19/10/2025
APC Ta Karyata Rahoton Da Aka Ce Ta Kafa Kwamiti Don Karɓar Gwamna Dauda Lawal
Daga Gusau – 19 ga Oktoba, 2025
Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta Jihar Zamfara ta nesanta kanta daga wani rahoton boge da aka wallafa a shafin confidentialreporters.blogspot.com, wanda ke ikirarin cewa jam’iyyar ta kafa kwamiti domin tarbar Gwamna Dauda Lawal cikin jam’iyyar.
Mai magana da yawun jam’iyyar, Yusuf Idris Gusau, ya bayyana cewa rahoton ƙarya ne kuma marar tushe, yana mai jaddada cewa jam’iyyar APC ba ta taɓa tattaunawa da jam’iyyar PDP ko kuma gwamnan jihar a kan wani yunkuri na shiga jam’iyyar ba.
Jam’iyyar APC ta Jihar Zamfara ba ta taɓa kusantar jam’iyyar PDP ko gwamnan jihar don neman ya shiga jam’iyyar ba. Wannan labari an ƙirƙire shi ne da mugun nufi don yaudaran jama’a,” inji Yusuf Idris.
Ya ce APC ta Zamfara ba ta taɓa gamsuwa da irin tafiyar gwamnatin Dauda Lawal ba, domin, a cewarsa, ayyukan gwamnatinsa sun gaza amfanin jama’a.
Yusuf Idris ya ƙara da cewa nasarar da jam’iyyar APC ta samu a zaben cike gurbi na Kaura Namoda South a ranar 16 ga Agusta, 2025, da kuma komawar ɗan takarar PDP da magoya bayansa zuwa APC, ya nuna irin goyon bayan da jama’a ke nunawa jam’iyyar a Zamfara.
Ya roƙi jama’a da su yi watsi da rahoton confidentialreporters, yana mai cewa jam’iyyar tana da hanyoyin yada bayanai na gaskiya da jama’a ke yarda da su.
Jam’iyyar APC za ta ci gaba da hulɗa da jama’a cikin mutunci da tsari, kuma ba za ta amince da labaran karya daga wasu kafafe marasa amana ba,” inji shi.