04/09/2025
YAKI DA ‘YAN BINDIGA: BABU GASKIYA CIKIN IKIRARIN DA EL-RUFAI YAKE YI— ONSA
Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaro (ONSA) ya karyata ikirarin da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Mal. Nasir El-Rufai yayi cewa Gwamnatin Tarayya na biyan ‘yan bindiga kudin fansa ko tana basu wasu kudade da zunmar faranta musu.
El-Rufai yayi wannan zargi ne a wani shirin talabijin a ranar Lahadi, inda ya ce ONSA nada hannu wajen biyan kudin fansa ga miyagu. Sai dai cikin gaggawa, Ofishin NSA ta bayyana kalaman nasa a matsayin ƙarya kuma yaudara, tare da jaddada cewa babu ko wata hukuma a ƙarƙashin wannan gwamnati data taba shiga harkar biyan fansa ko kuma bayar da wasu fa’idodi ga ‘yan bindiga.
“A maimakon haka, kullum muna gargadin ‘yan Najeriya kada su shiga biyan fansa,” in ji ONSA, tana mai cewa ikirarin El-Rufai ya saba da gaskiyar dake faruwa a ƙasa.
A cewar Ofishin, Gwamnatin Tinubu ta ɗauki tsari mai ginshiƙai biyu wajen yaƙi da rashin tsaro: amfani da ƙarfi ta hanyar farmaki da kuma shiga tattaunawa da al’umma domin magance korafe-korafen cikin gida. Wannan tsari, in ji ONSA, ya fara samar da sak**ako musamman a yankunan Kaduna k**ar Igabi, Birnin Gwari da Giwa, waɗanda ada suke fama da hare-haren kai-tsaye amma yanzu suna samun zaman lafiya mai ɗorewa.
Haka kuma ONSA tayi karin haske kan nasarorin da jami’an tsaro s**a samu wajen kawar da sanannun ‘yan bindiga ko k**a su a faɗin jihar. Ta tuna da yadda shugabannin miyagu irin su Boderi, Baleri, Sani Yellow Janburos, Buhari, da Boka aka halaka, yayin da aka cafke manyan jagororin ƙungiyar ta’addanci Ansaru da s**a kafa sansani a Kaduna kwanan nan.
Har rashe rashe akayi wajen tabbatar da wannan nasarori, domin wasu daga cikin jaruman jami’an tsaronmu sun sadaukar da rayukansu,” in ji ONSA. “Don haka, abin takaici ne ga tsohon gwamna irin El-Rufai yayi ƙoƙarin musanta waɗannan sadaukarwa a gaban al’umma.”
ONSA tayi kira ga El-Rufai da sauran ‘yan siyasa da su guji jawo hukumomin tsaro cikin rikicin siyasa, tana mai jaddada cewa yaki da ‘yan bindiga yaki ne na haɗin gwiwar kowa da kowa, ba wani abin da za'a amfani dashi zuwa wata fafutikar neman bukatar siyasa ba.