16/03/2026
Kotun Kolin ƙasar Saudiyya ta yi kira ga mazauna ƙasar su soma duban jaririn watan Shawwal ranar Laraba da maraice, 29 ga watan Ramadan Hijira 1447 AH wanda ya zo daidai da 18 ga watan Maris, 2026.
A wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, kotun ta buƙaci duk wanda ya ga watan da idanunsa ko kuma ta hanyar na'ura ta musamman, to ya kai rahoto ga kotun da ke kusa da shi.
Ta ƙara da cewa sakamakon ganin watan ne zai bayar da damar sanar da ranar da za a yi Ƙaramar Sallah.