30/08/2026
Rasha Ta Taimaka Wa Gwamnatin Nijar Ta Kwato Muhimmin Sansanin Soji a Yamai
Dakarun Rasha sun taimaka wa jami’an tsaron Nijar wajen kwato wani muhimmin sansanin soji a birnin Yamai, bayan wasu sojojin da s**a yi bore sun karɓe ikon sansanin.
Rahoton ya ce dakarun tsaron fadar shugaban ƙasar, tare da taimakon sojojin Rasha, sun sake karɓe ikon sansanin bayan an shafe sa’o’i ana musayar wuta.
Lamarin ya faru ne a cikin rikicin da ya ɓarke a Yamai, inda wasu sojoji s**a kai hare-hare kan wasu muhimman wurare, ciki har da filin jirgin saman Diori Hamani da fadar shugaban ƙasa.
Gwamnatin Nijar ta ce daga bisani ta sake dawo da iko, yayin da ake ci gaba da ƙarfafa tsaro a babban birnin ƙasar.
Wannan lamari na ƙara nuna yadda Nijar ta ƙara dogaro da haɗin gwiwar tsaro da Rasha tun bayan juyin mulkin 2023 da kuma ficewar sojojin ƙasashen Yamma daga ƙasar.