Madubi - H

Madubi - H The Only Hausa News Blog You Can Trust

Yau Shekaru 14 da kotun koli ta sake tabbatar wa yar wasan hausa (Kannywood) Rabi Isma'il (Rabi Acid) hukuncin kisa.A ra...
08/07/2025

Yau Shekaru 14 da kotun koli ta sake tabbatar wa yar wasan hausa (Kannywood) Rabi Isma'il (Rabi Acid) hukuncin kisa.

A ranar 8 Ga Watan Yuli 2011, kotun koli ta tabbatarwa jarumar Kannywood hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Rabi Isma'il (wacce ake yiwa lakabi da Rabi Acid) yar Asalin Jihar Edo ce, amma haifaffiyar Tudun Wada a Kano ce, ta fito a fina-finan Kannywood wanda su ka hada da Tsumagiya, da Aya, da Manakisa. A ranar Kirsimetin shekarar 2002, Rabi ta tunkuda saurayinta Alhaji Ibrahim Zazu cikin ruwan Tiga, in da rai yayi halinsa. Amma kafin ta tunkudashi shi cikin ruwan, sai da ta ba shi alewa cakuletin Ekiles wacce tayiwa cushe da maganin bacci. Sai da Rabi ta tabbatar ya fita a hayyacinsa sannan ta lalube aljihunsa ta kwashe kudi naira dubu dari, kana ta tunkudashi cikin ruwan.

Wannan dama dai ya nuna da niyar kisa ta tura Auwalu Zazu cikin ruwan. Jami'an binkice sun gano rabi ta aikata hakane domin ta gaje dukiyarsa. Kasancewarsa hamshakin maikudi.

Don haka a ranar 5 ga Junairun shekarar 2005 babbar kotun jihar Kano ta sami Rabi Acid mai lambar fursuna k/22c da laifin kisan kai. Mai shari'a Halliru Muhammad Abdullahi ya yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya, sai dai Rabi ta daukaka kara a kotun daukaka kara da ke Kaduna. A nanma dai kotun ta sake tabbatar wa da Rabi laifinta. Daga nan kuma sai ta sake daukaka kara zuwa kotun koli da ke Abuja. In da a rana mai k**ar ta yau 8 ga watan Yuli 2011 kotun koli ta tabbatar mata hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Alkalan kotun guda bakwai karkashin mai shari'a Francis fiddodi Tabai, sunce sun gamsu da hujjujin da aka bayar a kotun farko, don haka su ka sake tabbatar mata da hukuncin Kksa ta hanyar rataya. Sai dai k**ar a Fim! A ranar 16 ga watan disambar 2011, sai Rabi Isma'il tayi batan dabo daga gidan yarin Hadejia, in da aka neme ta kasa ko sama aka rasa.

Bayanai sunce a kurkukun Kano aka fara daureta kafin daga baya a mayar da kurkukun Kaduna lokacin da ta daukaka kara. In da a can ne Rabi Isma'il ta zama Jar wuya, in da ta rika safarar sigari da kwaya da Wiwi. Har ma anyi zargin Rabi tana sheke ayar ta ne da manyan jami'an gidan yarin a lokacin da ta ke a tsare.

Bayan da kotun koli ta yanke mata hukuncin kisa sai a ka sauya mata matsuguni zuwa gidan kurkukun Hadejia. A Hadejian ne ta yaudari wani babban Ganduroba, su ka tsunduma cikin kogin soyayya. Ana wannan halin ne ta ke shaida masa cewa ta mallaki Miliyoyin Naira, kuma da zai nema mata bizar Amurka ya fitar da ita daga kurkuku za ta aure shi," su ta re a can suyi ta cin duniyarsu da tsinke. Haka kuwa a kai a ranar 16 ga watan Disambar 2011, sai jami'in nan yayi hanyar da Rabi ta bi ta sulale daga kurkukun.

