Ck Media Service

Ck Media Service CK Media Service – Labarai na Gaskiya, Don Jama’a.

APC Ta Karyata Rahoton Da Aka Ce Ta Kafa Kwamiti Don Karɓar Gwamna Dauda LawalDaga Gusau – 19 ga Oktoba, 2025Jam’iyyar A...
19/10/2025

APC Ta Karyata Rahoton Da Aka Ce Ta Kafa Kwamiti Don Karɓar Gwamna Dauda Lawal

Daga Gusau – 19 ga Oktoba, 2025

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta Jihar Zamfara ta nesanta kanta daga wani rahoton boge da aka wallafa a shafin confidentialreporters.blogspot.com, wanda ke ikirarin cewa jam’iyyar ta kafa kwamiti domin tarbar Gwamna Dauda Lawal cikin jam’iyyar.

Mai magana da yawun jam’iyyar, Yusuf Idris Gusau, ya bayyana cewa rahoton ƙarya ne kuma marar tushe, yana mai jaddada cewa jam’iyyar APC ba ta taɓa tattaunawa da jam’iyyar PDP ko kuma gwamnan jihar a kan wani yunkuri na shiga jam’iyyar ba.

Jam’iyyar APC ta Jihar Zamfara ba ta taɓa kusantar jam’iyyar PDP ko gwamnan jihar don neman ya shiga jam’iyyar ba. Wannan labari an ƙirƙire shi ne da mugun nufi don yaudaran jama’a,” inji Yusuf Idris.

Ya ce APC ta Zamfara ba ta taɓa gamsuwa da irin tafiyar gwamnatin Dauda Lawal ba, domin, a cewarsa, ayyukan gwamnatinsa sun gaza amfanin jama’a.

Yusuf Idris ya ƙara da cewa nasarar da jam’iyyar APC ta samu a zaben cike gurbi na Kaura Namoda South a ranar 16 ga Agusta, 2025, da kuma komawar ɗan takarar PDP da magoya bayansa zuwa APC, ya nuna irin goyon bayan da jama’a ke nunawa jam’iyyar a Zamfara.

Ya roƙi jama’a da su yi watsi da rahoton confidentialreporters, yana mai cewa jam’iyyar tana da hanyoyin yada bayanai na gaskiya da jama’a ke yarda da su.

Jam’iyyar APC za ta ci gaba da hulɗa da jama’a cikin mutunci da tsari, kuma ba za ta amince da labaran karya daga wasu kafafe marasa amana ba,” inji shi.

YAWAN SHAN LEMU YANA HAIFAR DA RASHIN LAFIYA A JIKIN DAN ADAM.RAHOTO:Wani bincike na masana lafiya ya bayyana cewa yawan...
18/10/2025

YAWAN SHAN LEMU YANA HAIFAR DA RASHIN LAFIYA A JIKIN DAN ADAM.

RAHOTO:
Wani bincike na masana lafiya ya bayyana cewa yawan shan lemu irin su Coca-Cola, Fanta, Pepsi, 7Up, Sprite, Bigi, da LaCasera na iya zama babban barazana ga lafiyar jikin dan Adam, musamman idan ana shansu kullum ba tare da kima ba.

Masana sun bayyana cewa kwalban lemu guda ɗaya na ɗauke da s**ari mai yawa fiye da abin da jiki ke buƙata a rana, wanda ke iya haifar da kiba, ciwon s**ari (diabetes), da cututtukan zuciya (heart disease).

Haka kuma, acid da ke cikin irin wadannan abubuwan sha na iya lalata enamel na hakora, wanda ke haifar da ramuka da zafin hakori, tare da haɗarin samun ciwon ciki ko ulcer.

Bugu da ƙari, wasu daga cikin lemu suna ɗauke da caffeine, wacce ke iya jawo rashin bacci, tashin hankali, da dogaro (addiction) idan ana yawan sha.

Masana sun jaddada cewa, duk da cewa waɗannan lemu suna da daɗi, ba sa ƙara lafiya ga jiki, domin ba sa ɗauke da bitamin ko sinadarin gina jiki, sai s**ari da kalori kawai.

Sun ba da shawarar cewa maimakon haka, mutane su fi karkata zuwa ruwan zobo, ruwan lemon tsami da zuma, ko ruwan kwakwa, waɗanda ke taimakawa wajen ƙara lafiya ba tare da cutarwa ba.

An K**a Brigadier-General tare da wasu jami’an soja masu muk**ai daban-daban bisa zargin shirya juyin mulki domin kifar ...
18/10/2025

An K**a Brigadier-General tare da wasu jami’an soja masu muk**ai daban-daban bisa zargin shirya juyin mulki domin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Majiyoyin tsaro sun shaida wa SaharaReporters cewa jami’an da aka k**a suna da matsayin soja daga Captain zuwa Brigadier-General, kuma an tsare su a ofishin DIA domin bincike kan shirin da s**a yi na kifar da gwamnati ta hanyar karfin soja.

