12/09/2025
Kasan cewa zaka iya “Printing” gida kamar yadda kake printing takarda?
NB: Hoton dake kasa, hoton gida ne a kasar dubai, da akayi Printing dinsa da fasahar massive 3D printer, tsayinsa ya kai mita 9.5 (ƙafa 31) kuma yana da fadin mita 640 (ƙafa 6,889). An gina katangar siminti na ginin a wurin kai tsaye ta amfani da babban na’urar 3D Printer.
Bari muyi bayanin a fayyace, Misali, baka da gida kuma bakason zama gidan haya. Ga bikinka saura sati ɗaya, amma ginin gida bazai yiwu cikin sati ɗaya ba. To da fasahar 3D Printing zaka iya design na gidan a cikin computer, ita kuma na’urar 3D Printer zata maka printing ɗin gidan nan cikin kwanaki 3 kacal. Sai dai kawai ku shiga kai da amaryarka..😀
Tabbas wannan ba mafarki ba ne, wannan shi ake kira da Fasahar 3D Printing.
Farko dai menene 3D Printing?
3D Printing wata fasaha ce da take amfani da na’ura ta musamman domin ta samar maka da wani abu daga computer zuwa zahiri. Kamar yadda printer ke buga rubutu a takarda bayan an saka mata softcopy, ita kuma 3D Printer tana iya buga maka abu mai kauri ko mai girma kamar irin su gida, kayan wasa, ko ma sassan jikin ɗan’adam.
Yadda 3D Printer ke aiki:
Za'a fara zana abinda ake so ayi printing a cikin Computer (misali mota toy, kofin shayi, ko ginin gida). Bayan an kammala wannan zanen, na’urar zata raba zanen da aka saka mata gida-gida (layers). Sai ta fara buga sashen farko na zanen, a haka zata dinga yi tana dora na gaba, har sai ta kammala cikakken abinda akeso ta fitar.
Misali, a kasar Dubai an taba buga gida cikin kwanaki 3 kacal ta amfani da fasahar 3D Printing. Haka zalika a fannin lafiya, an dade ana amfani da fasahar wurin buga ƙasusuwan kunne da kafafu (prosthetics) da ake saka wa marasa lafiya. Hukumar NASA dake america suna amfani da 3D Printing wajen yin kayan bincike na sararin samaniya.
A Najeriya, akwai matasa da ke amfani da fasahar 3D Printing wajen yin hannaye na roba ga yara masu nakasa.
Ana sa ran an gaba idan fasahar ta kammala mamaye duniya zaka iya mallakar gida mai arha cikin kwanaki kaɗan. Likita kuwa zai iya printing maka sashen jikin mutum da zai dasa wa mara lafiya. Masana’antu zasu rage dogaro da import saboda mutane zasu iya buga abubuwan da suke buƙata daga gida.
A takaice, 3D Printing fasaha ce da zata sauya duniya gaba ɗaya, tun daga bangaren lafiya, zuwa gine-gine, zuwa harkar ilimi.
Allah yasa mu dace. 🤲
Salisu Abdurrazak Saheel