21/08/2023
PLATFORM (PONZI SCHEME)
Abunda yake faruwa gameda abubuwan da s**a samu mutanenmu wanda akwai su daga ko wannen bangare na kasar nan, saidai mafi yawan abun tausayi da zakaji shine daga arewa ne, kuma hakan ya samo asali ne daga wasu tsiraren mutanen da s**a san hadarin abun amma s**aki sanar da yan uwa da abokan arzikinsu da s**a gayyato acikin harkar, Sai kuma wa'yanda suma kansu gayyatar su akayi basu san hadarin dake cike da abinba, kuma aka dora su akan hanyar kawo wasu domin abunda suke samu ya ninku.
Banso nace komai ba akan wannan hali da yan uwa da abokan mu s**a tsinci kansu aciki, na rasa makudan kudade, dukda wasu kuma alhamdulillah sun samu alkhairi sosai, Ba zanyi wannan rubutu ne ba domin cin mutuncin wasu ba, hasali Nima Dinnan ina platform kuma alhamdulillah zan iya cewa kaso 80% cikin dari 100% na platform dinda nayi acikin riba nake suke guduwa, adan karamin tunani na platform mafi hatsari shine wanda ake ninka maka duk abunda ka saka acikin awa ashirin da hudu 24hrs (DOUBLER), masu yin platform munsan abunda ake nufi da DOUBLER, to ni Dinnan nayi DOUBLER.
Asarar da aka samu wannan karon yanada alaka da yanda wasu mutanen s**a dauki cewa platform Dinnan suma fah kaman bankunan mune na gargajiya wato First Bank ko UBA, wannan shine babban kuskuren da sababbi a harkar s**a aikata kuma yazama sillar wannan mummunar asarar, bana tunanin akwai wanda yasan platform irinsu, INSMI, UWORK, SUN POWER, ToLike, ON THE WAY, Sbot da Strx da sauransu, ko kuma yayi shekara daya yana platform amma ace wai baya cire abunda yake samu acikin wayanan platform din irinsu, MTFE, AlphaAGPT, Catly đ¤, shiyasa zamuji asarar tafi yawa ga wa'yanda Ba'a yi musu cikakken bayanin akan harkar ba.
Naji mamakin yanda wasu s**a dinga bayarda kwarin guiwa wa wasu mutane su siyarda abunda s**a mallaka su shiga harkar, wanda duk wani babba aharkar bazai baka wannan shawara ba, hasali ma nasan CEO MTFE wanda yace cewa basa don suji ance za'a siyar da wata kadara ashiga sunfison suji ance ancire daga ciki an siyi kadarorin.
Yau naji wani lost daga bakin mai ita wanda ya girgizani amma babu abinda na'iya fiyeda nace Allah ya mayar da alkairi, dan Allah ya kamata komai zamu saka wasu mudinga fada musu alkairi da kuma abunda ke iya faruwa idan aka samu matsala, nayi platform abaya wanda yanzun na fahimci kuskuren dake cikin hakan saboda abunda ya faru wannan lokacin, ina rokon Allah da ya yafe mana kuma ya bamu ikon gane gaskiya da yarda da ita komai Dacinta.
a karshe ina mai rokon Allah ya mayar da alkairi ga wyaanda wannan abu ya rutsa dasu.