17/07/2025
BUY BACK STRATEGY – Tsarin Siyan Coin Sau Biyu Don Riba Mai Sauki
Koda ba ka da cikakken ilimin Technical Analysis, har yanzu kana iya zama mai cin riba a kasuwa. Wannan yana yiwuwa idan ka kware a Fundamental Analysis.
Menene Fundamental Analysis?
Fundamental Analysis shine tsarin binciken coins masu inganci kafin a zuba jari a cikinsu. Wannan jari yawanci ana barinsa na tsawon lokaci—kamar wata 3, 6 ko har zuwa shekara 5. Wadanda ke yin wannan irin zuba jari ana kiransu da Investors ko Long-Term Traders.
Amma kasancewarka long-term trader ba yana nufin ka zuba kudi ka manta da su ba. A’a. Dole ka kasance kana sa ido da bincike lokaci-lokaci akan coin ɗin da kake rike da shi.
Yaya Ake Amfani da Buy Back Strategy?
Buy Back Strategy hanya ce da masu kasuwa ke amfani da ita don ninka adadin coins da suke da shi, ba tare da sun tsaya jiran karshen lokacin jari ba.
Misali:
Ka sayi wani coin a $100. Sai ka ji cewa wani event yana tafe wanda zai iya haifar da tashin farashi. Bayan event din, farashin coin ɗin ya tashi zuwa $170.
Ka siyar da coin din, amma ka bar kudin a cikin wallet dinka. Bayan wasu kwanaki, farashin coin din ya dawo ƙasa—misali ya sauka zuwa $85.
A wannan lokacin sai ka sake siyan coin din da $170 ɗin da ka samu, maimakon $100 dinka na farko. Wannan yana baka damar samun ninki ko fiye na coin ɗin da ka rike a farko.
> Amfanin Tsarin:
Ka fitar da riba.
Ka kara adadin coin dinka.
Ka ci gaba da kasancewa cikin kasuwa tare da karuwar holdings.
Amma Fa...
Idan ba ka yi bincike ba, kana iya rasa wannan dama. Abin da ya fi muhimmanci shi ne:
Kula da labarai.
Fahimtar fundamentals na project.
Kula da abubuwan da ke iya kawo canji a kasuwa.
Misali Na Gaskiya – SIDRA Token:
Na yi mining na coin mai suna SIDRA, wanda har yanzu bai shiga manyan kasuwanni ba. Na tara SIDRA 1000, amma 500 ne kawai aka ba ni damar siyarwa.
Bayan na kammala KYC, na siyar da 500 SIDRA akan ₦175,000.
Na yi amfani da wannan kuɗin na saya computer 💻.
Bayan wani lokaci, na samu wasu kuɗi na tambayi farashin SIDRA – sai aka ce 500 SIDRA = ₦34,000.
Na saya SIDRA ɗin da wannan ƙananan kuɗin, na dawo da coin ɗin da na siyar da babban riba a baya.
> Wannan shine cikakken amfani na Buy Back Strategy.
---
Kammalawa:
Kasuwanci yana bukatar ilimi, haƙuri da kuma bincike. Kada ka dogara da tsammani kawai. Idan ka fahimci Buy Back Strategy da kyau, zaka iya ci gaba da samun riba duk da cewa kana kasuwanci na dogon lokaci.
Allah yasa mu dace, Ameen.