21/12/2024
🗣️Idan Kana So Ka Samu Followers a Faceb00k Kuma Su Fara Biyanka Dole Saika Cika Waɗannan Sharuɗan Da Zan Lissafa Maka.
1. Ƙirƙirar Abinda Zaija Hankali
Ka Tabbatar Abin Da Kake Wallafawa Yana Da Kyau, Kamar Abubuwan ilmantarwa, Da Nishadantarwa, Ko Kuma Na Taimakon Mutane Kan Abinda Basu Sani Ba.
Ka Rika Wallafa Abinda Kakeyi Akai-akai (Misali, Sau Biyu Ko Sau Uku a Sati). Wannan Yana Kawo Hankalin Mutane Kuma Yana Muna Cewa Kai Jajirtacce Ne.
2. Ƙirƙirar Abinda Yake Trending
Ka Riƙa Wallafa Abubuwan Dake Da Alaƙa Da Abubuwan Da Mutane S**afi Magana Akansu a Lokacin, Kamar Abubuwan Da S**a Shafi Kide-kide, Fina-finai, Ko Wasu Abubuwan Da Suke Trending.
Facebook Yana Bada Fifiko Ga Bidiyo Da Hotuna a Wajen Tafiyar Da Ayyukan Ka. Ka Tabbatar Kana Amfani Dasu Sosai.
3. Kayi Mu'amala Da Mabiyanka
Kake Yin Reply Ga Masu Yi Maka Comment Ka Amsa Tambayoyinsu, Kuma Ka Nuna Godiya Ga Waɗanda Suke Son Ayyukan Ka. Wannan Yana Ƙarfafa Ka Tare Da Ƙara Haɗaka Da Mabiyanka.
4. Dole Ne Ka Cika Waɗannan Sharuɗɗa Kafin Ka Samu Damar Samun Kuɗin Faceb00k:
Samun Mabiya Aƙalla 10,000 Ko Fiye Da Haka.
Samun Mintuna 60,000 Na Masu Kallon Bidiyon Da Kake Wallafawa Acikin Wata 12 Da S**a Gabata Ko Kallon Bidiyon Ka Na Minti 3 Sau 30,000.
Ka Tabbatar Kabi Dokokin Faceb00k Monetization Policies.
Da Zarar Facebook Sun Buɗe Maka Ɗaya Daga Cikin Waɗannan Abubuwan Insha Allah Zaka Fara Samun Kuɗi Dasu. In-stream Ads, Ko Subscriptions Ko Kuma Ads On Reels.
Ka Dage Kuma Ka Kasance Mai Haƙuri, Saboda Yana Ɗaukar Lokaci Kafin Kakai Ga Wannan Matakin..