Rahoton ya bayyana cewa jami’an sun fara shirye-shiryen juyin mulki ne tun kafin bikin Ranar ‘Yancin Kai ta Najeriya (1 ga Oktoba, 2025), inda s**a gudanar da wasu tarurruka na sirri domin tsara yadda za su kwace mulki daga hannun gwamnatin farar hula.

Majiyar ta ce an gano cewa wasu daga cikin jami’an sun nuna rashin gamsuwa da salon mulkin gwamnati da kuma matsin tattalin arziki, abin da ya sa s**a fara neman goyon bayan wasu abokan aikinsu don gudanar da juyin mulki.

Kwamishinan Ilimi, Malam Wadatau Madawaki, ya ce malaman da aka mayar suna cikin ma’aikata 780 da aka dakatar saboda kur...
17/10/2025

Kwamishinan Ilimi, Malam Wadatau Madawaki, ya ce malaman da aka mayar suna cikin ma’aikata 780 da aka dakatar saboda kura-kurai na gudanarwa, inda Gwamna Dauda Lawal ya amince da dawo da su tare da biyan bashin albashinsu daga Janairu zuwa Yuli 2025.

RAHOTO; CK MEDIA SERVICES ✍️

Hanif Sani  Shugaban kungiyar Matawalle Dependers yabayyana Haka a shafinsa na Facebook.ya ce akwai dalilai da dama da s...
17/10/2025

Hanif Sani Shugaban kungiyar Matawalle Dependers yabayyana Haka a shafinsa na Facebook.

ya ce akwai dalilai da dama da s**a haifar da wannan mataki, duk da cewa ba lallai ne a bayyana su a wannan lokaci ba, yana mai tabbatar da cewa lokaci ne kadai zai bayyana komai da yardar Allah.

A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Jumu’a, an karyata rade-radin da ake yadawa cewa Gwamna Dauda Lawal zai bar Jam’...
17/10/2025

A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Jumu’a, an karyata rade-radin da ake yadawa cewa Gwamna Dauda Lawal zai bar Jam’iyyar PDP ya koma Jam’iyyar APC.

Sanarwar ta jaddada cewa Jam’iyyar PDP ita ce jam’iyyar gaskiya da amana, kuma babu wani shiri ko niyyar da Gwamnan ke da shi na barin jam’iyyar.

A cewar sanarwar, waɗanda ke yada wannan labari sun ƙirƙira ne da nufin karkatar da hankalin jama’a daga muhimman ayyukan raya ƙasa da gwamnatin Gwamna Dauda Lawal ke aiwatarwa a fadin Jihar Zamfara.

Sai dai wasu manazarta harkokin siyasa sun bayyana cewa irin waɗannan jita-jitai na yawan fitowa ne a lokutan da ake shirye-shiryen siyasa, domin gwada ƙarfin jam’iyyu da kuma jan hankalin magoya baya.

Sarkin Musulmi Ya Nemi Gwamnatin Tarayya Ta Kula Da Amfani Da Kafafen Sada Zumunta, Yace Sun Zama Barazana Ga ƘasaSarkin...
16/10/2025

Sarkin Musulmi Ya Nemi Gwamnatin Tarayya Ta Kula Da Amfani Da Kafafen Sada Zumunta, Yace Sun Zama Barazana Ga Ƙasa

Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayyar Najeriya da ta ɗauki matakin tsara dokokin da za su daidaita amfani da kafafen sada zumunta (social media), yana mai cewa ana ƙara amfani da su ta hanyoyin da ke haifar da rikici, rarrabuwar kai, da rashin girmama juna a cikin ƙasa.

Sarkin ya bayyana haka ne ta bakin Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli, a taron Northern Ulamah Summit da aka gudanar a Kaduna, wanda ya tattauna batutuwan tsaro da kalubalen tattalin arziki a Arewa.

Ya bayyana damuwarsa kan yadda kafafen sada zumunta s**a zama hanyar zagi, raini da ɓata suna, inda kowa ke iya tashi safe ya ɗauki wayarsa ya zagi shugabanni, makwabta, ko ‘yan uwa ba tare da fuskantar hukunci ba.

> “A wasu ƙasashe, ana da tsauraran dokoki kan yadda ake amfani da kafafen sada zumunta, kuma duk wanda ya wallafa saƙon da ke haifar da rarrabuwar kai ko tayar da fitina ana gano shi, ana hukunta shi. Ya k**ata Najeriya ma ta ɗauki irin wannan mataki,” in ji Sarkin Musulmi.

