18/07/2023
Domin iya rayuwa a sabuwar Najeriya sai ka koyi abubuwa kamar haka:
1. Bajet: ka dinga ware nawa za ka dinga kashewa a wata ko sati. Hakan zai sa ka dinga lura ba za ka dinga kashe-kashe kana rasa inda kudin ke zuwa ba. Sannan zai sa kudi ba zai dinga yanke maka kafin ka samu wani ba.
2. Ka hau motar haya: idan kana da abin hawa, ka dinga ajiyewa sai lokaci zuwa lokaci. Ba kowace rana ne za ka hau motarka ko mashin dinka ka je inda akwai ababan hawa na haya suna zuwa ba. Ka tuna cewa ko da za ka iya siyan fetur, yawan hawa abin hawanka zai ballo maka gyara kuma za ka dinga yi masa juyen bakin mai.
3. Rage yawaitar biki: Ka rage kashe kudi akan biki irin su birthday ko anniversary ko kuma wedding mai tsada. Irin wadannan abubuwan suna cinye kudi ba tare da ka ga manufarsu a zahiri ba. Maimakon haka, ka zuba kudin wajen gina rayuwarka kamar siyan fili don gini ko kuma kasuwanci.
4. Gayawa kanka gaskiya: ya kamata ka san kai talaka ne. Ka gayawa kanka gaskiya kai fa talaka ne. Ka dena kokarin yin abin da zai nuna kai mai kudi ne a idon jama'a alhalin a zuciyarka ka san ba ka da kudi. Abubuwa irin su dinke-dinke, siyan takalma da huluna masu tsada suna da lokacinsu. Kai talaka ne don haka ka gane lokacinka bai zo ba.
5. Ka rage kashe kudi a "subscriptions": yawan hawa TikTok yana zuke data. Yawan hawa YouTube yana zuke data. Don haka ka sani cewa kudinka mai yawa yana tafiya a data, don haka sai ka saita rayuwarka. Idan kana da subscriptions da Netflix, to ku hada kudi ku hudu ko biyar ku dinga biya tare maimakon kai kadai.
6. Rage cin bashi: ka dena cin bashin banki idan ka san ba kasuwanci za ka yi da kudin ba. Kada ka ci bashin gwamnati ka yi aure. Kada ka ci bashin kamfanoni ka sayi waya. Ka dena cin bashi da yawa. Ka dena kai kanka inda baka kai ba.
7. Ka koyi kananun gyara: ka koyi saita kwanon satellite dinka. Ka koyi gyaran socket din gidanka. Ka iya gyaran famfon gidanka da kanka. Ka koyi zuwa aike ba tare da ka nemo dan aiki ba. Ka koyi sauran kananun gyararrarki ba tare da sai ka dauko wani ya yi maka ba.
8. Ka yi aiki tukuru. Sannan ka yi addu'a. Manyan abubuwa kamar gina gida ko siyan mota sun fi zuwarwa mai aiki tukuru. Idan ba haka ba sai dai kawai ka ga ana yi amma kai ba za ka samu ba. Ka bude hanyoyin samunka. Hanya daya ba za ta bulle ba. Idan da dama ka yi aiyuka masu yawa don fadada samunka. Ka zama mai sana'a goma ka magance talauci.