi nata fitowa daga jikina. zuciya tana bugawa da qarfi.
Nanfa na fara tinanin ayyukan alherin da ya k**ata in fara aikatawa.
Don haka y'an uwa kuyi saurin aikata aikin alheri domin rai batasan abinda zai faru a gareta ba gobe. Kuma batasan a inda zata mutu ba.
Allah yasa mudace amin.

Ishaq Digital Hub

24/04/2025

Mafi girman nasara shine ka taimaki wani yayi nasara a rayuwa.

AbumukhtarZero ✍️

BARKAN MU DA SAFIYA 📍
20/04/2025

BARKAN MU DA SAFIYA 📍

13/04/2025

Barkan mu da wannan lokacin

04/04/2025

Nayi posting ɗin hoton DR bisa rashin sanin cewa: "Ya bayar da wasiyar kada a yaɗa hotonsa a media bayan rasuwarsa, hakan yasa na goge posting ɗin nan take bayan sanin hakan", muna masu addu'ar (Allah ya jikan malam, ya yimai rahamah).

Idan tamu tazo, Allah yasa mu cika da imani.

03/04/2025

Jira kakeyi sai kayi kuɗi tukunna kayi Aure ? Yaushe zakayi kuɗin ? Meye tabbacin zakayi kuɗin kafin Auren?

Indai kanada Sana'a wacce zaka iya riƙe kanka da Abokiyar zamanka (mata) Abokina kawai kayi ƙundunbala kayi Aure, wasu lokutan kuɗaɗen da ƙattin banzan nan marasa Aure suke kashewa masu auren basa kashewa a gidajen su, ga tarin lada, ga kuma buɗi da Allah yakeyi musu falalar Aure, Sau tari idan zaka hanga ka gani, Irin manyan kuɗaɗen nan sunfi zuwa bayan Aure kuma sunfi daɗin kashewa idan da Auren.

Allah ka Horewa masu niyyar Aure, ka basu abunda zasu riƙe auren dashi.

Ishaq Digital Hub

MABIYA ADDININ KIRISTANCI NA DUNIYA NA  FUSKANTAR BARAZANA Hankalin Fafaroma Ya Tashi Sak**akon Gano Wani Bible Da 'Jesu...
02/04/2025

MABIYA ADDININ KIRISTANCI NA DUNIYA NA FUSKANTAR BARAZANA
Hankalin Fafaroma Ya Tashi Sak**akon Gano Wani Bible Da 'Jesus'
Ke Wasiyyan Zuwan Annabi Muhammadu (S.A.W)
'Yan sanda a kasar Turkiyya sun gano wani tsohon littafin bible
wanda ake kyautata zaton a cikinsa akwai inda, Annabi Isah A.S
(Jesus) ya yi wa mabiyansa albishir da zuwan Annabin karshe mai
suna Muhammad (Annabi Muhammadu S.A.W).
An yi ittifakin cewa Littafin ya kai shekara 1,500 da rubutawa. Kuma
an rubuta shi ne da ruwan zinari a cikin harshen "Aramaic" (Larabci).
Jaridar Daily Mail ta Amerika ta ruwaito cewa, gano littafin wanda
aka yi hasashen duk falle daya a cikinsa zai kai kimanin Yuro milyan
£14 ya jawo muhawara mai tsanani a tsakanin mabiya darikar Vatican
da musulmi inda har Fafaroma Pope Benedict XVI ya nemi a kawo
masa bibile din ya gani.
Idan dai aka tabbatar da zargin da ake yi akan Bible din kuma ta
tabbata haka din ne. To akwai chakwakiya ganin cewa littafin zai
karyata mabiya addinin kirista dake Allantar da Isah (AS) da kuma
masu cewa Jesus din dan Allah ne. Bible din zai tabbatar da cewa
addinin Islama shine gaskiya kuma Musulmai sune ke kan addini na
gaskiya wanda (Almasihu/Jesus) ya umurci mabiyansa akai.
Majiyar ta mu ta kuma ruwaito cewa an gano littafin ne tun a
shekara ta 2000 amma hukumomin kasar Turkiyya s**a cigaba da
tsaron shi har zuwa shekara ta 2012 inda s**a kaishi gidan tarihi na
Ankara Ethnography Museum. Kuma ana sa ran nan bada jimawa ba
za'a rika nunawa mutane Bible din a gidan tarihin kasar.
Ministan raya Al'adu da yawon bude ido na kasar Turkiyya, Ertugrul
Gunay ya ce suna kyautata zaton Bible din na gaskiya ne shi yasa
wasu s**a boye shi saboda yadda littafin ya yi bayani akan ainihin
matsyin Almasihu (Jesus) sabanin tunaninsu.
Jaridar ta daily mail ta kara da cewa hankalin fafaroma da sauran
manyan limaman kiristoci ya tashi sak**akon gano wannan littafi na
Bible.
Don Allah idan ka karanta ka tura a other groups.

Ishaq Digital Hub

Dan Sanda Guda 1 Kenan Daya Gama Aikin Sa Cikin Nasara Da Soyayyar Al'ummah ✊CP WAKILI MWane fata dakay masa?Barkan mu d...
02/04/2025

Dan Sanda Guda 1 Kenan Daya Gama Aikin Sa Cikin Nasara Da Soyayyar Al'ummah ✊

CP WAKILI M

Wane fata dakay masa?
Barkan mu da safiya
Ishaq Digital Hub

Ziyarar da muka kawo muku ba ta ta’aziyya kadai ba ce, ziyara ce ta tabbatar da cewa an yi wa mutanenmu na arewa da aka ...
01/04/2025

Ziyarar da muka kawo muku ba ta ta’aziyya kadai ba ce, ziyara ce ta tabbatar da cewa an yi wa mutanenmu na arewa da aka yi ajalinsu a jihar Edo adalci in ji gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf a yayin da ya kai ziyara kauyen Toronkawa, kauyen mutanen da abin ya ritsa da su tareda governor na Edo State.

Address

JK/Fari
Gombe

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Ishaq Digital Hub posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Ishaq Digital Hub:

Share