10/10/2025
JIBWIS Internet Media Committee Ta Gabatar Da Taron Bita Ga Membobinta
A kokarinta na ganin membobinta sun cigaba da yin aiki cikin kwarewa da bin dokoki da kaโidodi na addinin musulunci da dokar kasa, Kwamitin Yanar Gizo na kungiyar Jamaโatu Izalatil Bidโah Wa Ikamatis Sunnah NHQ Jos, reshen jihar Gombe ta gabatar da taron bita domin fadakar da membobin sanin makamar aiki.
Taron wanda ya gudana a karkashin jagorancin Shugaban Majalisar Malamai na jihar Gombe, Sheikh Hamza Adam Abdulhamid, ya samu hakartan babban daracta janar na harkokin yada labarai na gidan Gwamnatin jihar Gombe (Director General Press Affairs, Government House) Ismail Uba Misilli.
A yayin jawabinsa, Sheikh Hamza ya bayyana cewa harkar yada labarai yana da asali a cikin Alkurโani mai girma, da kuma rayuwar Annabi Muhammad SAW. Shehin Malamin ya karanto ayoyin Alkurโani mai girma da bayanai na salon isar da sako da Annabi Muhammad SAW yayi amfani dasu a lokacin rayuwarsa, kuma ya bayyana dokoki da hukunce-hukuncen harkar yada labarai daga Alkurโani da Hadisi.
Sheikh Hamza ya yabawa yan kwamitin bisa aiki tukuru da sukeyi wajen yada karatuttuka, waโazozi da aiyyukan kungiya a kafafen sadarwa, ya kirayesu da cewa su kyautata niyya wajen yin aikin domin samun lada a wajen Allah SWT.
A jawabinsa, Hon. Ismaโil Uba Misilli ya yabawa tsarin gudanarwa na kungiyar Izala, yana mai bayyana cewa kungiya ce da take tafiya akan tsari da ladabi da biyayya da girmama shugabanci.
Hon. Misilli ya jinjinawa kwarewa da yan kwamitin yanar gizo na kungiyar Izala suke nunawa a cikin aiyyukansu, ya kuma kirayesu da suyi aiki da abunda s**a koya a yayin taron bitar.
Wadanda s**a gabatar da makala a taron, Barrister Abdulhayyi Saโid Imam da Ustaz Abdulaziz Isa Waziri, sun karantar da mahalarta taron kundin tsarin gudanar da Kwamitin, da kuma dokoki da kaโidodi da s**a shafi harkar yada labarai na zamani.
Taron wanda ya gudana a babban dakin taro na Masallacin Jumaโan Izala na daya dake shagon goro, ya samu halartan rassan kungiyar na kananan hukumomi da yankunan cigaba guda 27 dake fadin jihar Gombe
Jibwis Gombe State
Internet Media