02/08/2025
Daga NafI'u Abubakar
Zuwa ga Al'mansoor Gusau akan ƙazafi da ɓata sunan da yake ƙoƙarin yi ga food palace Restaurant Gusau, da ma'aikatan wurin.
Da farko dai Al'mansoor kaji tsoron Allah, ka Daina siyasantar da abinda ya shafi harakar tsaro.
Haka kuma kasani shi wanda kake ƙoƙarin ɓata ma siyasa ta hanyar masana'anta to wallahi tun baka da wayo rabon shi da yasan miyake gudana a food palace, b***e har yasan waye ma'akacin food palace.
Sannan kuma mutanen da suke aiki a gidan abincin nan akwai waɗanda sunyi shekarun haihuwarka gidan nan kuma ba'ataɓa k**a su da irin laifin da ka rataya masuba, kuma shi wannan yaron da ya aikata wannan mugun laifin duka haifi wata shidda yana aiki a wurinba Sannan abu ne wanda ako ina ana samun ɓare gurbi koda cikin jami'an gwamnati. Kai koma cikin gida ko cikin unguwa ne.
Al'mansoor tunda kai kana ganin kafi jami'an tsaro iya aiki to sai kaje ka tantance ma'aikatan kokuma kaba su sunayen waɗanda kake zargi acikin ma'aikatan ko ka rubuta sunayensu k**ar yadda ka rubuta sunan ma'aikatar.
Kuma Yak**ata kasani duk wurin da Allah ya ɗaukaka kai baka isa ka rosashiba, saboda haka wannan kwangilar da ka karɓo bakaiya cimma burinkaba.
Daga ƙarshe Ni ba ina goyon bayan abinda wannan yaron ya aikata bane, amma dai kudin goron da kukeyima ma'aikatan wurin ba daidai bane kuma gobe kiyama sai kunyi bayani a gaban Ubangiji da kai da duk mai irin wannan zargin.
Ubangiji Allah ya ƙara tsare muna mutuncinmu, ya kawo muna zaman lafiya da kwanciyar hankali.