13/09/2026
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Najeriya (INEC) ta wallafa jerin sunayen ƙarshe na ƴan takarar shugaban ƙasa da mataimakansu da za su fafata a babban zaɓen watan Janairun 2027.
Jerin sunayen, wanda Sakatariyar Hukumar, Rose Oriaran-Anthony, ta sanya wa hannu, kuma aka fitar da shi ranar Asabar a Abuja, ya ƙunshi ƴan takarar da jam'iyyun siyasa 18 s**a tsayar domin neman kujerar shugaban ƙasa a 2027.
Hukumar ta INEC ta bayyana sunayen'yantakarar 18 da mataimakansu ga dai wasu daga cikinsu:
APC
Tinubu da Shettima
Shugaban kasa mai ci a Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, shi ne dan takarar shugaban kasa a jam'iyya mai mulkin Najeriya APC, kuma Kashim Shettima, shi ne zai sake yi masa mataimaki a zaben 2027.
ADC
Atiku da Amaechi
Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa a Najeriya a lokacin mulkin Obasanjo, shi ne zai yi wa jam'iyyar ADC takarar shugaban kasa, inda Chibuike Rotimi Amaechi kuma zai masa mataimaki.
NDC
Obi da Kwankwaso
Peter Gregory Obi, tsohon gwamnan jihar Anambra kuma tsohon dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour a zaben 2023, shi ne zai yi wa jam'iyyar NDC, takarar shugaban kasa a zaben 2027 da ke tafe, yayin da Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso kuma zai masa mataimaki.
Sauran 'yan takarar shugaban kasa da mataimakansu a zaben na 2027, sun hada da;
Jam'iyyar LP, in da Sunday Chibuzo Okereke, zai yi mata takarar shugaban kasa Hajja Bintu Konto, kuma mataimakiya.