Sai dai a ranar 21 ga watan mayun 2017, jami'an tsaron DSS Su ka cafke Rabi Isma'il a kan iyakar Najeriya da Jamhuriyyar Benin.
A cewar mai magana da yawun hukumar gidan yarin, Francis Enobore, jami’an leken asiri na hukumar kula da gidajen yari ta Najeriya ne s**a sake k**a Ismail tare da goyon bayan jami’an tsaro na DSS.

Daga nan su ka mika ta ga hukumar kula da gidajen Kurkuku ta kasa, a in da su ka sa ma mata gurbi a gidan kurkukun Kuje da ke Abuja. Shi kuma Ganduroban da ya taimaka mata ta tsere, an rage masa mukami tare da sauya masa wajen aiki. Hakan dai bai wa abokan aikinsa sa yawa dadi ba! Kasancewar laifinsa ya cancanci kora da gurfana a gaban Kotu.

Izuwa yanzu dai ba ni da labarin wani hali Rabi Isma'il (Rabi Acid) ta ke ciki...

✍️ Muhammad Cisse.

Ko ni natsaya takarar shugaban kasa zan kada yan sabuwar Tafiya Shin Kun Yadda Cewar Rarara Zai Iya Kayar Da Su Atiku Ab...
07/07/2025

Ko ni natsaya takarar shugaban kasa zan kada yan sabuwar Tafiya

Shin Kun Yadda Cewar Rarara Zai Iya Kayar Da Su Atiku Abubakar Idan Ya Tsaya Takarar Shugabancin Nijeriya Kamar Yadda Ya Bayyana?

Kamfanin NNPC ya Zaftare Farashin Litar Man Fetur Daga Naira 945 Zuwa 910Nawa kuke fatan farashin litar man fetur ya daw...
07/07/2025

Kamfanin NNPC ya Zaftare Farashin Litar Man Fetur Daga Naira 945 Zuwa 910

Nawa kuke fatan farashin litar man fetur ya dawo a Nijeriya?

Zamu Ci Gaba da Yaƙar Masu Kashe Masallata da Kirista a NajeriyaShugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya jaddada kudirin gwamn...
07/07/2025

Zamu Ci Gaba da Yaƙar Masu Kashe Masallata da Kirista a Najeriya

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya jaddada kudirin gwamnatinsa na tabbatar da walwala da samar da kayan yaƙi ga rundunar sojin Najeriya don ci gaba da yaƙar ta'addanci

Da yake jawabi a wajen bikin zagayowar ranar sojoji karo na 162 a Kaduna, Tinubu wanda mataimakinsa Kashim Shettima ya wakilta, ya tabbatar wa sojojin da cikakken goyon bayansa wajen tunkarar ‘yan ta’adda da kuma fatattakar su.

Shugaban ya misalta ƴan ta'addan da marasa imani, da basu martaba addini ko ƙabila, inda ya ce gwamnatinsa ba zata yi ƙasa a gwiwa ba wajen ci gaba da yaƙarsu

Shugaban ya yi alkawarin ci gaba da saka hannun jari a fannin samar da kayan aikin soji na zamani, da kafofin bayanan sirri, da samar da walawala ga rundunar don tabbatar da cewa jami’anta basu rasa mak**ai da kwarewa ba.

Shugaban ya amince da kalubalen tsaro da ke barazana ga zaman lafiya da hadin kan al’ummar kasar, waɗanda s**a haɗa da ta’addanci, tayar da ƙayar baya, da ‘yan fashin daji da masu tayar da zaune tsaye.

Shugaban ya bukaci sojojin Najeriya da su ƙara zage damtse tare da ba su tabbacin cikakken goyon bayansa da na ‘yan Najeriya.

Shugaban ya jinjina wa jaruman da s**a riga mu gidan gaskiya tare da jajanta wa iyalansu, inda ya basu tabbacin ci gaba da tunawa da su na har abada.

“Kuna da cikakken izinina da na al’ummar Najeriya kan fatattakar masu zagon kasa a ƙasarmu,” in ji Tinubu.

