03/06/2026
MAKIRCIN DA AKA ƘULLA A DARREN JIYA KAN JIHAR GOMBE DA TASIRIN PROFESSOR ISA ALI PANTAMI
An gudanar da wani taro a Gidan Gwamnati a daren jiya, Talata 2 ga Yuni, 2026. A cewar bayanan da s**a fito daga taron, babban abin da ya mamaye tattaunawar shi ne Malam Isa Ali Pantami, inda aka mayar da hankali kan muhimman batutuwa uku:
1. Sun sani sarai cewa Malam Isa Ali Pantami bai shiga abin da suke ƙira zaɓen fidda gwani ba. Duk da haka, an yi shawarar cewa a ci gaba da tayar da hayaniya a kan lamarin tare da amfani da wasu da ake ƙira masu ruwa da tsaki daga cikin gida domin jawo ruɗani da tsawaita cece-kuce.
2. Karɓuwar da Professor Isa Ali Pantami da sabuwar jam’iyyarsa ta PDP suke samu a faɗin jihar Gombe na ƙara damun su matuƙa. Shigowarsa ya sake farfaɗo da jam’iyyar gaba ɗaya. A kusan kowane taro da majalisa, Pantami da jam’iyyarsa su ne abin tattaunawa. A cewarsu, bai kamata a bar wannan yanayi ya ci gaba ba.
Abin takaici a gare su, sun manta cewa ikon Allah ne kaɗai ke tabbatar da abin da zai kasance.
3. A yayin da Malam Isa Ali Pantami ke ci gaba da gabatar wa al’ummar Gombe manufofinsa da kuma “Tsarin Sauya Fasalin Jihar Gombe” a fannoni kamar noma, samar da ayyukan yi, tsaro, ilimi, mata, matasa, masana’antu da sauran su, har yanzu ‘yan takarar su ba su gabatar wa jama’a wata cikakkiyar manufa ko tsari ba.
An ce an yi wa dukkan ‘yan takarar da s**a halarci taron tambayoyi kan wannan batu. A yau, Pantami ya zama abin koyi a gare su ta wannan fuska.
Mu ci gaba da lura da abubuwan da suke faruwa yayin da al’amura ke ƙara bayyana.
Allah Ya rushe duk wani mugun nufi da mugun shiri da ake yi wa al’ummar jihar Gombe da kuma duk wani abu da zai hana samuwar shugabanci Nagari a jihar.
Rubutawa:
Barrista Yahaya Ibrahim
03/Yuni/2026