07/04/2025
Alarammomi na Ahlussunnah Kar ku maida Alqur'ani ya zama abun buki ko neman wata daukaka ta Duniya, domin naga kullum kirkiro sabbin abubuwa akeyi akan Qur'ani.
Naga yanzu ma an kirkiro wani abu wai Yaumul Qurraa, kuji tsoron Allah kar neman Duniya da neman Burgewa yasa kuna kwaikwayo wasu Bukukuwa daga wajen Yahudu ko yan Bidi'ah kuna kawo shi cikin tafiyar Sunnah.
Allah ya kara daura mu akan dai-dai.