05/07/2024
MENENE SAMOA DEAL?
"Samoa" kalmace da aka dauko daga wani yare na wasu turawa da s**a rayu a tsibirin Pacific dake can yankin kudancin Amerika
A ranar 15 ga watan 11 shekarar 2023 kungiyar tarayyar turai (EU) sun sanya hannu akan wata sabuwar yarjejeniya da zasu kulla da kasashen Afirka akan manyan kudurorinsu na Turawa da zan lissafa a kasa, s**a yiwa yarjejiniyar take da "Samoa Agreement"
Daga cikin abubuwan da yarjejeniyar ta kunsa gasu kamar haka:
(1) Tattalin arziki
(2) Tsaro
(3) Dumamar yanayi
(3) Kare hakkin bil'adama
(4) Kare hakkin cin zarafi na yara kanana
(6) Kare hakkin mata
(7) 'Yancin sauya halitta na mutum
(8) 'Yancin Luwadi da Madigo
(9) 'Yancin auren jinsi
(10) 'Yancin zubar da ciki ga mata
A takaice wadannan abubuwa guda goma da na lissafa sune abinda wannan yarjejeniya na Samoa Deal ta kunsa, kuma babu shakka Gwamnatin Nigeria ta sanya hannu akan yarjejeniyar, sai dai ta yiwa abin kwaskwarima, amma fa dokar na Turawa ne ba na Gwamnatin Nigeria ba, don haka babu wani kwaskwarima da ta isa tayi
Wanda yake son ya karanta cikakken bayani akan wannan yarjejiniya na yahudu da nasara, na tura pdf app a Telegram 👇
https://t.me/DattiassalafiyTech
Magana ta gaskiya saka hannu da Gwamnatin Tinubu tayi akan wannan yarjejiniya na kungiyar tarayyar Turai amincewa ne da 'yancin Luwadi da Madigo a cikin Kasarmu Nigeria wanda Turawa suke neman a tabbatar dashi tsawon lokaci, sai gashi yanzu burinsu ya cika a Gwamnatin da aka kafa da sunan Musulunci
Ban taba zato da tsammani Gwamnatin Muslim Muslim zata mana haka ba, gashi nan sun sa mutanen kudu sai habaici suke mana cewa Gwamnatin Musulunci ta amince da 'yancin Luwadi, ku duba comment dinsu a Twitter da Facebook zaku gani
Yanzu ya rage wa Malamai wadanda s**a karbi kudi s**ace zaban Gwamnatin nan kamar zabar Musulunci ne, da kuma Malamai wadanda basu karbi kudi ba s**a tallata Gwamnatin, da Malaman da basu tallata ba duk su hadu su yaki wannan Gwamnatin da kudurinta na amincewa da yarjejiniyar Luwadi da Madigo
Ku saka ido ku gani, tunda Gwamnatin Nigeria ta saka hannu, shikenan yanzu za'a fara tallata harkokin Luwadi da Madigo gadangadan ta kowace irin kafar yada labarai a Nigeria, Gwamnatin ba zata goyi bayan a dakatar da su ba
Yaa Allah Ka i$ar mana tsakaninmu da wadannan ma¥audara mà ci¥a amana
أمين يا ØÙŠ ÙŠØ§ قيوم