Fityanul Islam Of Nigeria

Fityanul Islam Of Nigeria Yada Soyayyan Annabi ﷺ Da Salihan Bayin Allah Waliyai Tare Da Fadakarwa Tunatarwa Ga Al'ummar Musulmi Alhamdulillah

HOTUNA: Yanda Aka Gudanar Da Taron Addu'a Na Musamma Ga Marigayi Shugaban Kasa Gen. Muhammadu Buhari Wanda Allah Ubangij...
20/07/2025

HOTUNA: Yanda Aka Gudanar Da Taron Addu'a Na Musamma Ga Marigayi Shugaban Kasa Gen. Muhammadu Buhari Wanda Allah Ubangiji Madaukakin Sarki Ya Karbi Rayuwar Sa A Satin Daya Gabata.

Anyi taron ne karkashin jagorancin Sayyadi Alhaji Ibrahim Sheikh Dahiru Usman (Khadimul Faidha) Tare Da Sauran Yan'uwa Masoya.

Allah Ya Jikan Sa Da Rahma, Ya Gafarta Masa, Ya Sakawa Duk Wanda S**a Shirya Taron Da Alkhairi. Amiiiin Yaa ALLAH

Fityanu Media
Date: 20, July/2025

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN!!!...Mahaifin Sheikh Harisu Salihu Jos Ya Rasu.Allah ya yiwa Sheikh Salihu Abubakar ...
17/07/2025

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN!!!
...Mahaifin Sheikh Harisu Salihu Jos Ya Rasu.

Allah ya yiwa Sheikh Salihu Abubakar Wase (Baban Wase/Wazirin Malaman Wase) rasuwa a yammacin yau Alhamis 22/01/1447 - 17/07/2025 a garin Wase, Jihar Plateau.

Gobe Juma'a da ƙarfe Tara Na Safe (09:00am) za'a yi Jana'iza a garin Wase, In Shaa Allah.

Allah ya jaddada masa Rahmah Albarkar Shehu Tijani Radhiyallahu Ta'ala Anhu. Amiin Yaa ALLAH

Daga: Sheikh Harisu Jos

BARKA DA JUMA'AT: Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi OFR, Allah Ya Bamu Albarkan ANNABI MUHAMMADU saww. Amiin Yaa Allah
11/07/2025

BARKA DA JUMA'AT: Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi OFR, Allah Ya Bamu Albarkan ANNABI MUHAMMADU saww. Amiin Yaa Allah

SON ANNABI MUHAMMADU SALLALLAAHU ALAIHI WASALLAMA IMANI NE. Kaunar ANNABI Addini ne, so da kaunar ahlin gidansa, da saba...
09/07/2025

SON ANNABI MUHAMMADU SALLALLAAHU ALAIHI WASALLAMA IMANI NE.
Kaunar ANNABI Addini ne, so da kaunar ahlin gidansa, da sababbansa, da duk wanda yake biyayya ko koyi da abin da ya bari.
Duk wanda babu soyayyar ANNABI SALLALLAAHU ALAIHI WASALLAMA a ransa ko Yaji soyayyar wani tafi ta ANNABI a ransa, To Ya binciki imanin sa.
A cikin Hadisai Guda 2 ANNABI ya sanar da mu.
“Babu dayan ku da zai zama yana da imani
Sai ya zamo yafi kauna ta fiye da kansa, mahaifinsa/mahaifiyar sa, Ko dansa/'yarsa da sauran mutane.”
Mutane sun hada da malaminka/oganka/ mai kula da kai, ko wanda ya ke ba ka kariya cikin mutane in ka shiga kunci ko damuwa.
Muyi koyi da ayyukan ANNABI da maganganun sa, Duk wanda ya saba da Umarnin da ANNABI (S.A.W) ya bayar, ko waye! kabi ANNABI ka kyaleshi.
Muyi tutiya da son ANNABI (S.A.W) kuma ku bayyana shi a ko ina, a ko da Yaushe.
Domin yafi kaunar da mu ke tutiya da ita ta matan mu, iyayenmu, ‘Ya’yanmu, da Makusantan mu.
Yin salati ga Annabi yana cikin kauna da soyayyar sa.
Mu yawaita salati gareshi.
Allah ya kara mana son ANNABI SALLALLAAHU ALAIHI WASALLAMA
Amin.

