26/01/2026
Tsohon Ministan Matasa da Wasanni a Najeriya, kuma ɗan gwagwarmaya, Barrister Solomon Dalung, ya zargi jam’iyyar APC da amfani da hukumomin tsaro, musamman EFCC, domin matsa wa Gwamnatin Jihar Bauchi lamba da nufin tilasta mata sauya sheƙa zuwa jam’iyyar.
Dalung ya bayyana hakan ne a Bauchi yayin da yake jawabi a wani taron bayar da lambar yabo, inda ya ce k**a ma’aikatan gwamnatin jihar Bauchi da EFCC ke yi a halin yanzu na da alaƙa kai tsaye da siyasa, ba yaki da cin hanci ba.
A cewarsa,
“Ni lauya ne, aikina kenan. Kowace rana ina roƙon Allah ya bani aiki, kuma ga shi Allah ya bani aiki. EFCC sun je sun k**a ma’aikatan Bauchi suna tuhumar su da almundahana da ta’addanci, toh mu dai muna bada gudunmawa ne domin ganin an yi yaki da cin hanci da gaskiya.”
Dalung ya zargi APC da nuna wariya wajen yaƙi da cin hanci, inda ya ce ana kallon fuskar mutum kafin a k**a shi.
Ya ce,
“Shugabannin APC sun ce ko mutum ya saci banki ne idan ya gudu ya shiga APC, ya shiga Tudun Natsira. Shi ya sa manyan barayi da ake yi wa shari’a suna komawa APC, aka daina tuhumar su.”
Tsohon ministan ya yi ikirarin cewa ana matsa wa Gwamnatin Bauchi lamba ne saboda ana son tilasta mata shiga APC.
“Yanzu ana matsa wa Gwamnatin Bauchi ne, ana son Gwamnan Bauchi ya koma APC. Rashin yarda da hakan ne yasa ake kwashe ma’aikatan jihar domin a karyashi.”
Dalung ya ce gwagwarmaya da suke yi ita ce kare dimokuradiyya da zaman lafiyar Bauchi, ba kare mutum ɗaya kawai ba.
“Ba wanda ya isa ya tilasta wa Gwamnan Bauchi shiga APC. Idan Allah ne ya so zai je, amma ba da karfi ba. Idan ya ce ba zai je ba, ba hujja ba ce da za a rika k**a ma’aikata.”
Ya kara da cewa manufar k**a manyan jami’an kuɗi ita ce tayar da hankalin jama’a ta hanyar jawo tsaikon biyan albashi, wanda hakan ka iya haddasa rikici.
“Ana son a k**a Kwamishinan Kuɗi, a k**a Accountant General, a hana biyan albashi domin a tayar da rigima. Bauchi tana zaman lafiya, amma ana neman a kawo rikicin kabilanci, addini da siyasa.”
A ƙarshe, Dalung ya ce gwagwarmayarsu na nufin dakile duk wani yunƙuri da zai jefa jihar cikin rikici.
“Mun tashi tsaye ne domin mu kare Gwamnatin Bauchi da Jihar Bauchi gaba ɗaya, mu dakile wannan iskancin.”