Diwani Group Gombe

Diwani Group Gombe ☆《لاإله إلاأنت سبحانك إني كنت من الظالمين 》☆
☆《عليه صلاةالله ثم سلامه بديوان طاه الهاشمي صرت ملحقا》☆

03/03/2025
RAMADAN KAREEM 2025BARKAMMU DA SHAN RUWA YAN UWA. HAPPY RAMADAN DAY 0️⃣0️⃣3️⃣إِذَا شَرَعْتَ فِي ادِّكَارِ الْوِرْدِ فَلا...
03/03/2025

RAMADAN KAREEM 2025

BARKAMMU DA SHAN RUWA YAN UWA. HAPPY RAMADAN DAY 0️⃣0️⃣3️⃣

إِذَا شَرَعْتَ فِي ادِّكَارِ الْوِرْدِ فَلاَزِمِ الْأَدَبَ قَدْرَ الْحَدِّ
Idan kun hadu a cikin karanta wuridin to ka lizimci yin ladabi gwargwadon iyaka.

تَأَدُّبٌ فِي ظَاهِرٍ وَبَاطِنِ بِهِ يُرَقَّى الْمَرْءُ لِلْمَوَاطِنِ
Yin ladabi a zahiri da baɗini da shine ake hauhawar da mutum zuwa wuraren zama na muƙaman walittaka.

وَاسْتَحْضِرَنَّ شَيْخَكَ الْـمُرَبِّي كَذَاكَ شَيْخَهُ بِدُونِ رَيْبِ
Ka halarto da kamannin shehinka mai raino gareka haka kuma shaikhinsa, ba tare da kokwanto ba.

وَلاَزِمِ الْحُضُورَ وَالسُّكُونَا كَذَاكَ خلْوَة تُعِينُ حِينَا
Ka lizimci halartar zuciya da nutsuwar gaɓoɓi, haka kuma ka lizimci kaɗaitaka zata taimaka a lokacin wuridin.

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
Allah ya amsa mana ibadummu gaba daya ya sa muna cikin wayanda za a yiwa gafara acikin wannan wata mai Alfarma.dan isar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam 🥰🥰🥰❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️🥰🥰🥰🥰🥰❤️❤️

RAMADAN KAREEM 2025BARKAMMU DA SHAN RUWA YAN UWA. HAPPY RAMADAN DAY 0️⃣0️⃣2️⃣وَلاَزِمُوا لاَزِمَ ذِي الطَّرِيقِ بِذَا يُ...
02/03/2025

RAMADAN KAREEM 2025

BARKAMMU DA SHAN RUWA YAN UWA. HAPPY RAMADAN DAY 0️⃣0️⃣2️⃣

وَلاَزِمُوا لاَزِمَ ذِي الطَّرِيقِ بِذَا يُنَالُ الرِّبْحُ بِالتَّحْقِيقِ
Saboda haka sai ku lazimci lazimin wannan ɗarikar, da wannan ne za a sami riba bisa tabbatarwa.

فَلَسْتَ فِي أَخْذِ الطَّرِيقِ تَرْبَحُ إِلاَّ إِذَا كُنْتَ دَوَامًا تُصْلِحُ
Ba zaka sami riba a cikin karban darikar ba, har sai ka kasance kana da nagarta kowane lokaci.

مُكَمِّلاً شُرُوطَهُ الْمُقَرَّرَهْ مُكَابِدًا آدَابَهُ الْـمُعْتَبَرَهْ
Mai cika sharudansa wanda aka tabbatar mai yin gogayya da ladubansa abubuwan lura.

مُعَظِّمًا لِأَهْلِهِ جَمِيعًا لاَ سِيَّمَا الْخَاصةُ كُنْ مُطِيعًا
Mai girmama Ahlin dariƙar baki ɗaya, musamman ma keɓantattu, ka zama mai yin biyayya.

Allah ya amsa mana ibadummu gaba daya ya sa muna cikin wayanda za a yiwa gafara a cikin wannan wata mai Alfarma. dan isar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam 🥰🥰🥰❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️🥰🥰🥰🥰🥰❤️❤️

02/03/2025

Yawaita Salati Ga Manzon Allah ﷺ Sallallahu Alayhi Wa Sallam Yana Yaye Damuwa Kuma Yana Sa Allah Ya Biya Ma Mutum Bukata.👌

Address

Jekadafari Abcha Road Gombe
Gombe

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Diwani Group Gombe posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share