"Ba mu da wata kasa da ta wuce Najeriya, kada mu miƙa makomarta ga rarrabuwar kawuna, ko nuna halin ko-in-kula"

Taron ya samu halartar manyan baki da dama da s**a hada da tsohon shugaban kasa Janar Yakubu Gowon, gwamnan jihar Kaduna Malam Uba Sani, da Ministocin Tsaron Najeriya, Muhammad Badaru Abubakar da Bello Matawalle, sai shugaban hafsan soji Laftanar Janar Olufemi Oluyede.

Babu maganar cewa zan yi wa Atiku mataimaki, takarar shugaban kasa zan yi a 2027 domin na cancanta in ji Peter ObiTsohon...
06/07/2025

Babu maganar cewa zan yi wa Atiku mataimaki, takarar shugaban kasa zan yi a 2027 domin na cancanta in ji Peter Obi

Tsohon dan takarar shugaban Nijeriyar ya fadi haka ne a yayin tattaunawarsa da Channels TV da aka wallafa a wannan Lahadi.

Amsa kawai
06/07/2025

Amsa kawai

DA ƊUMI-ƊUMI: Farashin Kayan Abinci Yana Ta Sauka A NajeriyaRahotanni sun tabbatar da cewa ana ta samun saukar kayan abi...
06/07/2025

DA ƊUMI-ƊUMI: Farashin Kayan Abinci Yana Ta Sauka A Najeriya

Rahotanni sun tabbatar da cewa ana ta samun saukar kayan abinci a Najeriya, kwanan shinkafar da ada ake saya a kan Naira 3,000-4,000 yanzu ba ya wuce Naira 2,700-2,500.

Majiyoyi masu tushe sun tabbatar wa Dokin Ƙarfe TV cewa faɗuwar farashin kayayyakin ba iya shinkafa kaɗai ya shafa ba, ya haɗa har da dukkan sauran kayayyaki k**ar su mai, masara, wake da gero, da sauransu.

Shin ya farashin kayayyakin masarufi suke a inda kuke ?

*Fadar Shugaban Kasa Ta Mayar da Martani akan Sukar Datti Baba-Ahmed* Ofishin mataimakin shugaban kasa ya mayar da marta...
05/07/2025

*Fadar Shugaban Kasa Ta Mayar da Martani akan Sukar Datti Baba-Ahmed*

Ofishin mataimakin shugaban kasa ya mayar da martani ga kalaman Sanata Datti Baba-Ahmed, dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar Labour a 2023, wanda ya yi s**a kan matakin da shugaba Tinubu ya dauka na ci gaba da barin mataimakinsa Kashim Shettima akan karagarsa.

A wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun Mataimakin Shugaban kasar, Stanley Nkwocha, ofishin ya bayyana kalaman na Baba-Ahmed a matsayin" kalamai marasa kan gado" wadanda shugaban kasa da mataimakinsa basu da lokacin sauraronsu, kasancewar sun mayar da hankali kan ayyukansu na gina ƙasa.

Sanarwar ta kuma bayyana irin nasarorin da mataimakin shugaban kasa Shettima ya samu da ma kwarewarsa akan aiki da ta haɗa da gogewarsa a harkar koyarwa da bayar da ilimi da kasancewarsa ma’aikacin banki, sannan kwamishina, sannan gwamna gwamna, kana sanata, kafin ya zama Mataimakin ShugabanKasa.

Sanarwar ta ci gaba da cewa Shettima na biyayya ga shugaba Tinubu k**ar yadda yake nuna jajircewarsa kan tabbatar da ajandar sabunta fata ta Renewed Hope a turance.

Ofishin ya kuma tunatar da Baba-Ahmed abubuwan da s**a faru a baya, da s**a hada da cire shi daga majalisar dattawa a shekarar 2011 bayan da aka zarge shi da magudin zabe inda ta ƙara da cewa, zantukan na Baba Ahmed watakila ba za su rasa nasaba da ƙwaɗayinsa na ɗarewa kowace irin kujerar mulki ba ko da kuwa ta haramtacciyar hanya ce, musamman ma kujerar Mataimakin Shugaban kasar wadda Datti Baba-Ahmed din ya sha kaye a takararta a zaɓen bara sak**akon karawarsa da gogaggen ɗan siyasa ɗan asalin Arewa wanda ke da tarin abin faɗa na nasarori a ajandar sabunta fata ta Shugaban Kasa.

