
19/09/2025
Kungiyar matasan Arewacin Nijeriya ta yabi salon diflomasiyyar inganta tsaro da Matawalle ya bullo da ita
.....Jagora ne na gudanar da aiki, ba na ba da uzurorin karya ba....in ji kungiyar
Kungiyar matasan Arewacin Nijeriya mai suna Northern Youth Concert Citizen ta bayyana jin daɗinta da nutsuwa ga ire-iren ayyukan da ministan kasa a ma'aikatar tsaron Nijeriya, Dr. Bello Muhammad Matawallle ke aiwatarwa, tana mai kiran sa “jagoran gudanar da aiki tukuru, ba na ba da uzurorin babu gaira babu dalili ba” saboda jajircewarsa wajen ƙarfafa diflomasiyyar inganta tsaron Nijeriya.
Shugaban ƙungiyar, Dr. Ibrahim Garba daga Karamar Hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna, ya ce, “Matawalle ya sake fasalin diflomasiyyar inganta tsaro ta hanyar nuna batutuwan gyaran tsaro a aikace. Daga Turkiyya zuwa China, daga Pakistan zuwa Amurka, ƙoƙarinsa ya samar da kayayyakin aiki na zamani, inganta fasaha da kuma horo na zamani ga rundunar sojinmu.”
Sanarwar ta kuma nuna muhimmancin sababbin jiragen sintiri masu nisan zango, inda ta bayyana su a matsayin wani hangen nesansa da burin kare Nijeriya ta ƙasa, sama da ruwa da Minista Matawalle kebda shi.” Sanarwar ta ƙara da cewa hakan sadaukarwa ce wajen kare kima da martabar ƙasar.
Dr. Garba ya ƙara da cewa, “Ga matasan Arewacin Nijeriya da ke rayuwa a kullum da matsalar tsaro, jagorancin Matawalle ya dawo musu da cikakkiyar fata cewa Nijeriya za ta iya, kuma za ta shawo kan ƙalubalen tsaronta ta hanyar haɗin gwiwar dabaru da kuma ƙarfafa ƙarfin cikin gida.”
A ƙarshe, ƙungiyar ta sake tabbatar da cikakken goyon bayanta ga Ministan Matawalle, tana mai jaddada cewa
“Jajircewarsa na kara sanya kwarin gwiwa a zukatan miliyoyin ’yan kasa, musamman matasa, waɗanda ke fatan ganin ƙasa mai tsaro, ƙarfi da kuma cigaba.”