Taron, wanda Ƙungiyar Malaman Arewa (Congregation of Northern Ulamas) ta shirya, ya haɗa manyan malamai, shugabanni, da masu ruwa da tsaki daga sassan Arewa domin tattauna hanyoyin magance matsalolin tsaro da ƙarfafa haɗin kai tsakanin al’umma.

Rikici ya barke tsakanin Yaran Zannan Bungudu da Yaran tsohon gwamna Matawalle.Sai dai a bangaren su jagororin sun bayya...
16/10/2025

Rikici ya barke tsakanin Yaran Zannan Bungudu da Yaran tsohon gwamna Matawalle.

Sai dai a bangaren su jagororin sun bayyana damuwarsu akan musayar yawu da mabiyansu suke yi akan takarar gwamnan a 2027.

Wane ne kukafi so APC ta tsayar takara a 2037?.

Dalilin Kafa CWC Ya Bayyana — Inji Ibrahim Aminu, GusauIbrahim Aminu Gusau, ya bayyana cewa babban dalilin kafa CWC (Cam...
16/10/2025

Dalilin Kafa CWC Ya Bayyana — Inji Ibrahim Aminu, Gusau

Ibrahim Aminu Gusau, ya bayyana cewa babban dalilin kafa CWC (Campaign Working Committee) shi ne domin a yi aiki da tsari wajen tallata Zannan Bungudu a zaben 2027.

Mun barranta kanmu da su tunfarko saboda munsan Makiyan Matawalle ne, Gashi Yanzu ta bayyana karara.

Yan Bindiga Sun Kashe Jami'an Tsaro Takwas a Hanyar Funtuwa Zuwa GusauInna lillahi wa inna ilaihi raji’un.Mun samu labar...
16/10/2025

Yan Bindiga Sun Kashe Jami'an Tsaro Takwas a Hanyar Funtuwa Zuwa Gusau

Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un.
Mun samu labarin mummunan harin kwanton bauna da ‘yan bindiga s**a kai wa jami’an tsaro a hanyar Funtuwa zuwa Gusau, wanda ya yi sanadiyyar rasuwar jami’an ‘yan sanda da askarawa takwas.

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya mika sakon ta’aziyya ga rundunar ‘yan sanda da sojoji da iyalan waɗanda s**a rasa rayukansu.

> “Wannan hari babban rashi ne ga jami’an tsaro da al’ummar Zamfara baki ɗaya.
Muna roƙon Allah Ya jikan su, Ya ba iyalansu haƙuri, Ya kuma kawo ƙarshen wannan matsalar tsaro da ta addabi jiharmu da ƙasar baki ɗaya.”

— Gwamna Dauda Lawal

Umar M. Bawa ya bayyana wannan ne yayin da ake rikici cikin jam’iyyar APC kan wanda zai tsaya takarar gwamnan Zamfara a ...
16/10/2025

Umar M. Bawa ya bayyana wannan ne yayin da ake rikici cikin jam’iyyar APC kan wanda zai tsaya takarar gwamnan Zamfara a 2027, inda ya ce su magoya bayan Matawalle ba za su goyi bayan kowa ba sai Matawalle.

Sabon Rikici ya Fara Kunno Kai a Jam’iyyar APC Zamfara.Yayin da ake ganin an samu sulhu da fahimtar juna tsakanin manyan...
16/10/2025

Sabon Rikici ya Fara Kunno Kai a Jam’iyyar APC Zamfara.

Yayin da ake ganin an samu sulhu da fahimtar juna tsakanin manyan jagororin jam’iyyar APC a Jihar Zamfara — Sanata Abdulaziz Yari da Ministan Tsaro, Bello Matawalle — alamu na nuna cewa sabuwar rashin jituwa na iya sake bayyana.

Wannan na zuwa ne bayan wata sanarwa da Ahmad Dan-Wudil, wanda shi ne PA ga tsohon Gwamna kuma Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya wallafa a shafinsa na Facebook.

A cikin rubutunsa, Dan-Wudil ya bayyana cewa yanzu lokaci ne da ya dace bangaren Sanata Abdulaziz Yari su mayar da biki wajen marawa Minista Bello Matawalle baya a tunkarar zaben 2027 — k**ar yadda su a da s**a ba Yari cikakken goyon baya lokacin da yake neman shugabancin Majalisar Dattijai.

Wannan furuci ya tayar da cece-kuce a kafafen sada zumunta, inda wasu ke ganin hakan na iya tayar da sabuwar rashin fahimta tsakanin bangarorin biyu da ake ganin sun fara samun daidaito kwanan nan.

Rahoton CK Media Services✍️

Address

Tudun Wada Gusau
Gusau
GUS234

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Ck Media Service posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Ck Media Service:

Share