27/09/2025
AKWAI SAKACIN GWAMNATI A HARIN MASALLACIN YANDOTO - MALAM MUSA
Tsafe, Zamfara – Biyo bayan samun mummunan hari, ran 26 ga Satumba, inda wasu ƴan bindiga s**a kutsa cikin babban masallacin Yandoto, a karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara, s**a bude wuta kan masu ibada a lokacin sallar Asuba, mazauna yankin sun fara tofa albarkacin bakin su.
Shaidu sun bayyana cewa akalla mutum biyar ne s**a rasa rayukansu a wajen, yayin da wasu kuma aka yi garkuwa da su. Lamarin ya jefa al’ummar yankin cikin firgici da alhini, inda aka ce jinin waɗanda s**a mutu ya bata dardumar masallaci.
Wani mazaunin yankin, Malam Musa Tsafe, wanda ya yi magana da manema labarai a madadin jama’ar Yandoto, ya bayyana cewa akwai alamun sakacin gwamnati, yana mai karawa da cewa harin ya girgiza su matuƙa. “Mutane sun rasa rayuka a gaban mahaliccinsu yayin da suke ibada. Wannan abin bakin ciki ne da ya bar yara da mata cikin tsananin tashin hankali,” in ji shi.
Ya ce al’ummar yankin na kira ga hukumomi da su dauki matakai na gaggawa wajen ƙara tsaro a Tsafe da kauyukan da ke makwabtaka. Ya kuma bukaci a gudanar da bincike kan yadda maharan s**a shigo masallaci ba tare da wani shamaki ba, tare da samar da taimako ga waɗanda abin ya rutsa da su.
A cewarsa, abin da jama’ar ke bukata a halin yanzu shi ne “kariya ta hakika daga jami’an tsaro, taimakon gaggawa ga wadanda s**a tsira, da kuma matakan doka da za su tabbatar da tsaro a nan gaba.”
Wannan hari, kamar yadda rahotanni s**a nuna, na cikin jerin hare-haren da ake ta kaiwa a yankin Tsafe da wasu sassan jihar Zamfara, wanda s**a hada da sace-sacen mutane da kuma kai farmaki a masallatai.
A halin yanzu, hukumomin tsaro ba su fitar da cikakken bayani kan lamarin ba, sai dai al’ummar Yandoto na kira da a dauki matakin gaggawa don dakile irin wannan tashin hankali da ke ci gaba da addabar jihar.