09/09/2025
Ziyarar Shugaban JIBWIS Jihar Bauchi
Shugaban Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) na Jihar Bauchi, Prof. Zubairu Abubakar Madaki, ya kai ziyara zuwa gidan Mataimakin Shugaban Majalisar Malamai na Ɗaya na Kungiyar Izala, Mai Hedikwata a garin Jos, Sheikh Yusuf Muhammad Sambo Rigachikum, a gidansa dake garin Rigachikum, Jihar Kaduna.
Muna addu’ar Allah Ya albarkaci wannan ziyara, Ya ƙara ɗorewar haɗin kai da zumunci a tsakanin malamai, Ya kuma ba shugabanni ikon gudanar da jagoranci cikin adalci da hikima.