Vision Fm Zamfara

Vision Fm Zamfara Vision Fm Gusau

Majalisar dokokin jahar Zamfara ta dakatar da shugabannin kananan hukumomi guda biyu da s**a hada da ba Kaura Namoda da ...
08/04/2026

Majalisar dokokin jahar Zamfara ta dakatar da shugabannin kananan hukumomi guda biyu da s**a hada da ba Kaura Namoda da kuma Bukkuyum.

Shugabannin dai sune Hon. Umar A. Faru Nasarawa na karamar hukumar Bukkuyum da kuma Hon. Mannir Mu’azu Haidara na karamar hukumar Kaura Namoda.

Majalisar dokokin ta kuma umurci mataimakan shugabannin majalisun biyu da su ci gaba da tafiyar da ragamar mulki har sai an kammala bincike.

Yayin da masu rike da mukaman siyasa ke cigaba da marawa gwamna Dr. Dauda Lawal bayan wajan shiga jam'iyyar APC.Shi kuwa...
23/03/2026

Yayin da masu rike da mukaman siyasa ke cigaba da marawa gwamna Dr. Dauda Lawal bayan wajan shiga jam'iyyar APC.

Shi kuwa kwamishinan ma'aikatar ilimi Malam Wadatau Madawaki ya ajiye mukamin sa.

Tuni dai da gwamna Dr. Dauda Lawal ya aminta da ajiye mukamin nasa tare da baiwa kwamishinan ma'aikatar kudi da tsare-tsare Hon. Abdulmalik Gajam umurnin kula da ma'aikatar ilimin.

Gwamna Dr. Dauda Lawal ya umurci dukkanin masu rike da mukaman siyasa dake bukatar yin takara a kujerun siyasa a 2027, d...
23/03/2026

Gwamna Dr. Dauda Lawal ya umurci dukkanin masu rike da mukaman siyasa dake bukatar yin takara a kujerun siyasa a 2027, da su ajiye aikin su nan take.

An kafa komitoci da shugabanni duk a cikin shirye-shiryen sauya shekar gwamna Dr. Dauda Lawal na jahar Zamfara zuwa Jam'...
22/03/2026

An kafa komitoci da shugabanni duk a cikin shirye-shiryen sauya shekar gwamna Dr. Dauda Lawal na jahar Zamfara zuwa Jam'iyyar APC.

1. HE. Mal. Mani. Chairman Main / Reception Committee

2. Mukhtar Muhammad Lugga. Chairman Venue and protocol Committee

3. Hon. Lawal . Liman Gabdon Kaura. Chairman Media and publicity Committee

4. Hon. Abdulmalik Zannan Bungudu. Chairman Finance Committee

5. Hon. Kabiru Amadu Mai Palace. Chairman Monitoring and Compliance Committee

6. Alh. Abubakar na kwada. Chairman Security Committee.

Jirgin farko ya sauka a filin tashi da saukar jiragen saman kasa da kasa wato Gusau international airport.
22/03/2026

Jirgin farko ya sauka a filin tashi da saukar jiragen saman kasa da kasa wato Gusau international airport.

Bayan komawar gwamna Dr. Dauda Lawal jam'iyyar APC a yanzu me ya rage kenan?
09/03/2026

Bayan komawar gwamna Dr. Dauda Lawal jam'iyyar APC a yanzu me ya rage kenan?

26/01/2026

Shin abinda ke faruwa a jahar Kano na siyasa na baku mamaki?

Mustapha Rabi'u Kwankwaso ya ajiye mukamin sa na kwamishinan matasa da wasanni na jahar Kano.Wannan matakin na zuwa ne y...
26/01/2026

Mustapha Rabi'u Kwankwaso ya ajiye mukamin sa na kwamishinan matasa da wasanni na jahar Kano.

Wannan matakin na zuwa ne yayin aka shiga wani sabon babi a siyasar Kano bayan da gwamna Abba Kabir Yusuf ya koma jam'iyyar APC.

Kuna ganin matakin ya dace?

Gwamnan jahar Kano Abba Kabir Yusuf ya fice daga jam'iyyar da aka zabe shi ta NNPP.Sanarwar fitar gwamna Abba na zuwa ne...
23/01/2026

Gwamnan jahar Kano Abba Kabir Yusuf ya fice daga jam'iyyar da aka zabe shi ta NNPP.

Sanarwar fitar gwamna Abba na zuwa ne bayan wata sanarwar da mai magana da yawun sa Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a yau Juma'a.

Shin ya kuke kallon wannan matakin?

Tsohon gwamnan jahar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana takaicinsa kan halin da dimukradiyyar Najeriya ke ciki.Amin...
11/01/2026

Tsohon gwamnan jahar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana takaicinsa kan halin da dimukradiyyar Najeriya ke ciki.

Aminu Waziri Tambuwal wanda shine mai wakiltar yankin Sokoto ta Kudu yace akwai damuwa kan halin da Nijeriya ke ciki abinda ya kira da kasar na cikin hadari.

Kalaman na Tambuwal dai na zuwa ne a yayin da yake jawabi ga mahalarta taron bukin cikar sa shekaru 60 da haihuwa.

Shin ya kuke kallon kalaman nasa?

'Yan majalisar dokokin jahar Zamfara guda 6 dake inuwar jam'iyyar PDP sun sauya sheka zuwa babbar jam'iyyar adawa ta APC...
25/12/2025

'Yan majalisar dokokin jahar Zamfara guda 6 dake inuwar jam'iyyar PDP sun sauya sheka zuwa babbar jam'iyyar adawa ta APC a jahar.

Sauyar shekar nasu na zuwa dai-dai lokacin da suke cigaba da fuskantar dakatarwa daga shugabancin majalisar dokokin jahar karkashin jagorancin kakakin ta Right Hon. Bilyaminu Isma'il Moriki.

Address

Eastern Baypass Gusau
Gusau

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Vision Fm Zamfara posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Vision Fm Zamfara:

Share