ZAƁEN GWAJI 2027APC ko ADC?
05/07/2025

ZAƁEN GWAJI 2027

APC ko ADC?

Matasa Ku Farka Kar Ku Yarda A Ƙara Wasa Da Ƙwaƙwalenku Ana Bautar Da KuDAGA Bashir Abdullahi El-bashTa ya za a yi mutan...
05/07/2025

Matasa Ku Farka Kar Ku Yarda A Ƙara Wasa Da Ƙwaƙwalenku Ana Bautar Da Ku

DAGA Bashir Abdullahi El-bash

Ta ya za a yi mutanen da s**a kawo rashin tsaro a ƙasa, s**a haifar muku da tsadar rayuwa da talauci za su dawo su ƙara neman mulki kuma ku ƙara yarda ku sake ba su dama ? Ko shakka babu idan kuka sake ba su dama tamkar kun ƙara ba su lasisin ci gaba da haifar muku ƙarin matsaloli ne.

Idan ka cire Atiku cikin gungun waɗannan masu neman mulkin babu wanda ba da shi aka yi gwamnatin Buhari ba, sai ƴan kaɗan, amma su ne dai s**a ce Jonathan bai iya ba s**a shiga s**a fita Buhari ya hau aka kafa gwamnati tare da su kuma s**a tsunduma al’umma a wahalar da ta fi ta lokacin Jonathan.

Yanzu ma sun ƙara tasowa za su yi amfani da halin da kuke ciki wanda su ne silar faɗawarku cikinsa domin su sake yin amfani da ku. Da ace Tinubu yana yi da su na tabbata ba za ku ji motsinsu da sunan adawa ba.

Haƙiƙa, matasa ku ke da tasirin kafa gwamnati domin kowa ya ga gudunmawar da kuka bayar wajen kawo gwamnatin Buhari, kun yi amfani da Social Media k**ar yadda aka yi a Amerika wajen kafa gwamnati. Dan haka a wannan karon ku zama a ankare, ku yi amfani da wayewarku kar ku bari waɗancan mutanen su wawuntar da tunaninku.

Ban ce dole sai kun yi APC ba, amma dai ku tsaya ku auna. Gwamnatin Tinubu ba ta hana adawa ba, duk adawa mai amfani ko shawara tana maraba da ita. Wannan tasa za ku ga duk inda aka samu ƙorafe-ƙorafe tana ɗaukan matakin gyara.

Misali, cire ministar jinƙai Beta Edu da a gwamnatin Buhari ne ba za a cire ta ba. Haka shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dakta Ganduje, yadda yake da ƙarfi a wannan gwamnatin na tabbata da a gwamnatin Buhari ne ba za a cire shi ba. Kenan za mu iya cewa gwamnatin Tinubu tana sauraro. Dan haka duk inda kuka ga matsala ko kuke da wani ƙorafi kai tsaye ku yi, amma dai kar ku yarda ku sake yarda waɗancan mutanen su yi amfani da ku domin sake dawo wa kan mulki.

YANZU-YANZU: Gwamnan Kano ya amince da naɗa Ahmed Musa a matsayin sabon babban Manaja na kungiyar kwallon  ƙafa ta Kano ...
04/07/2025

YANZU-YANZU: Gwamnan Kano ya amince da naɗa Ahmed Musa a matsayin sabon babban Manaja na kungiyar kwallon ƙafa ta Kano Pillars

Cikin su waye ya cancanci tsayawa takarar shugaban kasa a ADC?
04/07/2025

Cikin su waye ya cancanci tsayawa takarar shugaban kasa a ADC?

Address

Gombe

Telephone

+2347080511115

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Madubi - H posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Madubi - H:

Share