Madinah garin Manzon Allah (saw). Allah ya kaimu birnin Madinatul Munawwara. Ameeeen
08/07/2025

Madinah garin Manzon Allah (saw). Allah ya kaimu birnin Madinatul Munawwara. Ameeeen

06/07/2025

SHI DA KANSA MAI MAGANAR SAI DAI YA FITO YA BAYYANA NADAMAR SA DA TUBAN SA (Malam Abdul Jabbar Yayi Nadama).

06/07/2025

RADDI ZUWAGA ABDUL JABBAR TARE DA SAQO ZUWA GA IYAYE AKAN 'YA'YAN SU DAGA SHEIKH FERFESA UMAR SANI FAGGE KANO.

06/07/2025

GASKIYAR ZANCE: Kada a kautar mana da hankula mana daga irin wannan katobarar har ma a dinga bashi mafita da kariya kamar ba annabin ne a gaban mu ba.

Tare da dukkan girmamawa zan so Prof ya saurari maganganun Abduljabbar Kabara da sune s**a janyo kotu ta hukuntashi.Daga...
06/07/2025

Tare da dukkan girmamawa zan so Prof ya saurari maganganun Abduljabbar Kabara da sune s**a janyo kotu ta hukuntashi.

Daga: Malam Aminu Daiba Kano

Lokacin ƙadayyar Abduljabbar idan ban manta ba Naji Prof din yace bai saurara ba kuma baya so ya saurara, to tunda Malam yana so yace wani abu game da batun to zan so ya saurara domin yiwa ko wane ɓangare Adalci.

Abin da yasa na magantu na samu halartar zaman shari'ar Abduljabbar 70%100 kuma na saurari tuhume tuhumen da ake masa da zaman muƙabalar da akayi, tun kafin nan nata bibiyar karatuttukansa da raddin da malamai suke masa, kaga kuwa zan dan fahimci wani abu dan gane da lamarin.

Bayan gama shari'ar Abduljabbar naji Prof ya magantu, yanzu ma ya dawo da zancen, dan haka zan so na kusa kusa su isar da saƙona ga shugabanmu Prof Ibrahim Maƙari Rahimahullah.

Allah yahanamu zamewa a cikin hadara ta Annabi S.A.W yasa mufi ganin girmansa fiye da komai da kowa. Amiiiin Yaa ALLAH

Allah Ya Saka Maka Da Maficicin Alkhairi, dan'adam yana dai-dai yana kuskure. Allah ya yafe mana kurakuran mu. Amiiiin Y...
06/07/2025

Allah Ya Saka Maka Da Maficicin Alkhairi, dan'adam yana dai-dai yana kuskure. Allah ya yafe mana kurakuran mu. Amiiiin Yaa ALLAH

06/07/2025

DAGA KARSHE PROF MAQARY: Ya yarda Malam Abdul Jabbar yayi batanci ga janibin fiyayyen halitta Annabi MUHAMMADU saw, Amma irin tsarin zaman da hukunci da aka yiwa Abdul Jabbar bai yi ba. Ya kuma bada shawara akan tsarin wa'azi a kasar Najeriya.

Muna kira ga mai girma gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya shirya Muqabala akan magagganun Malam Lawan Triumph akan w...
06/07/2025

Muna kira ga mai girma gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya shirya Muqabala akan magagganun Malam Lawan Triumph akan wasu Hadisai fassaran gatari. Yin haka zai zama adalci ga al'ummar musulmai na Kano, Najeriya har duniyar Musulunci.

Allah yasa gwamnati ta amsa wannan kira na al'umma. Allah ya shirye mu. Amiiiin

Address

Pantami
Gombe
760242

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Fityanul Islam Of Nigeria posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share